UWARGIDAN BAHAUSHEXXII (22)
✍️ Ayshatuuu 💙
Na Kara kallon motocin nasu sannan nayi murmushi, Dan a raina nasan dukkansu sunyi zuwan banza. Gurin Yaya Fahad na fara zuwa na bude bayan motar na zura paper bag din hannuna sannan na gaishe shi, baima lura Dani ba Dan gimbiyar shi na gaban shi. Inda Dr Bature yake na nufa Ina kallo Yana duba agogon dake daure tsintsinyar hannun shi. Da murmushi nace
" Ka gaji?"
Yayi saurin dagowa yace
" Ni bance ba, I was scanning my eyes Naga ta inda Zaki bullo"
Nayi murmushi Wanda indai Muna tare na dinga yi kenan bansan dalili ba, duk lokacin da muke tare se naji I'm Happy, Ina jin yanayin yafi kowanne dadi da tsayawa a Rai, lokuta da dama nakan zauna Ina rewinding maganganun da mukai sede kawai na dinga murmushi ni daya kamar tababba!
" Tunanin me kikeyi?"
Ya fada yana waving hannunshi akan fuskata, nayi saurin girgiza Kai nace
" Baba ne yace kazo? Yaya Fahad already yazo ha Yaya Ismail ma"
Se ya gyada Kai yace
" Oh baisan zasu zo ba shiyasa yace nazo, yaje Zaria ne"
Nace Masa I see sannan na raka shi inda Yaya Ismail yake zaune cikin motar shi, tunda muka taho na fara jin karfin idanun shi a kaina, Amma Bai dameni ba hirar mu kawai muke nida doctor har muka karasa. Dan knocking nayi a window, yayi wining din shi kasa nace
" Yaya Ismail!"
Ya Dan yatsina fuska sannan ya fito, ya mikawa Bature hannu Suka gaisa, ni nayi introducing din su ma junan su, kafin nace
" I'm sorry duka kunzo, Yaya Fahad already yazo"
Bature yace Babu matsala Bari yaje su gaisa da Fahad din kafin ya wuce, ya tafi na dubeshi nace
" Why did you come unannounced? Kasan Baba zai turo a dauke mu ko"
Maimaikon ya amsa tambayar Dana Masa se yace
" Who's that guy I don't like him!"
Nayi saurin dariya nace
" Ba Dole se kaso kowa ba, beside Shima he'll not like you"
Ya Dan karkato kanshi daidai kunnena yace
" I'm not here to impress anyone but you"
Na tabe baki na Yi gaba abuna, da sauri ya kulle motar ya biyoni, muna zuwa Bature yayi Mana sallama ya tafi, na Kara binshi na barsu da Ismail dake ma Fahad korafin me yasa zai zo daukar mu duk ya Bata Masa plan din shi, yasan Kuma bazan taba binshi ni daya ba. Seda ya daidaita seat belt dinsa kafin ya Miko min karamar leda da kwali a ciki, na kalleshi Ina girgiza Kai, se ya zare min idanu da yasa nayi dariya na karba, Shima yayi dariya yace
" As I promised ni Zan fara saya Miki waya. Gata nan komai is set a ciki"
Na kalleshi na kalla wayan na rungume ta a kirjina Ina kallon shi se Naga ya lumshe idanun shi nace
" Thank you so much! Amma me yasa ka saya min Baba zai saya Mana fa"
Ya danyi murmushi yace
" Na sani wannan shi ne gift dina gareki, kije ku tafi karki dare"
Na gyada Kai na na Kara Masa godiya sannan mukai sallama ya tafi. Ina zuwa na azalzali Yaya Fahad akan mu tafi, ai Yaya Ismail yace Shima nan zai bar motarsa ya Kira wani mutum anan malumfashi zai zo ya Kai Masa Kano, nayi tsaki na shige Bayan motar ya biyoni ya zauna gefena, hakan Yaya Fahad da Rayha na dariyar fushin nawa Suka shiga muka dauka hanya. Duk yadda yake kokarin Jana da Hira naki bashi hadin Kai, se ya kyaleni but I can sense the disappointment a yanayin shi. Hannun shi ya kai kan paper bag dinnan zai bude nayi saurin dauke wa nace