XXV

1K 177 22
                                    


UWARGIDAN BAHAUSHE

XXV (25)

✍️ Ayshatuuu 💜


Bayan Yan satittika result din post utme ya fita, Allah ya taimaka min na samu na haye. Abinda nake jira kawai shi ne admission list na samu na tafi makaranta Nima, Ina fata idan na danyi nesa da gida wasu abubuwan ba zasu dinga Bata min Rai ba, Zan dan manta cewar uwata a wulakance take wajen babana, duk da hakan ba me yiwuwa bane manta ba Amma dai bahaushe yace kazantar da baka gani ba to tsafta ce.

A wañnan lokacin shakuwata da Bature ta Kai wani level Wanda Ina jin ya Zama jinin jikina, dukda Ina kokarin ganin ban Bari sin shi yayi min illa sosae ba, saboda ni mutum ce paranoid ni nasan inada wannan disorder din. Ranar an tashi ana kwalla Rana kasancewar lokacin sanyi Bai shigo ba haka damuna ta riga ta Fadi, Ina zaune kan sofa din shagon Ammi, ita Kuma tana ta attending ma tsirarin customers da suke zuwa yawancin masu sari ne se Kuma masu fitar da anko. Hannuna rike da wani littafi 5 love languages by Gary Chapman, Yana daya daga cikin books din da Usman ya aiko min lokacin da na gama secondary, se wannan satin na fara karantawa, har na Gama da uku cikin goma. Tuna shi da nayi ko idan na dauka littafin se Ina samu kaina da tunanin ko Ina yake? Ki me yake? Kilan ya manta Dani yayi moving. To Amma wannan tunanin tamkar Ina downgrading abinda karfin kaddara zaiyi, lokuta da dama idan na tuna actions Dina se naga me yasa na Bata lokacina. To Amma kowanne mutum akwai path din da Allah ya tsara Masa ya bi.

Murmushi nayi Ina tuna lokutan da yake stalking dina da idanun shi ko ya biyo ni class very early kafin kowa ya fito,a lokacin gani nake ya takura min amma bayan ya tafi nakan Jima Ina kallon empty space din daya kamata ace shi yake zaune Yana min magana da gentle tone din shi Amma baya nan, I can't deny the fact that I missed him. Maganar da Ammi tayi min akan na binciko Mata wata batik wax yasa na aje litaffin na je na dauko na dawo. Littafin na Kara dauka Amma wannan Karan na maida dukkan hankalina wajen fahimtar me Chapman yake son isar Mana. Love languages guda biyar ne Wanda idan Kai da partner ka bakuyi understanding love language da kake speaking ba to zaayi ta samun matsala. Na farko shi ne words of affirmation, abinda na fahimta shi ne mutanen da suke nuna soyayya ta hanyar zance, shi ne amfani da zallan kalmomi wajen nunawa abinda suke so soyayya, na biyu Kuma quality time, Ina ganin shi ne abinda muke lacking, yawancin mu shi ne language din da muke ji, bawai a bamu gift ba ko zancen baki a'a a bamu lokaci, duk lokacin da kake bukatar abinda kake so ya Zama he's ko she's at your disposal. Na uku shi ne gift giving, to yanzun idan kace wannan language din kake ganewa se ace Kai kwadayayye ne you building your relationship based on materialistic. Ba mayiwa kanmu uzuri, may be shi namijin language din da yake ganewa kenan, na hudu shi ne act of service, akwai Wanda zasu bauta maka, being there for you a kowanne lokaci wannan se aga kamar baka da hankali ace kenan namiji kake yiwa hakan ko kuma macen kake yiwa hakan. Na biyar shi ne Wanda I'm strongly against it shi ne physical touch is much common a westerners Amma yanzun muma hausawan mu sun dauka wannan rashin addinin da jahilcin.

Bayan na Kare littafin tas se Naga inda nake Ina cikin quality time shi ne abinda nake ganewa when it comes to love language, na fahimci Likita na a Ina yake Shima, Yana cikin act of service Dan haka min fahimci kanmu so bamuda matsala. A hankali na maida littafin na rufe sannan na janyo wayata Dan na duba WhatsApp Dina Ina budawa message din Rayhana ya fara shigowa, ciki ne da ita, na tabbatar aure na Kara modelling mutum Dan itakam ta Kara nutsuwa more matured than before. Mun Jima Muna Hira har mukai video call sannan mukai sallama bayan sunyi magana da Ammi itama.

Se yamma muka koma gida, Bayan nayi wanka na shiga kitchen Dan hada Mana dinner, Ina aikin Muna waya da likta dake fada min Yana nan isowa cikin weekend din Dan ya ganni

" Sure zaka zo? Kada ranar tazo kace min aiki ya maka yawa"

Na fada Ina juya Irish din dake cikin Mai, yayi dariya da yasa ni murmushi yace

UWARGIDAN BAHAUSHEWhere stories live. Discover now