Wani irin Gudu ne take yi a cikin dokar daji kamar zata tashi sama. Wata irin mayunwaciyar ƙatuwar ɓakar halitta ce ke biyarta tana so ta halakata. Sosai take gudu dan ta tseratar da rayuwarta gareta. Bata yi aune ba taga wata Baƙar halitta mai dauke da jajayen idanuwa da wasu zara zaran ƙahoni a kanta ta gitto a gabanta.
Juyawa ta yi a bayanta taga waccan halittar ta kusa zuwa gareta ga wannan na yunƙurin ta saka mata zara zaran akaifun hannunta a fuskarta. Bata san ta inda ya fito ba kuma bata ga fuskarsa ba saboda tsawon gashin da me kansa da ya rufe fuskarsa ruf. Hannunta kawai taga ya kama yayin da wani iska mai sanyi ya kaɗa ya yi sama dasu. Tana ganin yanda halittun nan ke ƙanƙancewa ganinta har ta kusa ta daina ganinsu ta falka.
"Ya Allah!" Ta faɗa da ƙarar gaske tana mai buɗe idanuwanta duka biyu.
"Rumana!" Hajja ta faɗa tana mai shafa mata ruwan da ta yi wa karatu a fuskarta.
"Hajja na sake yin mafalkin nan da nagaya maki ranar" ta faɗa cikin tsananin tashin hankali.
"Ba abunda zai same ki Rumana. Ki yi addu'a Hajja ta faɗa ita ma kanta na mata wani irin sarawa.
"Ina take wannan yarinyar?" Suka jiyo muryar Baba ta doso ɗakin.
Miƙewa zaune ta yi daƙyar tana shafe fuskarta da hijab din da ke jikinta.
Wani kallo Baba ya jefeta da shi da ya birkita yan hanjinta.
"Ki shirya yanzu yanzu za'a kai ki gidan mijinki, na ɗaura maki aure yanzun nan.
Wata irin miƙewa Ruman ta yi, tana mai jin wani abu na rufe mata ilahirin zuciya.
"Aure kuma Baba?" Ta faɗa da wata irin murya mai kauri da bata yi kama da tata ba.
Ita kanta Hajja tambayar da take yi masa kenan.
Kallon Hajja ya yi yana ɗan nazarinta saboda ganin kallon da take yi masa da idanun da bai saba gani ba.
Cikin dakakkar muryars ya furta."Eh aure na ɗaura mata yanzun nan saboda na isa da ita." Ya faɗa fuskarsa dauke da alfahari mai girma.
"Allah zai saka mata Iro. Allah zai tambayeka hakkin rumana. Kana ganin kamar tunda kai ka haifeta Allah ba zai kamaka da laifin musguna mata ba ko? To wallahi ka sani Allah zai saka mata saboda itama tanada hakki a kanka kamar yanda kake iƙirarin kanada haƙƙi a kanta". Ta faɗa tare da goge hawayen idanuwanta tana mai jin wani sanyi na shiga ƙafafuwanta yana ratsawa har zuwa kwanyar kanta.
Bata san ya aka yi ba. Bata san me ya shiga kanta ba, bata san zata iya faɗawa ɗanta magana irin haka ba. Ita dai ji kawai ta yi tana gaya masa magangannun da ko a mafalki bata taɓa yunkurin kallon idanuwansa ta gaya masa ba. Amma yau bata san me ya hau kanta take faɗin maganar da ke yawo a kanta ko da yaushe ba.
Duk kuwa da irin tsoron da ya mamaye dukkanin ilahirin zuciyar Hajjan bai sa ta fasa cigaba da maganarta ba. jikinta sai wani irin kaɗawa yake yi da har ya so ya tsoratar da mutane biyun da ke zagaye da ita."Ina ji a jikina cewa, watarana sai ka yi kuka da idanuwanka, a kan Rumana. Sai ka yi kuka Iro kan wannan ɗiyar taka ƙwara ɗaya dake gabanka. Ina kuma roƙon Allah da ya wargaza duk wani abu da ka sanya a gabanka da ba alkhairi ba. Allah ya wargaza shi Iro ko mene ne" Wannan karon jikinta kasa ɗaukarta ya yi, yayin da kalamanta suka fara yankewa suna fitowa da guda guda.
YOU ARE READING
Zuciya Da Hawaye
RomantizmWani irin zufa mai yawa yake sharcewa a ko wace kusurwa ta jikinsa. Tun tana 'yar ƙanƙanuwar ta yake ɗauke da buri a kanta, yake so ya biya buƙatarsa gareta dan cimma wata manufa ta shi guda ɗaya da yake rayuwa domin ta a doron ƙasar nan. Amma ko da...