XLV

1.1K 194 12
                                    

UWARGIDAN BAHAUSHE

XLV (45)

✍️ Ayshatuuu 💚




Tunda na saka kafata gidan Albi, duk lokacin da Ammi zamuyi waya da ita to se tayi min nasiha akan hakuri, ta fada min Zama da wata babban kalubale ne Wanda idan Ina ganin na sani to ban sani ba, tunda ita da Anty Rumasa'u basu ci talata da laraba tare ba, dukda haka an samu matsala balle ni da muke tare. Nayi hakuri dukda tasan yanzun banida hakuri dangin ubana sun canja min halayena gaba daya, ku kanku kunsan da ba hakan nake ba.

Bayan ansha ruwa se naji kaina na yimin masifar ciwo, da kyar na Dan taba abinci na tafi daki na kwanta, bama bacci nayi ba Amma dai kawai nayi shiru ne Ina tunanin rayuwa, se Dana ji Kiran sallah sannan na tashi nayi sallah anan cikin bedroom din, Ina zaune naji sallamar shi, na dago Ina amsawa har ya karaso ciki, Zama yayi gefen gado yana kallona yace

" Kinsha ruwa lafiya?"

Nace

" Lafiya Lau! Kaima kasha lafiya?"

Ya gyada kan shi sannan yace

" Naga kamar Baki ci abincin ba, are you ok?"

Hannuna nasa na rike kaina nace

" Ciwo yake min ne"

Dakkowa yayi ya dawo gefena tareda zare hijab din jikina ya taba wuyana da goshi na, inata kallon shi Yana bin skin Dina da hannun shi Dan yaji temperature Dina, se naji zuciyata tayi melting, na rike hannun shi Ina Dan murmushi nace

" Ba fever nake ba, ianga stress ne Nasha magani fa"

Se ya saki ajiyar zuciya yace

" Ki huta kinji, if there's anything just call me kinji ko?"

Na gyada Kai na se ya Mike tareda kissing hannuna dake cikin nashi ya min seda safe, Bayan shi na bi na rufe kofar sannan na tattare kayan dake parlor na Kai kitchen na koma daki na kwanta, bansan dalili ba kawai se na fara kuka, na rufe fuskata da hannuna Ina kuka a hankali a hakan bacci ya daukeni. Ko da na tashi da asuba da zazzabi na tashi, Amma haka na daure naje nayi alwala sannnan na Nika ayar dake jike tun jiya, na hada komai se naji ana taba kofa, ya bude ya shigo ckin Ash jallabiyya, na gaishe shi ya tambayi jikina na amsa da sauki sannan ya tafi masallaci, Nima se nayi sallah sannan na zuzzuba cikin robobi na mayar cikin fridge, nayi wanka na koma na kwanta Ina jin zazzabin na raguwa, wajen bakwai na tashi jin wayata na ringing, na duba Naga Albi ke kira,

" Ki fito zamu tafi masallaci yanzun"

Na tashi na zauna nace

" Ban shirya ba ai"

" To mu zamu wuce kawai se min dawo"

Ko Allah ya kiyaye ban ce Masa ba na aje wayata na Mike Ina jin Raina ya fara baci, ya kamata tun jiya ya fada min zamuje masallaci na shirya da wuri Amma seda ya fito tukun zai ce na fito, koma ba zai fada ba ya kamata ya fada min da ya shigo da asuba. Na tashi na gyara gadon, nayi shara na gyara gidan sannan na dawo na sake wanka na fara neman kayan da Zan saka, wani farin lace na hango na fara kokarin janyo shi se na fasa na dakko wata brown shadda da aka hada min a lefe na, dinkin skirt da riga aka min, da bead work me kyau, na saka a jikina nayi barin turare, na gyara fuskata da gashina sannan na wuce kitchen nayi wanke wanke, abincin da ban ci ba na juye a wani kwano na saka hijab na bawa me gadi, Yana ta min godiya na koma ciki na kunna turare sannan na daura dankwali Wanda gashina dake daure da band ya samu damar fitowa. Parlo na zauna nayi tilawa sannan na janyo wani SciFi novel na fara karantawa, anyi basing dinsa a Mexico, suke tada wani beast ya tashi ya addaba gaba daya garin. Ina daga zaune naji parking din motar shi, na Mike na Nemo katon baho na juye zobon da kunun ayar duka sannan na dawo na zauna, wajen after ten minutes Ina jiran shigowar shi Sega Amna a guje ta shigo, ta riko hannuna

UWARGIDAN BAHAUSHEWhere stories live. Discover now