XLVII

1.1K 191 7
                                    


UWARGIDAN BAHAUSHE

XLVII (47)

✍️ Ayshatuuu 💕

*Note that Ramla kanwar Ismail ce, Amira Kuma kanwar Hanifa ce! FAQ answered!*


Har me napep din ya fara kokarin ja, ta tsayar dashi tunawa da tayi Babu kudi hannunta, a hannun Amira da har lokacin take tsaye ta karba kudin sannan ya nufi race course da ita, tunda Suka nufi gidan ta hango motar Ismail Yana reverse da alamar zai bar gidanne, ta rufe fuskar ta yadda bazai ganta ba, shima dake Kai ya dauka caji Bai ma lura da ita ba. A kofar gidan ta fito hannunta rike da sabuwar halittar da ya kamata ace a killace take Amma se gata ana yawo da ita cikin napep. Ta sallameshi sannan ta nufi cikin gidan, tun daga kan security Suka fara gaida ta saboda sanin matsayin ta, kowanne mamakin me ya fito da ita itada aka ce ta haihu Daren jiya, straight parlor ta wuce sede dama tun a compound din gidan ta lura da motoci uku baki tana Kuma saka ran cewar barka suka fara zuwa se kace ba ita ta haihu ba.

" Kaya sunyi kyau sosae Hajiya Furaira, ni se Naga kamar nata sunfi na matar tashi kyau"

Abinda ta fara ji kenan kafin ta saka kafarta cikin parlon, Bata ji me Ummaah tace ba Dan tsayawa tayi cak se sun Gama magana ta far musu,

" Ai ni nayi mamakin hada auren da Kika Yi, me Zaki da yarinyar da uwarta ta shanye ubanta, ai da Hunaynah ita ce daidai class din Ismail wallahi"

Ina Hanifa kasa cigaba tayi da jin abinda suke fada, wato da gaske dao aure zaayiwa Ismail dinta, ta girgiza Kai ta shiga ciki ta manta ma me ya kawo ta gidan, kawai ganinta Ummaah tayi da jaririya a hannu, ta dago ta kalleta sannan ta kalla kayan dake gaban ta na idon duniya tace

" Uwata lafiya? Na zata zaku wuce gidan jidda ne"

Aje yarinyar Hanifa tayi a gefe tana duban kayan tana jin zuciyar ta na wani irin tafasa kamar zata Kona kirjinta, se huci kawai take ta dubi Ummaah da sauran matan dake Mata kallon mamaki tace

" Banji daidai ba ko? Bawai Ismail Zaki aurawa wata ba ko? Kice min kunnena yaji ba daidai ba"

Ummaah ta Mike da kyar saboda yadda ciwon kafar ta ya tsananta kwana biyu, ta mayi booking appointment a wani asibiti dake America zataje a dubata, tana jiran ayi bikin Ismail a Gama ne.

" Hanifa kalleni ni saarki ce? Ni Zaki zo kina yiwa dibar albarka?"

Hannunta tasa a kunne ta rufe tana girgiza Kai tace

" Kinsan ke ba saata bace Zaki Shiga hurumin aurena? Meye matsalar ki da ni da Zaki ce se ya Kara aure, Bari kiji kuskure na farko da kikai shi ne hada auren mu da shi, wallahi Babu wata mace da ta Isa ta shigo gidana da sunan matar shi sede Yar aiki!"

Bata ankare ba taji Mari a fuskarta, Ummaah is still Ummaah, wannan izzar tata tana nan Babu inda taje, Hanifa ta rike kuncinta Dan Marin ya shige ta, ta Yi kan kayan da aka hada ta fara rarumar turarrruka tana fasawa cikin tsakiyar parlon, Hajiya zaituna ta fara kokarin rike ta Amma yadda kuka San karfin mutane ne aka hada Mata. Ummaah ta daka Mata tsawa tace

" Hanifa ki maida hankalin ki, ko uwar ki jidda tayi kadan ta Hana airennan balle ke"

A hankali taji hancinta ya shanshano Mata kamshin turaren shi, ta yadda Parket din oil rolls din dake hannunta ta juyo, shi dinne a tsaye Yana binta da kallo Yana kallon yadda parlon ya hargitse ga kamshin turarrruka da idan ka Shaka se sun saka ka mura, ta taho gareshi a hanzarce tareda rungume shi ta fara kuka tana fadin

" Kasan Ina sonka, kace Mata baka bukatar wata matar, ni kadai na ishe ka"

A hankali ya banbareta daga jikin shi sannan ya Isa inda Yar shi ke kwance ya dakkota ya fita daga parlon, Babu yadda Hanifa ta iya face tabi Bayan shi, a ranta taso ba yanzun yazo ba seda ta Kona kayan tukunna. Gidan Anty jidda ya kaita kamar yadda Suka tsara tun kafin ta haihu, ta riko hannun shi Jim tunda Suka taho ko uffan Bai ce Mata ba,

UWARGIDAN BAHAUSHEWhere stories live. Discover now