XLII

1.1K 216 11
                                    

UWARGIDAN BAHAUSHE

XLII (42)

✍️ Ayshatuuu 🤎

Ba komai ke zuwa maka a matsayin pleasure ba, rayuwa gaba daya trial and test ce. A hanyar da kake tafiya zaka hadu da tudu da gangare, yau zaka ji dadi gobe zaayi akasin hakan, bazai zaman kullum yadda kake so haka ce zata kasance ba, wani lokacin ma abinda kafi ki shi Allah yake baka Dan ya gwada imanin ka, Dole kayi accepting whatever life throws at you and you cannot question Allah akan hukuncin shi.

Nayi karatu na novels kala kala, romantic da genres kalakala, na karanta yadda ake samun pleasure a gidajen aure dukda ni nasan aure is not all about pleasure tunda Ammi ta Isa ta zame min misali akan hakan, Amma zuciya kullum tunani take tana hasaso Abu mai dadi, ban taba kawowa ba zanje da gaske in tarar da UWARGIDAN BAHAUSHE cikin gidan Usman Dikko tana jirana.

" Yusra! Yusra!! Yusra!!!"

Cikin sauri Anty yusra ta fito hannunta rike da babyn ta Dan kwana ashirin jin Kiran da mahaifiyar ta take Mata Babu ji Babu gani, ita tunanin ta wani abun ne yasa ta fito tana fadin

" Mama lafiya kike Kirana?'

Ta fada tana Zama kan kujerar dake facing wadda matar ke zaune, duk inda kake Neman mutum karami ka sameta to ka koma ka samu, ta dubi yusra tace

" Bazan kiraki ba seda wani dalili? Ke me nake ji kamar Hamman ku zaiyi aure?"

Anty yusra ta sauke ajiyar zuciya tace

" Kai Baki sani ba? To ai Banda an Kara sati uku da tuni Nanda sati biyu anyi"

Ta kankance idanu cikeda fada tace

" Ni meye amfanin zamana a gidannan kenan? Har ni zaa ware ko ni ba uwar shi bace ai dai na rike shi"

Anty yusra ta girgiza Kai tace

" Mama wallahi ki daina haka, kin manta Hamma yazo zau fada Miki Kika ki bashi fuska"

Ta tabe baki tace

" Ina ce dai ba yarinyar matsiyata zaije ya Kara dakkowa ba kamar yadda ya auro Kubra?"

Ita dai Anty yusra se ta fara breastfeeding babynta kawai ba tareda ta amsa ta ba, haushi ya Kara Kama Mama yace

" Banza Kika min kenan? Irin banida amsa ko? To Kin kyauta"

" Mama ni ta Ina Zan San matar shi Dan Allah? Kuma meye damuwar mu da wani kudi ko rashin shi, itada ba ita zata ciyar dashi ba . Kede kiyi addua kawai ta gari ce"

Mikewa Mama tayi tana fadin

" Ai ya kamata a bani girma a fada min, ko ban Haifa ba ai na rike. Kuma yarinya Yar arziki ai yafi bangirma ko ba komai kace kasan manyan mutane, da namiji da Allah Bai bani ba bawai baya Sona bane ba."

Sanin halinta yasa Anty yusra Bata Kara ce Mata komai ba, Itafa Mama Bata taba haifar namiji ba, duka yaranta mata ne gaba daya. Shi kadai ne namiji, Amma idan kuka ji yadda take buri akan matar Dan ta zakiyi tunanin gobe zaa ce zata haifa namiji.

Ammi kullum maganar ta yadda bikina zai kasance, da yake ni ba mutum bace me high taste dinnan ba yasa ko siyayya idan zataje sede suje itada Anty Safara'u ko Anty Siyama kanwarta da Rayha. ko sun dawo sede na kalla kawai nace yayi. Bikin saura sati uku Gwoggo ta fara rashin lafiya Dole aka daga bikin, ga Kuma exams Dita da zanyi finals. Dan haka na Dan samu lokaci na nutsu na fara exams. Sati biyu na Gama exams Dita na Zama cikkakiyar vetenary doctor ko nace likitan dabobbi, kaf class din mu mu uku ne Mata, mukai applying Kuma ni kadai na Gama. A matukar gajiye Baba da Ammi suka sameni, Ina ganin Baba na tafi na rungume shi, ya shafa kaina tareda fadin

UWARGIDAN BAHAUSHEWhere stories live. Discover now