💔 AFIYYA 💔Three (Free)
✍️Ayshatuuu
Mutuwar Mama ta girgiza mutane da dama saboda rashin lafiyar da tayi ma ba kowa bane ya San batada lafiya, it was very brief Amma da yake karar kwana ce se gashi ta rasu ta barmu ni da Abbuna. He was completely shattered beyond imagination, har ya koma ga Allah Babu ranar da baya cewa " da Halima nada Rai, Allah sarki Halima" maganar shi kenan, kullum Rana se ya bani labarin ta sede idan baya gari ko bana nan. A luth ta kwanta aka Gama duk wani cike cike da ya kamata sannan yayi booking flight within few hours suka dakko gawar zuwa Kano, kafin mu karaso an turo Mana motoci daga Ringim Emirate council Wanda zasu tafi da gawar zuwa inda dubban mutane ke jira a sallace ta. Abbuna yana rike Dani a kafadar shi tunda muka taho nayi bacci bayan Nanny ta bani oat nasha. Muna zuwa danginta da suke nigeria duka sun biyo flight zuwa Kano sun karasa Ringim, ita mamanta Bata gidan Kuma ita daya ta Haifa, asalin ta Yar Ethiopia ce, so Bayan sun rabu da shehun borno ta koma kasarta, acan Bata wani Jima ba ta rasu, so nidin jini da yawa ke bin veins dina. Ina baccin Nanny ta shiga Dani ta goya ni a wañnan yammacin aka kaita makabarta aka binne ta. Abbu was devastated, kallon shi kadai zai baka tausayi kowa yabin halayen kirkinta yake. Mutane da yawa kallon Abbu Dani ke saka su kuka na tausayin mu. Tunda na farka a baccin aka bani abinci naci se na kankame Nanny dama ni me kowa ce saboda ban Saba ganin mutane a gidan mu ba. Idan Naga mutane Kuma to se na nanike mamata ko Abbuna, idan Babu daya se na nanike Nanny. Kwana uku mutane suka baje yawancin zaman makokin Ina jikin Abbuna a kofar gida Dan naki Zama ciki, kowa se yaji tausayi na. A Rana ta bakwai Bayan an gama adduaa aka raba gado, a cikin dangin Mama Babu Wanda yace zai tafi Dani shima Kuma Abbu Bai yiwa kowa tayi ba, sun tafi suna ta jin rashin dadin rasuwar Yar uwarsu. Duk yadda rayuwa zatayi Dole mutum ya cigaba da rayuwa, duk wani bakin ciki da zaka dandana akwai ranar da zai wuce kaji kamar baayi ba. Bayan gidan ya watse Hajiya tayiwa Abbu nasiha sosae Amma se yace Mata shifa tayi hakuri aure daya ne Kuma yayi Amma baya tunanin zai Kara wani. Mummy tace to ita zata karbe ni ta hada Rooks Amma yace ya gode zai rike ni Yana ganina yaji Dadi. Daga nan muka koma Abuja saboda transfer da akai masa zuwa can. Gidan daga ni se shi se Nanny se Kuma maids din dake Mana aiki, da Nanny ke Mana komai Amma tunda ita ce sabuwar uwata Abbuna ya maida ita kawai kula Dani su Kuma sauran suyi aikin gida. Akai akai yake kaini Ringim Dan na Saba dasu, Yan uwan Mama Babu Wanda ya taba zuwa ya ganni Dan haka Abbu yace shima bazai kaini ba, har na Isa yaye aka daina feeding Dina da Madara se aka koma solid food. Ban Jima da yaye ba na cika shekara biyu, Abbu ya kaini creche, so ni dai as far as am concern tunda nayi wayo a makaranta nake, karatu nake, Dan hakan karatu a cikin Raina yake, shekarata ta farko bani ma da wayo bazan iya tuna komai ba, seda nayi shekara biyar sannan na fara sanin kaina, mutum daya na gane matsayin uwata da ubana Abbu, shi kadai na sani kowa as preliminary nake ganin shi,duk Wanda na Kira da Baba to Kara ce kawai,Dan Babu Wanda ya yimin abinda Abbu yayi min.
Saboda yadda na Shiga makaranta da wuri yasa kankanin lokaci na gama. Munje Ringim Ina kwance akan cinyar Hajiya Abbuna ya shigo Dan tun isowar mu fada ya fara zuwa ya gaishe da sarki sannan ya fito mutane Kuma suka tareshi kowa na fada Masa financial complain dinsu Dan ya taimaka musu. Da kyar na yadda na shigo gida shima Yaya na gidan Kawu Sa'idu ne ya lallaba ni muka shigo cikin gidan dashi, Ina ganin Hajiya se na saki hannun shi na nufi inda take zaune ta mike kafafun ta na kwanta Ina ce Mata
" I was waiting for you, you didn't come to my house and I missed you!"
Ta dungure min kaina tace
" Ni bana jin wannan yaran nasarar da Baban ki yake koya Miki, yimin hausa"
Yaya dake gefe yayi ta Mana dariya sannan ya fassara Mata abinda nace, ta rungume ni Yana cemin ita ta tsufa ba zata iya zuwa har can capital wajena ba. Tana ta tambayata abinda zanci ne Abbuna ya shigo, nayi saurin tashi na koma kan cinyar shi, murmushi yayi ya zaunar Dani Yana gyara min hular kaina suka gaisa da Hajiya, Yaya ya Mike Dan yasan ya kamata ya Basu guri, hannu ya Mika min yace
" So muje na kaiki gidan mu"
Na kalleshi sannan na kalla Abbu, ya gyada min Kai tareda mikar Dani tsaye, har na tafi na dawo na rungume shi nace
" I'll mish u"
Yayi dariya yace
" My Princess go"
Na wuce hannuna cikin na Yaya muka nufi gidan su dake can gefe duka a cikin Ausar ne. Muna zuwa duka suna zaune ita Ummaah na gaban murhu tana rabon shinkafa da Mai da yaji, su Kuma suna zaune an shimfida katuwar tabarma na bogaji suna jiran a Gama kowa ya dauki nashi. Muna sallama suna ganina Mino ta mike tana fadin
" Afiyya oyoyo! Ummaah Kinga Afiyya tazo"
Ta juyo ta kalleni ni Kuma naje kamar yadda Abbu yace min idan Naga babba na gaishe shi na tsugunna nace Mata Ina kwana, ta tabe baki ta fara fadin
" Kanwar uwarki ce Afiyya da Zaki dinga wannan ihun? Shashasha kawai"
Jiki a sabule ta zauna, shikam Yaya Zama yayi yace
" Ummaah Baki amsa Mata gaisuwar ba"
" To uban shishiggi Kai Kuma, Wai ita wannan Afiyya din Yar gwal ce, bazan amsa ba"
Sanin halinta yasa ya guntse bakin shi ya Mike yace min na zauna yanzun zai dawo, na Mike na Kama hannun shi Dan kada ya tafi, Mino yasa ta daukeni haka na Dan zauna a dadare saboda rashin sabo, abinci kowa yaje ya dauki nashi, Nima aka Miko min wani Dan mitsitsi cikin karamin roba, na karba na aje Amma naki ci saboda bana ma jin Yunwa, suna Gama ci Siyama ta janyo nawa ta cinye, Mino na Mata magana Ummaah tace ta barta dama ni na xo na datse musu abincin su. Yaya ya dawo da kifi a Leda ya dauki abincin shi yace nazo naci me kifi, ni Kuma since from childhood bana ketare tayin kifi saboda yadda Abbu ya Saba min cin kifi kullum se mun ci a dinner. Ina ganin Kifin naje na zauna Siyama ma ta taho ya dinga bamu muna ci har ya Gama naje nace ma Ummaah ta wanke min hannu, ruwa kawai ta zuba min na cuda tace naje, nace Mata ai se an saka detergent sanann zai fita, se ta koreni Wai Ina Mata iyayi. Ban wani Kara sakewa ba saboda karnin da hannuna yake na dameshi ya maida ni gurin Abbuna.
" Jarabar ka tasa ka dakko ta,seka maida ita ai"
Ya Mike ya Kama hannuna muka tafi, Ina zuwa na samu Abbu ya fita, se na zauna wajen Hajiya Ina Mata hirar school, se dare ya dawo da Kifin shi. Naci nayi bacci, bayan fita ta Hajiya ta nuna Masa lallai ya kamata ya kaini maiduguri Koda su Basu neme ni ba to shi ya kamata ya Kai ni na gansu, idan sun cigaba da nemana kansu idan Basu Kara ba shi dai ya sauke wannan nauyin. Washegari muka tafi Kano muka bi flight zuwa maiduguri, ya kaini na gaida kakkani na duk sunata borin kunyar Wai Basu San min koma Abuja ba, se zuzzuta yadda na girma nake Kama da Mama suke. Akazo zau tafi na dinga kuka bazan zauna ba hakan shima ya hakura muka tafi tare. Kawata Dana fara Yi a school namesake Dita ce, sunan ta Amina Abubakar Rogo, gari kadai ya banbanta sunan mu. An tashi school drivern mu duka Bai zo daukar mu ba, muna zaune inda muke Zama mu jira na Bata book Dina Wanda tsayin shi bazai Shiga cikin backpack Dita ba haka itama, inda water dispenser ke aje naje na tsiyayo ruwa nasha sannan nayi discarding cup din sannan na dawo na karba book Dina, kafin na zauna Nanny ta shigo cikin sauri, nayi sauri na nufe ta Ina rungume ta nace
" Nanny!"
Ta shafa kaina ta karba book Dina, da food box dina da Kuma backpack Dita nayi waving Amina muka tafi. Tun cikin mota nake Mata complain Yunwa nake ji, tace ai ta Gama abinci, nace Mata Abbuna ya dawo tace ai yace se dare zai dawo. Muna zuwa gida na wuce dakina da gudu na dauki waya nayi dialing wayar office din Daddy, Yana picking nace Masa yaushe zai dawo yace nayi hakuri naci abinci zai dawo da daddare, ba yadda naso haka na yadda mukai sallama. Akazo wanka nace ni fa da kaina zanyi da kyar na yadda Nanny tayi min.
Ina zaune Bayan maghrib a dakina na tasa drawing book a gaba dasu pencil colors da water color Dole se na zana picture Mama da Abbuna dake rungume Dani on my first birthday,
" Where's my princess?"
Naji muryar Abbu Yana tahowa dakina, na yadda drawing book din na taho a guje gurin shi na rungume shi, ya daga ni sama ya wulla ni ya cabe nayi dariya na rungume shi. Tare mukaci abinci sannan na raka shi yayi Dan walk cikin compound dinmu sannan Muna dawowa Nanny ta min wanka yazo ya zauna gefena Yana tambayata yadda school ta kasance a hakan nayi bacci sannan ya tafi. Haka yake min kullum indai Yana gida to zai zauna side bed Dina har se nayi bacci. My father my world!
AFIYYA is not free, pay 300 into 3091721807 A'isha Hassan kwalam, first Bank of Nigeria. Send evidence of payment through 09063467258.
Shatttzzzx