💔 AFIYYA 💔Seven (Free)
✍️ Ayshatuuu
Bayan Malam ya Gama sauraron duk bayanan zainab se ya sakata a gaba Suka tafi police station Dan ita kadai ce zata saka ayi bailing Junaidu. Tunda dama it's din ta hada husumar so seta Zama wadda zata warware ta. Lokacinda Suka Isa gaba daya Junaidu ya canja kammanni saboda dukan da ya Sha, tunda Suka shiga DPO yace a lallasa masa shi har se ya gane baa dukan mace. Ga Junaidu da bakar zuciya haka yaki Basu hakuri se amsar dukan yake. Malam na Isa yayi ma officers din dake tsaye a reception bayani, daya daga ciki yace Masa
" Malam kawai ka tafi Dan bansan ranar belin wannan gaggararren Dan naka ba"
Malam ya gyara tsayuwan shi yace" Idan ba zaku damu ba Ina son magana da DPO din ku"
Daya daga ciki yace
" DPO baya gari yaje headquarter acan Dutse"
Malam ya gyada Kai yace
" Idan ba zaka damu ba ko Zan samu num..."
" Baya cikin aiki, kaga Malam Muna ganin girmanka a gurinnan, tunda munce ka wuce kawai ka tafi"
Malam ya Kama hannun zainab Suka fita a station din, haihuwa kenan sanadin ta Babu abinda bazai same ka ba walau sharri walau khairi, shi Bai taba zuwa police station ba Amma dalilin Junaidu yau shi ake cewa ya fita duk girman shi da darajar shi.
" Ai da ka sani ka tatse shi wallahi, malaman nan kudi be dasu, yaran Yan siyasa ne fa"
Dayan yace
" A'a gwara dai a kyaleshi saboda wannan Yana da connection da manyan mutane kada mu jawa aikin mu"
Yana zuwa gidan ya tarar da fada ya barke tsakanin Fatima da Hasiya, Hajja nata kokarin raba su Amma sunki, sede suka hi sallamar shi sannan cacar bakin da suke ta lafa, Bai ce musu komai ba ya nufi dakin shi, Amma kowacce Tasha jinin jikinta, Hajja ta bi Bayan shi ta sameshi zaune ya kurawa guri daya idanu, he looks disturbed. Zama tayi tana fadin
" Malam kayi hakuri kada ka Bari abin Junaidu ya dameka, adduar shiriya ita ce zata rabamu dashi"
Ya gyada Kai Amma Bai ce komai ba hakan ya tabbatar Mata ba zaiyi magana ba, se ta tashi ta fito dukda tana son taji yadda aka Kare a station din Amma Bata son damun shi, Kuma alamu sun nuna baayi nasara ba, tunda ya shigo babu Junaidu. A tsakar gida taji zainab na fadawa Hasiya yadda sukai a station da officers din, hankalinta ya Kara tashi to Amma ya zatayi? Sai dai ta zubawa sarautar Allah idanu. Wasawasa magana se ta Zama babba tun Malam yana zuwa wajen police din suna Masa yawo da hankali har ya kyalle su, Fatima Kuma sunyi magana da DPO akan se Malam ya Bata hakuri sannan zai sake Junaidu. Ko fahimtar abinda take nufi yayi se ya kyaleta Bai ce da ita komai ba Amma se ya kaurace Mata, kwana biyu da tayi a dakin shi magana ta fatar Baki Bata hada su ba, hankalin ta yayi mummunan tashi, washegari wajen azahar se ga Junaidu an sako Shi, fuskar shi ta kumbura saboda duka, ga jikin shi da duk shatin bulala a jiki. Hajja Huwaila ta daura ruwan zafi tasa yayi wanka, ta gasa Masa jiki sannan ta shafa Masa man zafin da Hasiya ta kawo Mata. Yaci abinci ya kwanta a ranshi Yana saka next abinda zaiyi!
Na karasa gaban gadon tareda jijjiga Abbu, Amma a hakan nan dai yake kwance lifeless, Babu digon numfashi dake jikin shi, gaba daya jikin yayi sanyi, kwayar idanun shi a rufe tamkar me bacci, hakan ya tabbatar min daga baccin aka zare Masa Rai. Naja baya da sauri tareda rufe bakina da hannuna Ina jin ilahirin jikina Yana rawa kamar ana kada min mazari. Hajiya na kuka ta fita yayinda ni banyi kukan ba sede Ina tsaye a gaban shi Ina fatan Nanny ta buga min gefen gado na ta tashe ni tace min na tashi zanje makaranta, Amma ba mafarki nake ba, idanuna biyu it's happening in reality Abbu is no more. Nayi shiru ban masan me zuciyata ke sakawa ba a wañnan lokacin, bazan iya Baku labarin yanayin da na shiga ba nasan dai I was more than shattered. Babu wata kalma da Zan muku amfani da ita ta nuna bayyana muku halin da na shiga, Wanda kadai ya rasa iyaye shi zai fahimci me nake nufi. Ina nan a tsaye na fara jin koke koken mutane, Ina tsaye na tsira Masa idanu, Kawu Sa'idu da wasu daga cikin Yayan sarki Suka shigo, duka Ina tsaye aka fara kokarin shiray shi, nasan an ja hannuna an fita Dani, but bazan iya cewa waye ba, kowa kallon shi kawai nake na Zama tamkar statue. Gidan kafin wani lokaci ya cika dam da mutane, se kuka suke Amma gani nake duk yadda suke ji ba zai Kai yadda nakeji ba. Mummy Maryam da Rooks Naga sun shigo, ta rike hannun Mummy dake wani irin kuka tamkar ranta zai fita Amma Ina nikam nawa idanu ne. Seda aka fito dashi cikin makara sannan na Mike tsaye, Kawu Tijjani yazo ya rike hannun na idanun shi se hawaye ke fita yace