AFIYYA 1

712 47 8
                                    

💔 AFIYYA 💔

One (Free page)

✍️ Ayshatuuu 💙


RINGIM, JIGAWA STATE.

Taken mu a kullum shi ne " Jinin dabo ringimgim da ka garin karamci" mun amsa wannan taken Dan mu mutane ne masu karamci da dattako, masu riko da alada, garin me ruwa, me kifi Wanda suka San kansu a wajen noma. Bari na barku hakan kada kuce na Koda garin mu da yawa, believe me idan kuka je ringim zaku San ba karya nake ba.

Sunana Amina Abubakar Salihu, Amma anyi min lakani da AFIYYA kasancewar na ci sunan kakata data haifi babana ne. Kakana Alhaji Salihu shi ne wazirin sarkin ringim kunga kenan na hada jini da sarauta. Na kanyi tunanin Anya infertility wato rashin haihuwa baya running cikin zuriar mu? Ko Dan ba hakan ya kamata nace ba , zance tabbas infertility na yawo cikin familyn mu. Dukda haihuwar ana yinta sede batada yawa, da anyi daya shikenan, se ta tsaya. Hajiya Amina ita ce kakata, asalinta mutuniyar Ganjin gebi ce. Ita kadai ce matar daya aura Bai Kara Kuma wani auren ba. Yaranta su biyar ne. Mahaifina Abubakar shi ne babba se Wanda ke bi Masa kawu Sa'idu, se Yar tsakiyar su Mummy Maryam, me bi Mata se kawu Ahmad ana ce Masa Tijjani  autansu Uncle Salihu amma Babawo ake Kiran shi, my very own savior.

Kamar yadda muka sani lokacin da westerners Suka kawo karatun boko an fara dauka ne daga gidajen masarautu Dan a bada misali ga sauran alumma su biyo baya. To mu dinma hakan ce ta kasance lokacin da yaran sarki zasu tafi se aka hada da Babana da Kuma Kawu Sa'idu aka kaisu. Hajiya Bata so saboda tana ganin kamar wani Abu ne ake son koyawa Yara Dan a dauke hankalin su akan turbar musulinci. Da kyar aka samu akai convincing dinta ta amince Suka tafi makaranta, sede kawu Sa'idu fur yaki idan an kaishi se ya gudo ya tafi gidan Gwoggon su dake kyarama, duk kuwa da tsakanin Ringim da kyarama akwai tazara Amma hakan zai gudu. Idan mahaifina ya dawo yayiwa Hajiya complain tayi fada Amma a banza tunda ita Baso take ba Amma tana ganin Dole tayiwa waziri biyayya, Kuma ba zata so yayanta Suki Masa biyayya ba. A haka aka Gama karatun Babu abinda kawu ya tsint, da waziri ya fahimci hakan se kawai ya kaishi kasuwa yace gwara ya nemi abinyi kada ya ja Masa magana a gari. Nanma Babu wani abinda yake illa yaje yayi shawagi ya tafi yawon shi, sede a wañnan shekarar baya ga waccan budurwar baya ga gidan wane, Kuma kowa saboda darajar waziri yake kyale shi.

Daddy a kings college dake Lagos anan yayi secondary School din shi, Yana gamawa aka bashi offer Amma se yaki karba akan shi fa se yaje ya Karo karatu. Hajiya Babu yadda batayi dashi ba Akan yayi aure Amma yaki. Haka ta kaishi Kara wajen fulanin sarki se ta nuna Mata itama fama take da nata dan maslaha kawai su kyalesu suyi masu addua.

Mahaifiyata sunanta Halima, ban taba ganin ta ba, asalin ta Yar shehun borno ce, akai alliance Akan zaa hada auren yayarta da Baba Mustapha Dan sarki Wanda yake saan Abbuna ne Kuma tare suke karatun acan UK. Yayar ta ita Kuma Mariya, da zasu zo aka saka mamana ta Mata rakiya, bayan an gama komai se sarki yace ai tunda Halima tazo se a hadata da da Abbuna tunda Suma Yan uwa ne. Haka akai aka daura aure mazan na can wata duniya, kowanne se gani yayi an aika Masa da matar shi. Abbu yace min Bai taba ganin mace kyakyawa kamar mahaifiya ta ba, me hakuri da juriya irinta ba. Ya fada min zamansu Zama ne sukai Akan fahimtar juna da soyayya.

Shekara na zagayowa Ummin Istanbul kamar yadda muke ce Mata ta haihu Amma mamana shiru ko Bari babu, wannan haihuwar daidai Gama karatun su Suka dawo Nigeria, precisely Ringim, sosae aka tarbesu aka nuna jin dadi musamman haihuwar Ummiey ta dada musu. Anan suka cigaba da rayuwa, Abbuna ya samu aiki a Lagos ga damuwar da mamana ta saka a ranta na rashin haihuwa se aikin yazo Masa da Dadi yasan zata Dan ji Dadi idan tayi nisa dukda bawai takura Mata ake ba, Hajiya me tsananin Kara ce Kuma ta fada min Bata taba suruka ta gari ta kirki me Kara da kawaici who owns a golden heart irin mahaifiyata ba. Baba Mustapha da Ummiey se Suka bar kasar gaba daya, a hakan rayuwa ta cigaba da tafiya.

Bangaren Kawu Sa'idu yayi aure matar shi Zinatu, a yawon shi ya samo ta Yar Kano ce Muna kiranta Ummaah, a yanzun bazan ce muku komai akanta ba Amma nan gaba kadan zaku gane irin rawar data taka wajen lalata rayuwata, idan Babu Ummaah cikin labarin AFIYYA to labarin bashi da amfani. Kawu ba karatu yayi ba , shi ba Sanaa yake ba sede standing order da Abbuna yayi Masa duk wata akwai amounts din da yake bashi, dukkan yayan shi Abbuna yake daukar nauyin karatun su. Shi ne kadai Wanda ya haihu da yawa, Ina tunanin kamar ma ya riga Abbuna yin aure. Danshi na farko sunan sarkin Ringim gareshi shi ne aka Kiran shi Baba, na biyu shi ne Yaya, sunan waziri gare shi, bazan taba manta Yaya a rayuwa ta ba, mutum me alkhairi Wanda yaci sunan me sunan shi. Ta uku sunan Hajiya ne da ita ana kiranta Mino, se Siyama se Hafsa. Banda saa a gidan na girmi Hafsa Siyama ta girmeni. Haka yaran shi suke. Mummy Maryam tana auren daya daga cikin yayan sarkin Ringim tana zaune a NY yarinyar ta daya Rukayya muna kiranta Rooks. Kawu Tijjani yana Kano da matar shi Anty Salma, yarsu daya Basma se Uncle Babawo shi ne a UK precisely a Lancashire yake. Shi Bai ma tana haihuwa ba.

Abbuna seda sukai shekara ashirin Basu haihu ba, Abbuna yayi kudi,ga ilimi gashi successful business man Amma Babu haihuwa har ya gaji da zuwa asibiti suka fawwalawa Allah. Se at the last minute da suka fitar da Rai sannan kamar Wasa mama ta fara laulayi suna zuwa asibiti akai confirming ciki gareta. Bayan kwana biyu Suka tafi Germany rainon ciki. Kowa yaji labarin cikin se yayi farin ciki Banda Wanda suke adduar Allah yasa kada ta haihu idan Abbuna ya mutu gado nasu ne. Saura sati daya a haifeni waziri ya fara rashin lafiya kamar zai mutu. Dole Abbu ya tafi Nigeria Dan sadawa dashi, Ashe rashin lafiyar ba ta tashi bace kwanan shi daya da zuwa ya rasu. Wanann sakon da ya samu Mama se ya sata ta fara labor, dama tasan cs zaa Mata tunda ta Dade Bata haihu ba. Take aka shiga da ita ot baa fito ba seda sabuwar halitta wato ni! Seda mukai sati daya sannan Abbuna ya dawo jikinta yayi sauki muka dawo Nigeria, a wannan dawowar  gaba daya Babu wani dadi, Mama taso waziri ya ganni ya rike no kamar yadda yake Mata nasiha kullum cewar watarana zata hahihu zata dauki danta a hannunta. Se gashi lokaci yayi Amma baya da Rai. Abbu ya saka min Amina, Mummy Maryam ta saka min AFIYYA lokacin tanada tsohon cikin Rooks. Mama Bayan zaman makokin ya lafa ta tafi borno seda ta zubar da wanka sannan ta dawo. Rasuwar waziri ta girgiza mutane sosae nan akazo tunanin Wanda zaa bawa sarauta kowa ya nuna Abbuna yake so Amma se wasu suka nuna ai baya Zama balle a bashi, why not Kawu Sa'idu. Shi dinma so yake a bashi Kuma ace Yana cikin council members na emirate ai yayi gaba kawai. Hakan Bai kasance ba aka bawa Abby shi Kuma se ya wakilta kanin waziri kamar yadda Hajiya ta fada Masa. Wannan abin ya Kara Bata ran Ummaah da kawu Sa'idu.

Satin Mama biyu da dawowa muka koma Lagos muka fara sabuwar rayuwa, idan ka kallesu ka kalleni zaka Yi tunanin ni din jikar su ce ba Yar su ba, Dan sunyi girma ace ni din Yar su ce. Na samu gata na samu tarbiya na Kuma samu jin Dadi sede Bai daure ba, Allah ya yanke min hakan ya jefo min wata hanyar da zanbi Dan ya gwada imanina. Shekarata daya Mama tayi rashin lafiya kwananta biyu a asibiti Allah ya Mata rasuwa.


AFIYYA is not free! Pay through 3091721807, Aisha Hassan kwalam, First bank of Nigeria (FBN). Send evidence of payment through 09063467258.



Ayshatuuu

UWARGIDAN BAHAUSHEWhere stories live. Discover now