Babi na uku

120 9 0
                                    

Kano

"Yanzu dan Allah Saada rayuwar da kuka daukarwa kanku kuna ganin dai dai ce? A gaban yaranku Saada a gaban kowa zaku iya yin fada kamar karnuka. Kai ba ķaramin mutum ba, da darajarka da komai naka kake biyewa mace kuna sa'insa.  Me yasa ba zaka iya  sauwake mata ba idan ba zaku iya zaunawa lafiya ba?"

A tsorace Abba ya kalle Dada a karo na farko tun zamansa cikin falon saboda yau ne karo na farko da ya ji ta furta cewa ya kamata ya sauwakewsla Haleemar. Tabbas yasan sun  kaita matukar kul tunda har a matsayinta na uwa mai kaunar yaranta ta iya furta ya sakar mata 'yarta hakanan.

Cikin sanyi murya ya furta a dai qara hakuri Dada dan Allah. haka ba za ta sake faruwa ba insha Allahu" Ya faða a cikin girmamawar.

"A'a Saada zaku sake ba yau kuka saba fura hakan ba"

"Ba zamu sake ba Dada insha Allahu." Cewar Ummi ita ma a karo na farko na zamanta wurin.

"Hmm Allah dai ya kyauta kawai, ai sai ki tashi ki ðauko mayafinki ku tafi, tunda haka kuka zabarwa kanku tsofai tsofai daku kullum cikin yi maku sulhu ake wannan jaraba da me tayi kama?."  Dada ta fada tana mai mikewa ta yi shegewarta ðaki ta barsu dan har ga Allah abun nasunya wuce duk inda take tunaninsa.

"Ina jiranki a waje." Ya fada tare da miƙewa.

bada daɗewa ba ta fito. ta samesa a mota. Fara tafiyarsu keda wuya.  Ya kalleta ransa ɓace ya ce.

"Wai ni Zulaiha zata kalla ido da ido taķi yiwa magna. Wallahi duk abunda yarinyar nan take yi laifink ki ne, ke kika ɗaure mata gindi a duk abunda take aikatawa."

"Zaka fara ko? Wai ka fisabilillahi me yasa ba zaka bari a zauna lafiya ba. Ni ban san me Zulaiha ta tare maka ba da kabi ka tsaneta kamar ba kai ka haifeta ba."

"Haka ma zaki ce ko, yanzu kina nufin abunda ta yi, ba ta yi laifi ba ko meye kike so ki ce?." Ya faɗa yana kafeta da manyan idanuwansa.

"Ba haka nake nufi ba fa. Ya  kamata dai ai  ka riƙa sassauta mata har yanzu ita yarinya ce lallaɓata ya kamata ka yi har ta gane cewa ba tsanarta kake yi ba. Dan Allah ka riƙa sanyawa zuciyarka salama mana. Kuma sauran yaranka ai ba haka kake yi masu ba." Ta fada cikin marairaicewa.

"Hmm toh shikenan  i will make it up to her, Happy?"
Ya faɗa cikin murmushi.

Ita ma murmushin ta yi har jerarrun fararen hakoranta suka bayyana.!!!!!!!!.......*************

***********

"Dan Allah Hamma Saifu ka yi haƙuri ka tafiyarka dan wallahi yau ko ficika ba zaka samu a wurina ba".

"Haba Rumana. Ni ɗin ne yau ba zaki taimakawa ba?"

"Taimakon me zan yi maka Ya Saif, bancin ina da tabbacin  ba yunwa kake ji ba ballantana ka ce abinci zaka ci."

"Ke gane zazzaɓi nake ɗan ji magani  nake so na saya." Ya fad'a kamar da gaske.

"Hmm da dai ban sanka ba Ya Saif, Amma Wallahi ba abunda ke damunka, so dai kake yi kawai na baka ka je can ka sha abunda ka saba sha, toh gaskiya ba zan bayar ba dan yau ba zan iya iya ɗaukar tujara Mama kan kuɗinta ba"

Sosa ƙeyarsa ya yi tare da ɗaure fuskarsa yana yi mata yar barazana duk da yasan ba tsoratata zai yi ba. Saboda sosai ya san kafiya irin ta ƙanwar tasa, muddun ta kafe a kan abu to fa ba zata tanƙwasu cikin lumana ba, shi yasa lokutta da yawa take shan wahala.

Zuciya Da Hawaye Where stories live. Discover now