LVII & LVIII

1.3K 220 10
                                    


UWARGIDAN BAHAUSHE

LVII & LVIII (57 & 58)

✍️Ayshatuuu💛

Wutar dakin ya kunna ya tsaya Yana karemin kallo na wani lokaci kafin ya hayo gadon ya kwanta Bayan ya kashe Kwan. Hannunshi yasa ya zagayo kuguna dashi, dayan Kuma yasa cikin rigata, ya sani it's something that weakens my soul and body, ya riga yasan Lago ne, ganin zai fara min wasu abubuwa yasa nasa hannuna na buge nashi. Cak ya tsaya tareda fadin

" Bakiyi bacci ba?"

Ya tambaya da mamaki a muryar shi, Wata zuciyar na fada min nayi hakuri kar nayi magana na nusa Masa bacci nake  Amma na kasa hakan saboda Gani nake zuciyata bugawa zatayi na mutu kafin safe, Abhi is what will make me live, na tashi na zauna tareda daukar wayata na kunna fitilar Dan ya ganni na ganshi ayi wadda zaayi.

" What happened to your face? You cried?"

Ya tambaya saboda yadda idona ya kumbura fuskata tayi ja, haka fuskata take ko tashin hankali kwakwara ba shiga se tayi ja.  hannunshi ya Kai Yana kokarin caressing fuskar na dauke kaina se hannunya sauka a kasa. Kawai se na fara kuka nace

" Na Bata maka gidan ka, tunda nazo ka rasa zaman lafiya! Amma Ina son ka tuna ni bani na dinga binka ka aureni ba, Kai ka dinga Bina kana son ka aureni..."

Hannun shi yasa a bakina Dan nayi shiru saboda muryata ta fara sama alamar Raina yakai kololuwar baci, cizon hannun nayi yayi saurin daukewa Yana yarfe hannun, alamar na ciza da yawa. Na cigaba da fadin

" Na fada maka matar daka aura shekara dari da wadda ka aura kwana daya hakkinsu daya, me kake nufi dani, zaka nunawa kishiyata bamu zaman lafiya, whatever you will do muyi shi ni dakai stop involving her, lemme tell you this duk abinda kake min Allah Yana kallonka and at this rate nayi Dana sanin aurenka!Kuma idan Kun hada Kai Kun zalunce ni Allah ya Isa tsakanina da ku."

Ina Gama fadar hakan na dira a gadon na dauki Dana da wayata na barshi a zaune tamkar mutum mutumi, he always says I'm stubborn I'm sure Bai taba tunanin haka ba Dan ko ni ban taba tunanin zai iya min hakan ba. Ina kwantar da Abhi ana dauke wuta, gashi dakin shi ne kawai Babu sauro a part Dina. Nayi shiru Ina tuna fadan da aka min da zaa kawoni, cewar no matter what kada mu raba daki, kada Naga daki uku gareji, Amma yau bazan iya ba, bazan iya kwana dashi ba balle har ya taba ni. Nayi kamar na koma dakin saboda tsiron kada sauro ya ciza Abhi Amma na hakura, Hawaye wani na bin wani na nufi dakina na dakko net dinsa na Masa shimfida nasa shi ciki ni Kuma na zauna tareda saka kaina cikin gwiwata na dinga kuka, saboda inajin shi kadai zai saka zuciyata ta warke daga radadin  da take. A hankali naji ya rungume ni ta baya Yana buga bayana, I needed wani ya lallashe ni a lokacin to tell me everything will be ok, Amma ba daga gurin shi nake bukatar hakan ba, hakan yasa na ture shi da duk karfina na tashi tsaye na nufi Abhi Dan na dauke shi, se yayi saurin rikeni muryar shi a hankali yace

" Safiyya you can't sleep here, akwai sauro da yawa. Idan Baki son mu kwana tare ni Zan bar Miki dakin. I'm very sorry"

Nai Masa banza na cigaba da goge hawayen dake fita, wannan sorry da yace kara Bata min Rai take. ya gaji da tsayuwa yaga na ma kwantta kan dandanin carpet, yasan Raina ya Gama baci kenan, Dan ko baccin Rana zanyi nafi son najini in comfy of my bed. Ya janye jikin shi ya koma can Kan kujera zai kwanta se Kuma ya fasa ya tafi dakina Dan yasan na hanashi kwanciya akan kujera saboda saurin lalacewa, lokacin idan na fada Masa haka se yace gori nake masa. Na sauke ajiyar zuciya wadda tunda kukan ya dauke nake sauke ta akai akai, a hankali na fara tunani how much I don't know life, I'm not so much exposed into this world, nayi tunanin Amarya ke cutar uwargida, nayi tunanin duk namiji Yana tarewa wajen amaryar shi ya takurawa UWARGIDAN shi kenan abin ba haka yake ba, a kowanne rank kike Zaki iya cutar abokiyar zaman ki. Naki auren Usman saboda kada daukina yasa ya cuce ta se gashi uta take cuta. Ni a gurina Babu zancen nayi hakuri, wannan idan na cigaba da dauka ba hakuri nake ba hauka nake Dan haka tun kafin Abu yayi nisa Zan nema ma kaina mafita. Alwala na tashi nayi Lokacin da dare ya tsala na shimfida sallayya na fara sallah mostly idan na fara addua se na fara kuka, haka se da nayi asuba sannan wani bacci me karfin gaske ya tafi Dani wata duniyar. Wajen Tara na Mike a gigice saboda kukan Abhi, nasa hannuna na Ciro shi Ina rarrashin shi na fara feeding dinsa Ina dudduba ko sauro ya cije shi kamar yadda ya cije ni, I felt relief da naji Bai cije shi ba. Kamar yasan jiya Babar shi na cikin masifa ko farkawa baiyi ba I'm very grateful for that. Cikin sauri na mishi wanka Nima nayi, nasan ya Dade da fita Dan naji tada motar shi Amma kuma kafin ya fita har pecking Dina yayi a goshina sannan ya lulluba min quilt ya fita. Ina Gama shiryawa na sakko da trolley na bude wardrobe na loda Kaya a ciki na Goya Dana na jawo kofar na fita ban dauke ko quilt din da na lulluba dashi ba balle shara ko kintsa gurin.

UWARGIDAN BAHAUSHEWhere stories live. Discover now