UWARGIDAN BAHAUSHEXXXIII (33)
✍️ Ayshatuuu 🖤
Haka na dawo gidan bikin jikina a sanyaye, hannuna rike da wayata da Kuma novel din da ya kawo min. Dan guri na samu na zauna na cira wayar na cire ta daga flight mode da na saka ta kafin naje gurin Usman. A hankali naji Abu me dumi ya saukar min akan kumatu na, cikin sauri na goge hawayen tare da waigawa kada wani ya ganni Ina hawaye ayimin sharri ace saboda Ismail Bai aureni bane. Gaba daya se naji zaman ya gundure ni kawai so nake na kadaice, dakin su Amira naje, dake ana Shirin tafiya dinner yasa Babu mutane Dan haka na shiga toilet na rufe na tsaya gaban mirror din Ina kallon fuskata yadda ta koma so pitiful, se kawai na fara kuka tareda jingina jikina jikin bangon toilet din, nayi kukan me isata sanan na tatso wani face gel Dana gani cikin toilet trolley na wanke fuskar, Amma dukda haka tayi ja Dana fito, haka Kuma idan na tuna ya tafi se naji hawaye na Kara taruwa cikin idanuna, I wonder me zuciyata take nufi dani da zata Zama so fragile kawai Dan abinda Bata so ya tafi, Ina ce tareda ita muka hada karfi wajen ganin mun koreshi ni Ina ikirarin bana son kishiya. Ammi ta kirani na fita na same ta tace ana ta nemana tun dasun, na zauna gefenta ita da Anty Safara'u da suke hira ta dubeni tace
" Ya akai fuskar ki tayi ja, kuka kikayi?"
Na girgiza Kai nace
" A'a kaina ke ciwo"
Suka min sannu sannan Ammi tace idan bazan iya zuwa dinner ba na koma gida, nace Mata a'a zanje. Tasa aka rakani aka min light makeup a fuektaa, Ina tunanin shi ne Karan farko da foundation ta fara zama a fuskata, na zura ankon da mukai na lace maroon me Dan adon sea green a jiki. Skirt da riga nayi kamar ko yaushe Dan ita nake sawa na jini comfortable. Wajen takwas aka tafi tsadadden event center na Kano Kai kuwa abin manya, gurin kanshi abin kallo ne, sosae Yan uwanshi Yan gayu masu kudi ga sarauta na wajen baban shi suka zo. Na samu guri na zauna na maida hankali na kan littafin da Usman ya kawo min. Muna nan Babu jimawa ango da amarya Suka karaso, ko shedan ya kalla Hanifa se ya Kara kallonta ba karamin kyau tayi ba, kayan da ta saka masu duhu Dan haka fatar jikinta ta haska Kaya tayi kyau ga murmushi da take itada uwarta na cikar buri, na aurar abinda zuciya ke muradi, na shagala sosae Ina kallon su, idanuna ya koma kan Ismail that looks a bit complicated, fuskar shi Babu alamar annuri Amma dukda haka me kyau me kyau ne, yayi kyau a manyan kayan da ya saka. Suna Zama aka fara program din smoothly, ko inda nake ban daga ba seda aka fara spraying kudi sannan ne na maida hankalina kan yadda ake ruwan kudi wasu suna can Basu ci abinci ba. Haka aka tashi na fito a gajiye tikis. Ammi dama sun tafi so ta hadani da Yaya Nasir zai maudani gida, na fito dake Yana tawagar angwaye Dole se na jira sun fito, haka na tsaya gefen motar shi immersed a cikin wayata, inata kallon update din mutane bikin went viral Dan bikin famous mutane ne. Ina nan tsaye na fara jiyo dariyar su ga Yan matan amarya anata karairaya anga maza, Ina dago idanuna ya sauka akan na Ismail, nayi saurin dauke kaina Dan baisan nazo ba Kuma bana son ya sani, na maida hankalina kan wayata Ina ta lallashin Bature dake kumfar bakin naje dinner har after eleven ban koma gida ba, dagowa nayi jin kamshin turaren shi, hannun shi yasa ya amsa wayar hannuna tareda Danna lock yace
" Ashe kinzo ko liki bakiyi min ba"
Na danyi murmushi nace
" Bana spraying beside bana son kayi noticing presence Dina"
Ya kalleni looking Disturbed yace
" Me yasa kike son nunawa mutane baki Sona? Me nayi Miki sofiyya da kike kina haka?"
Na Dan gyara tsayuwaa na nace
" Dan Allah karka dakko maganar nan, ni bance bana sonka ba, I just turned down auren ka. Dalilin Kuma gaskiya bazan iya fada maka ba"