Babi na biyu

170 9 0
                                    

A hankali take buɗe idanuwanta da suka yi mata wani irin nauyi haɗe da zafi. Cikin ikon Allah ta yi nasarar ware su tar a kan fuskar Hajja da ke ta kokarin tayar da ita dan ta yi sallar asuba.

"Kin ga Rumana ki tashi ki yi sallah lokaci har yana nema ya wuce. Ni ma kaina yau irin barcin nan naki na asara da kike yi a wasu lokuttan shi na yi. Ko da na tashi har an daɗe da sallame sallah a wasu masallatai, ga kuma Mamarki  ta shigo tana nemanki ta ce ki shirya yau tare zaku tafi shago.

Jin maganar Hajja ta karshe da ta  ambaci sakon Mam ne yasa ta ɗan ja tsaki tana mai kallonta da kumburarrun idanuwanta cikin wani irin yanayi mai nuna alamar jin haushin tsohuwar haɗe da tausayinta. Saboda ganin yanda take yin wasu abubuwa tana nuna kamar ta san dukkanin abubuwan da ke wakana a rayuwarta.

Ta ya zata fara gaya ma Hajja cewa bata san komai dangane da rayuwarta ba. Ta ya ya zata fara sanar da ita cewa a duk lokacin da take irin wannan barcin da ta kira na asarar ba yin kanta ba ne? Ta ina zata samu bakin sanar da ita cewa a duk lokacin da take irin wannan barcin  na asarar,a  lokacin sheɗan yana nan saman kan mahaifinta yana kiɗa masa ganga mafi sharri daga cikin gangunnansa?.

Wasu irin hawaye ta ji sun ziro daga idanuwanta na tausayin kanta da kuma dattijuwar da ke tsugunne a gabanta.

"Hajjah dan Allah ki gaya min gaskiya, ki gaya min shin da gaske ne Baba da Mama ne suka haife ni ko a wani wuri suka samo ni?"

Wani irin abu Hajja ta ji ya soke ta tun daga kanta har zuwa ƙafafuwanta.

"Me ya dawo da wannan maganar kuma Ummu Rumana, me ya dawo da zancen nan naki da baya da kai baya da gindi?"

cikin kuka Rumana tace.
"Ni ki gaya min gaskiya kawai Hajja, ki gaya min dan Allah. wallahi ina ji a jikina kamar basu suka kawo ni duniya ba. Hajja ki gaya min dan Allah na rokeki." Ta ƙarashe cikin wani irin yanayi mai wuyar ganewa.

"Wa ya kawo ki duniya banda Ibrahim da Salamtu. Rumana wallahi su ne suka kawo ki duniyar nan. Kaddararki ce kawai ta zo a haka ta samun iyaye irinsu da basu ɗauki rayuwarki da ko wane irin muhimmanci ba."

Wani murmushi Rumana ta yi wanda sam bai da alaƙa da nishaɗi, tana yi wa Hajja wani kallo na tausayawa dan kuwa tabbas bata yi dace da nagartaccen tsatson da za ayi  alfahari da shi ba.

Ba tare da ta sake cewa komai ba, ta mike ta faɗa banɗaki dan tsalkake kanta. Sai dai yau ma kamar ko yaushe, sam ita bata ga wata alama da ke nuna wani namiji ya kusanceta ba, amma saboda ba wani ilimi ne da ita a wannan fannin ba yasa ta yi wankan tsarkinta kawai, tunda sam bata iya tuna abunda ya faru da ita lokacin da ta suma. Ko ya samu biyan buƙatarsa kanta ko bai samu ba ita sam bata sani ba............!!!!!

"Ummie wai a haka Rayuwarki zata ci gaba da zama ne dan Allah? me yasa Baba ba zai sauwake maki ba ne  ki huta ba?"

wani kallo maihaifiyar tata ta watsa mata mai dauke da gargadin kar ki sake min irin wannan maganar.

"Allah waddan naka ya lalace, yanzu ke Zulaiha har kin san ki zo kina gayawa mahaifiyarki wannan maganar. Har kin yi girman da kike iya zabarwa mahaifiyarki rabuwar aure da mahaifinki ya rabb Anya kuwa yar nan kina nema ki gama da duniya lafiya kuwa.?" Dada ta faða cikin tsananin ɓacin rai

turo baki Zulaiha ta yi. "Ni kinga Dada ba ruwanki da sha'anin nan tunda ke ko da yaushe goyon bayan Abba kike yi yana muzgunawa yar da kika haifa. Konke kika haifesa ai iyaka annan"

Zuciya Da Hawaye Where stories live. Discover now