Babi na takwas

90 6 0
                                    


Kano

"Kwananki nawa baki je kika duba Baba Malam ba Zulaiha?"

Ɗan turo baki tayi.

"Ni Allah Ummi tsohon nan tsoro yake bani sai in riƙa ganin yana min wani kallo tamkar wata halitta abin tsoro a garesa. Ni ban san me ya hanasa mutuwa ba. Lokacinsa ya fa yi da kun daina wahalar da kanku a k......."

Bugun bakinta da taji anyi ne da ƙarfi yasa ta katse maganarta tana sosawa.

"Baki da hankali ko Zulaiha. Baki da hankali wallahi sai yau na tabbatar da haka" Ummi ta faɗa cikin tsananin ɓacin rai.

"Ki yi haƙuri Ummi ban faɗa dan ranki ya ɓaci ba. Amma kema kin san halin da Baba malam yake ciki zamarwa mutane liability ne kawai. Abba yayita kashe kuɗaɗensa a banza ga ciwon da bana tunanin yanada magani." Ta faɗa kanta tsaye ba tare da ta damu da kallon da mahaifiyarta ke jifanta da shi ba.

"Tashi ki bani wuri marasa kunyar banza da wofi. Zan yi maganinki kwanan nan idan baki shiga hankalinki ba."

"Tuba nake Mamana amma dai Baba Malam kam tashi ta ƙare lokaci kawai muke jira" ta faɗa tare da ƙyalƙyacewa da dariya.

"Allah ya shiryeki toh Zulaiha. Kakanki dai ne da ya haife ubanki kuma ba zaki iya hana mahaifinki ya kula da shi ba"

"Toh ai sai ya yi ta wahalar da kansa tunda shi ya ji ya gani. Ni dai gaskiya am out of this, a daina takurani da maganar tsohon nan"

"Anya zaki iya jinƙanmu lokacin da muke kamar Baba Malam kuwa Zulaiha, ni fa kin fara bani tsoro fah." Ummi ta faɗa tana mai kafe Zulai da ido.

"Ummi a bar maganar kawai. Insha Allahu ma ba zaku zama irin Baba malam ba. Ke kika gaya min fah tun ina jaririya yake haka ba baki ba ƙafafu gashinan dai kamar gunki ido ne kawai dashi na kallon mutane" Ta faɗa tare da miƙewa.

"Bari dai toh na tafi na duba shi dan ba halinsa ba. May be this is the last time da zan tafi"

"Toh ja'ira ai sai ki jira muje tare. Ga ma maganinsa  nan da aka siyo nasan wancan ya ƙare" Ta faɗa tare da janyo mayafinta...!!!!!!!

****"""""""***†****""""*********

Tun aika aikar da Rumana ta aikata bata sake samun nutsuwa a zuciyarta ba, koda yaushe idan ta kwanta sai ta riƙa ganin mugun mutumin da ta bari kwance cikin jini yana yi mata gizo a idanuwanta. Kuma tun lokacin bata sake jin ɗuriyar Mahaifinta ba.


Kammala cin abincinta kenan, ta fito waje dan ta ajiye plate taga shigowar mutum tamkar guguwa.

Saukar wani gigitaccen marin da ya sauka a kuncenta na dama ne ya tabbatar mata da ko waye ya mareta. 
Sosai ta fita hayyacinta na kimanin yan ɗiƙiƙu ƙalilan.

"Mutuniyar banza mutuniyar yofi, yaushe kika zamo yar ta'adda? Rumana kisan kai kika so ki aikata ko meye?  Wallahi yau sai kin tabbatar da  kin bijirewa umurnina Rumana."

Ya faɗa yana mai kai hannayensa a wuyanta ya yi mata wata irin  kyakkyawar shaƙar da ta kusa ta sake zautar da tunaninta.

Wani irin abu ta riƙa yi tamkar ana cire ranta, sosai nunfashin da take shaƙa ya ƙaramta a gareta. Sassauci take buƙata ko yaya ne daga garesa, bakinta rawa yake haɗe da kakkarwa, sosai take neman kalaman da za ta fizgo a halshenta dan su taimake ta daga mummunan hukuncin da yake so ya aikata a gareta.

Zuciya Da Hawaye Where stories live. Discover now