Drawing the curtains

1.6K 172 25
                                    

UWARGIDAN BAHAUSHE

FINALE

Ayshatuuu

Ya shafa kanshi yana girgiza Kai sannan ya dauka Abhi ya bini dashi, ya sameni Ina zaune na kashe wutar dakin Amma baby phone Dina na kunna touch dinta Ina rubutu jikin wani littafi. Zaunar da Abhi yayi a gefena, yaron ya rarrafo se Dole ya karbe pen din, haka na tattara na aje gefe Ina fadin to taho naji menene.

" Safiyya I said I'm sorry, why are you doing this for crying out loud"

Bance komai ba, se ya kyaleni Naga kamar ranshi ya baci ne ya fita a dakin. Ban Jima ba bacci yayi gaba damu, but cikin bacci naji yadda ake kokarin daga min hankali with those palms of his, kafin nayi retaliating yayi dominating, I can't resist Dole na bada Kai bori ya hau. Washegari ya Gama kwanan shi Dan haka ya koma wajen gimbiya sarautar Mata. Da safe na gaishe shi dukda inata hade Rai shi kuwa ko a jikin shi se wani murmushi yake, kamar na shake kaina haka nakeji na biye Masa da nayi. Yayi breakfast ya fita office. Na zauna na fara lissafin yadda Zan daidaita gidana, shi yanzun nasan bazai Kara abinda yayi min ba tunda kwana biyunnan ya amshi gashi yadda ya kamata, ita Kuma Kubra na riga na Gama da ita tunda yanzun duk abinda zata fada a matsayin makaryaciya wadda Bata son zaman lafiya take a gurin shi, I've gained his trust hakan kadai ya isheni. Ba kowanne lokaci fada yake ci ba, ba kowanne lokaci zaka dinga mita ba, mutane masu Miya they're boring, simple Abu zakiyi indai kece me gaskiya magana ta kare. Ya kamata mu fito mu gyara rayuwar mu, dukkan mu dangin miji ne, idan mun Hana wata zaman lafiya muma zaa hanamu. Me yasa maza basuda matsala kullum semu.

" Aiki zata fara zuwa Kuma? Ai bamuyi haka da Kai ba. Ka barta tana tuka mota tana daga min hanci ni banida ita, nace ka siya min kace bakai ka siya Mata ba yanzun Kuma kace zataje aiki ni Kuma na Zama me muku gadi kenan"

Ya gyara zaman shi Bayan ya Gama sauraron duk abinda Kubra ta Gama fada yace

" Na farko Zan Kara maimaita Miki, mota ganinta nayi da abar ta, mahaifinta ya siya Mata banida right da zance ba zata tuka mota ba, ni sauki nane ma ta Kai kanta inda take so. Na fada Miki bazan siya Miki mota ba saboda banida wannan halin yanzun. Duk inda kike son zuwa Zan kaiki ko nasa a kaiki. Na biyu Lokacin da na aureta ta Gama karatu, tayi karatu babanta ya dauki nauyin karatun ta ya Samar Mata aiki ban Isa nace a'a ba, ban Mata wahalar komai ba Dan haka akan wannan bazan tauye su ba. Da na aureki secondary kawai Kika Gama, banmiki zancen makaranta ba, kema Kika nuna Baki damu ba, to kin gani ba yadda zakiyi sede kiyi hakuri"

Ta Bata Rai tace

" Haka ma zakace? Ni fa sede na koma makaranta"

Yayi dariya Yana kallonta yace

" Allah ya bada saa"

Kamar Wasa ta Kade ssce dinta ta fara neman admission a GSU, ni banma San me suke ciki ba na riga na fara aikina Kuma na jona masters dina, seda akazo jamb sanann ta gane kanta ya kwanta bataia making ba Dan haka ta fara neman college of education Allah ya taimaka ta samu ta fara karatu, gaba dayan mu se muka Zama very busy into our lives kowa na neman na kanshi bamu da lokacin Zama muyi fada, mussaman ni idan bana gurin aiki Ina gurin research work Dina. A hakan lokacin yayen Abhi yazo na aika shi wajen Mama ta yaye shi daga haka ta rike shi.

" Seda nace kikai shi gurin Ammi Amma Kika nace ke gurin Mama, yanzun gashi Taki bada shi"

Nayi murmushi nace

" To meye abin fadan Kuma, I wanted space dama yazo ya hanani na maka abubuwa da yawa"

Yayi dariya yace

" Sharri Zaki Masa! Yaron da Babu ruwanshi"

Nima nayi dariya Ina Kara rike wayar a kunnena nace

UWARGIDAN BAHAUSHEDove le storie prendono vita. Scoprilo ora