UWARGIDAN BAHAUSHEXXVI (26)
✍️ Ayshatuuu 💛
Baba ya biyo Ammi daki, tana zaune ta maida kanta kan wani karamin littafi da take lissafi a ciki, dukda ba wai gane abinda take takeyi ba Amma kokari take wajen ganin ta nuna karfin zuciyar ta,Yana shigowa ya karbi pen din hannunta ya wulla tsakiyar gadon, ta dago idanunta ta zube cikin nashi da suke boiling da masifa, Shima kallonta ya tsaya Yi na wajen mintina uku seda tabbatar kallon yayi tasiri a kanshi kafin tace
" Baban Sofy"
Se ya samu guri ya zauna, ya riko hannunta Wanda ba Zama ta iya tuna last da yake kallonta with admiration ba,
" Me yasa Kika koyi fada, kwana biyu ne kawai zatayi ta tafi"
Ta girgiza kanta tace
" A'a taje gidan Gwoggo ta zauna!"
Ta fada tana karbe hannunta daga nashi,ya Jima Yana lallashin ta cikin nutsuwa tace ita Bata yarda ba se kawai ya Mike ya fito, ita Anty Rumasa'u tunanin ta tunda ya Shiga dakin da masifa expectation dinta ya ciwa Ammi mutunci ko ya saketa, ko ma ya daketa ita dai burinta taga Ammi ta wulakanta, ganin shi ya fito a sanyaye Kuma tunda ya Shiga dakin duk yadda ta kasa kunne bata ji Koda tarin su ba yasa hankalinta yayi mummunan tashi ba dai aikin ya lalace ba? Sede Babu me Bata amsa, akwatin ta ya dauka yace
" Muje ki zauna gidan Gwoggo!"
Ta tattaro duk wani karfin gwiwa tace
" Wanne irin gidan Gwoggo ni nan gidan Zan kwana ai na riga na fada maka"
Tsaki yayi yace
" Rumasa'u why are you so naughty, nace ba anan Zaki zauna ba"
Ya fada Yana Dan daga Mata murya, ganin ya fara hasala se kawai ta bi bayan shi kamar zuciyar ta zata fito Dan bakin ciki.
Bansan Ina Ammi ta samu karfin gwiwa ba, Amma nasan dai me hakuri Bai iya fushi ba ko kadan, nasan Ammi tayi hakuri ko nace tana kan Yi ma, Amma wannan tsakuwa da ta tauna tabbas aya taji tsoro, se Baba ya Dan dawo hayyacin shi abubuwa da dama da yakeyi se ya daina, badai su koma kamar yadda suke da ba Amma Kuma an samu cigba. Ita kuwa Bata Kara zuwa gidan mu ba, ranar Monday na raka Baba gidan Gwoggo anan na sameta ta Gama shiryawa zasu koma Funtua, kamar nayi dariya yadda naga tana ta hararata amma na Dan daidaita na gaishe ta na shige wajen Gwoggo abuna. Seda zasu tafi sannan muka wuce tare zanje Registration, tun a hanya Hira kawai muke ni da Baba. Anan ya ke tambayata
" Sofy daughter, Ummaah ta min magana akan ke da Ismail"
Na danyi murmushi Ina jin kunya tareda kallon bangaren Anty Rumasa'u dake bacci Kain da nain, se da ya Kuma cemin
" Ina jinki, tace min wai tana son ki aura Ismail ne, kin yadda?'
Na girgiza kaina Dan kada na Bari wannan kunyan yasa na cuci kaina, nace
" A'a Baba ni ba komai tsakanin mu"
Ta rear mirror ya kalleni sannan ya maida kan shi kan titi yace
" Are you sure? Bature fa?"
Gabana seda ya Fadi na sunkuyar da kaina, abinda nake ta gudu kenan wannan tambayar hi nake kamar na nutse cikin seat din motar, yayi murmushi lovingly yace
" Kar kiji kunyata, Ina son nayi coming da decision, bana son nayi abinda zai Bata ranki ko na Ammin ki"
Hakan daya fada yasa naji dadi sosae, na sauke ajiyar zuciya nace
" Ni dai Baba I want Dr."
Words din na fita a bakina ban Kara cewa komai ba, Baba ya nuna min dadin daya ji sannan yace min Bature tun Ina SS1 ya fada Masa kudurin shi Amma se ya dakatar dashi akan ya Bari se na Gama secondary Shima ba wai aure zamuyi ba Aa kawai dai ya dinga zuwa gurina mu shirya kanmu Kuma mu fuskanci juna. Sannan ya nuna min yau na riga na kulle duk wata kofar kula wani, baya son Kama ni da wani Ina dating Dole na tsaya akan magana daya. Idan ya dawo zai bawa Bature aurena officially.