Babi na sha takwas

71 11 1
                                    

Wata irin dariyar jin daɗi Hajiya Rukayya ke yi tana kallon Uncle Sulaiman da ya yi arsheshe arsheshe kan kujera yana kurɓar lemu.

"Ban taɓa yarda da kwanyarka na ja ba sai yau Sule."

Murmushi ya saki yana jin daɗin yabonsa da yayar tasa ke yi. Ya daɗe bi ji kalmar jinjina ta fito a bakinta garesa ba sai yau.

Shigowar su Khamal ce ta katse masu magana.

Da gudu Arif ya isa kan cinyar kakansa ya ɗale. Yayin da Nazifa ke gaida Hajj Falmata. Sarakuwarta kuma gwaggonta kasancewarta ɗiya ƙwara ɗaya ga uncle Sulaiman.

"Kin ga ni shaf na manta da zancen zuwan nan naku, saboda ɗan iskan yaron can da ke chaja min kwanya har da ciwon mantuwa yake sanya ni" cewar Hajja Falmata kanta tsaye saboda duk wanda ke ɗakin ya san ƙiyayar da ke tsakaninta Jabeer.

Taɓe baki Nazifa ta yi dan ko ba a faɗa ba tasan da wanda ta ke, dan tasan duk duniya Hajja Falmata ba ta da wani maƙiyi da ya wuce Jabeer, tasan da hakan tun tana ƙankanuwarta.

"Ki riƙa jama mijinki kunne Nazifa  dan shi har yanzu sam bai san abunda yake yi ba. Ana nema a nema masa incinsa, da soyayyar mahaifinsa yana ganin kamar ba daidai ake yi ba"

Wani kallo Uncle Sulaiman ya yi wa Khamal da su kaɗai suka san ma'anarsa.

Murmushin yaƙe Khamal ya yi. "Mommy kenan a riƙa dai bin komai a hankali. Jabeer bai tare min komai ba har yaushe ma yake da nutsuwar da zai yi abunda kike tunani."

"Bar ganin sa kamar bai san abunda yake yi ba Khamal. Billahil azim nasan shegen yaro ne. Nasan sa kamar yunwar cikina kar yake kallon mutane. Ban da ma damuwar da ya sanyawa rayuwarsa ai da tuni ya kaini kwance, ko kuma cikin kushewata. Shi yasa nake neman abunda zai ƙara nakasa masa zuciya ya mutu can in huta da baƙin cikinasa." Ta faɗa wani zafi na taso mata sosai a ƙasan zuciya.

Sosai Khamal ya ji haushin kalamnta ga ɗan uwansa shiyasa ya tsura mata idanuwa yana kallonta ko zai ga wani abu da ya chanja a halittarta.

"Ka daina yi min irin wannan kallon dan uwarka. Duk abunda nake ai danku nake yinsa shashashan banza, ni ka zo ma ka wuce ka bani wuri kar in sauke ma haushin da nake ji yanzun nan" Ta faɗa tana mai galla masa harara kamar idanuwanta za su fito.

"Allah ya huce zuciyarki Mommy.  Nazifa zo ki karɓi saƙo ni zan wuce assibiti idan kuma kika ƙare kisa Aina ta maidaki gida ko driver, dan inaga ba zan dawo da wuri ba akwai ayukka da yawa a gabana." Khamal ɗin ya faɗa yana  miƙewa, Nazifar ma miƙewa ta yi ta mara masa baya.

"Ni wallahi sau da yawa wani lokaci sai inga kamar chanja min Khamal aka yi a assibiti" Hajja Falmta ta sake faɗa cikin ɓacin rai.

"Daina faɗar haka Anty, lokaci ya kusa da Khamal zai baki mamaki ina da yaƙinin haka insha Allahu". Cewar Uncle Sulaiman da ke murmushin da shi kaɗai ya san ko na miye.

"Haka dai kake cewa ko yaushe Sule. Amma ba zan ce komai ba sai dai in yi addu'ar Allah ya nuna min ranar dan ni al'amurran Khamal suna tsorotar dani wani lokaci."

"Uhm." Kawai  Uncle Sulaima ya ce, dan baya son ya furta wata magana da zata iya zame masa ɗan zane......

"Mommy dan Allah ki sanya ya chanja min mota. Wallahi nagaji da hawan motar can duk ta tsufa  yanzu haka ma fah tana wurin gyara." Cewar Nazifa da ta dawo wurin raka mijin nata.

Zuciya Da Hawaye Where stories live. Discover now