Tun lokacin da kunnuwanta suka jiyo mata labari mafi muni a duniyarta bata sake sanin inda kanta yake ba har aka kai Hajja makwancinta bata cikin hayyacinta. Gani take tamkar ba gaskiya ne ba, gani tak tamkar cikin bacci take kuma zata falka ta tashi daga mummunan mafalkin da take yi.
Saida taga an yi wasu yan kwanakki Hajja bata dawo ba sannan ne ta yardarwa kanta cewa Hajja ta tafi, tafiyar da ba za a dawo ba har abada.
Tayi rashin kaka, uwa, uba, ƙawa da kuma malama. Hajja ita ce komanta
Shi yasa a cikin yan kwanakkin nan duk wanda ya santa ba zai ganeta ba saboda yanda ta zabge ta rame, ta yi baƙi sosai saboda damuwa da kaɗaici.Tun bayan ukun Hajja bata sake sanya Baba a idanuwanta ba, Ranar tana zaune ta ji hayaniyar mutane cikin gidan aka ce mata amaryar mahaifinta aka kawo.
Ko ba komai ta ji ɗan sanyi cikin ranta dan ta san ko yaya ne zata ɗan rage mata kaɗaicin da take fama da shi a cikin gidan.
Bayan kwana biyu tana zaune ɗaki ita kaɗai kamar mayya, dan amaryar tashi ita da babu duk ɗaya dan da safiya ta waye take fita gidan kuma bata dawowa sai dare. Shigowa ɗakin Baba ya yi tunda ta gaidashi bata sake ko kallonsa ba taci gaba da jan tasbaharta tana istigifari.
"Ki shirya anjima zan sadaki da gidan mijinki, dan aure an riga an daura shi kamar yanda na gaya miki. Na ƙyale ki ne kawai ban kaiki ba kamar yanda naso tun ranar da aka ɗaura saboda rasuwar nan. Dan haka yau zaki tare Hindu zata kawo maki kaya ki shirya dan ban son ɓacin lokaci." Ya faɗa yana jin haushinta na taso masa dan gani yake yi kamar it ce tayi sanadiyar ya rasa Hajjarsa.
Sai lokacin ne Rumana ta ɗago ta kalleshi da idanuwanta da suka soye da baƙin ciki da damuwa. Amma bata ce komai ba ta koma maida kanta ƙasa tana jin ranta na mata zafi saboda tunawar da ta yi cewa wannan maganar ce sanadin rasa Hajja.
Bata yi mishi gardama ba, bata kuma tada hankalinta ba, saboda zuciyarta ta daɗe da bata mafitar da take ganin ita ce kaɗai hanyar da zata bi ta rabu da bala'in da mahaifinta ke afkata cikinsa.
*************!!!!!!!!!!!!!!!!
"Mommy dan Allah ki daina damuwa da sha'anin Jabeer ni nagaya miki ban damu da ko wane irin matsayi Daddy zai dorasa akai ba. shin ba ni nake kula da assibitinsa ba to miye abun damuwa tunda nima inada abinyi ba zaman banza nake yi ba?"
"Kai banza ne baka san ma inda kanka ke ciwo ba wallahi. Assibitin tsiyar me, duka assibitin ƙwara nawa ce da har zaka yi comparing ɗinta da Amfagsons drugsfield and food industry kamfanin da ba nigeria kaɗai ba kai kanka kasan har ƙasashen kusa da mu ana alfahari da shi dan haka ba zan taɓa lamunta ya shiga hannun ɗan ƙwaya ba wallahi" Hajja Falmata ta faɗa tana huci.
"Wai meke faruwa a gidan nan ne mom? Tun a falo nake jiyo hayaniyarki" cewar Aina da dawowarta kenan daga makaranta.
"Bannin da wannan banzan Yayan naki, ni narasa gane kalar Khamal wani lokaci ji nake kar bani na haifeshi ba dan sam bai san ciwon kansa ba ko kaɗan. Hakkinsa ma sai na sanar da shi yaje ya karɓa dan yana lusari" cewar Falmata tana hararar Khamal.
Tsaki Ainah taja tare da cewa. "Akwai abunda Allah ya gani bai yini namiji ba Mommy, amma wallahi very soon zan baki mamaki dan ina mai tabbatar maki nima ankusa damawa dani a kamfanin nan jira kawai nake na kammala masters ɗin nan dan nafi so duk inda zanje a kalle ni da ƙima." Ta ƙarashe maganarta tana fari da idanuwa.
Murmushin jin daɗi Hajja Falamata ta yi. "Nasani Ainah, nasan kuma ke ɗin ta daban ce shi yasa koda yaushe nake alfahari dake. Bani da haufi kanki Ainah dan nasan kina son duk abunda nake so"
Sosai daɗi ya kama Ainah ta kalle Khamal ta masa gwalo.
"Sai na ɓallaki Ainah idan baki fita hancina ba wallahi, ke me kika sani da zaki kaɗowa mutane ƙaton bakinki ana magana, ki kiyaye ni fah" Khamal ya faɗa yana ji kamar ya kama Ainah da duka.
"Ai nan kaci rani har damana ta iskeka da yan uwanka kaɗai ka iya tada jijiyoyin wuya, ni tashi ma ka bani wuri dan magana dakai ma bacin lokaci ne. Bari Sule yazo idan ni baka yi yanda nake so ba ai shi sai ya sanyaka ka idan yanada ƙima a idunka shima"
Khamal dai bai ce komai ba sai banbamin bala'inta take yi tana aibanta Jabeer Ainah na tayata. Ganin basu da niyar dainawa yasa ya yi masu sallama ya kama hanyar gidansa inda iyalinsa.*****
**********************!!!!!!!!!!!!!Kano
Zaune take kan motarta a bakin department of english. fuskarta sanye da makeken madubi sai taunar cingam take tana dannar wayarta.
"No wander nake ta rabon idanuwa ina nemanki a wurin lectures ashe you are here enjoying your self. Me ya hanaki shiga lectures hala"
Sumayya ta faɗa lokacin da ta ƙaraso kusa da Zulai.Cikin ko in kula Zulai tace. "I don't want. Kin san na tsane malamin wani mummuna dashi"
Dariya Sumayya tayi tare da cewa. "Baki da dama ƙawata. Dan kawai yana mummuna zaki tsanesa you are unbelievable Zully, amma kinsan Allah yau ya ɗauki serious attendance and yace shi ne matsayin first CA."
Taɓe baki Zulai tayi. "Shi ya sani, ni abinda nasani dai ko exam ɗinshi ce ban rubuta ba dole ne nayi passing kin sani kema"
Murmushi Sumayya tayi. "We shall see. Yanzu ina zaki je?" Ta faɗa tana mai ɗale bayan motar itama.
Agogon hannunta Zulai ta duba tare da cewa. "Banzan Jamal ɗin nan ne nake jira yanata damuna yana so ya ganni. Ban san ko uwar me yake so nayi masa ba."
"Kice hand bag ɗinki nafi fahimta. Your one and onl....."
"Pls cut it off Summy. Allah ya tsare ya zama one and only ina dai kulashi ne hakanan saboda yana Babban yaro amma ni kin san kyaunsa bai yi min ba he is not the man of my choice."
"Naso ganin man of your choice ɗin nan da kike faɗa. Kwanan baya guy ɗin da muka haɗu dashi mall ko alama banga makusarsa ba. Amma haka kika yi dumping dinshi wai bai cika irin kalar da kike so ba. Anya ba aljani kike so ba Zully ni fa kin fara ban tsoro" Sumayya ta faɗa tana daƙune fuska.
Murmushi Zully ta yi ta ce "manta kawai Summy bazaki taɓa ganewa ba. Ni inaga kawai mu wuce dan naga alamar banzan nan kamar bayada niyar zuwa yanzu, ni kuma ba zan sake kiransa ba muje kawai inada abun yi a gida Ummih zan raka salon, wai gobe mijinta zai dawo"
Baki Sumayya ta saki tana kallonta kafin ta kwashe da dariya. "Ban taɓa ganin yar iska irinki ba Zully mahaifinki ne fa kike yiwa shaƙiyancin nan"
Dariya suka yi dukansu kafin su shiga motar, Zulai ta bata wuta suka fita cikin makarantar.*******"""""""**""""""
****"""""""""""
*****""""""""""!!!!Kamar yanda Baba ya gaya mata haka ne ta faru da yin magaribar fari yazo, suka tasa ƙeyarta gaba shida matarsa suka sadata gidan da ya shaida mata nan ne gidan mijinta.
Har cikin ɗaki Anty Hindu ta kaita fuskarta lulluɓe da mayafi. Bata san ya gidan yake ba dan tunda ta shiga motar kanta ke ƙasa idanuwanta ba alamar hawaye ko ƙwara ɗaya. Amma ga masu iya gane hawayen zuciya kallo ɗaya zasu yi mata su hango haywayen da ke kwarara a zuciyarta.............*******!!!!!!!!
Kuna ganin da gaske Baba ya aurar da ita ko solo ne yake mata.
Idan har ya aurar da ita wa kuke ganin ya aurawa? Me yasa ya aura masa ita? Ku dai biyo ni kawai dan jin yanda zata kasance.
Vote comments and share.
#ZDH#
#Ayshart Farouq#
#NWA#
YOU ARE READING
Zuciya Da Hawaye
RomanceWani irin zufa mai yawa yake sharcewa a ko wace kusurwa ta jikinsa. Tun tana 'yar ƙanƙanuwar ta yake ɗauke da buri a kanta, yake so ya biya buƙatarsa gareta dan cimma wata manufa ta shi guda ɗaya da yake rayuwa domin ta a doron ƙasar nan. Amma ko da...