Tana nan zaune inda aka ajiyeta ko motsawa bata yi ba saboda zuciyarta rufe take ruf. Ƙofar ɗakin ta ji an buɗe an shigo.
Sai dai ganin yanda aka jima da shigowa kuma ba ayi magana ba ya sa ta tabbatar da ko waye ya shigo ɗakin ƙare mata kallo yake yi saboda sosai take jin idanuwansa a kanta.
Ita har cikin zuciyarta ba ta yarda cewa aurar da ita Baba yayi ba. Tafi yardarwa kanta cewa caca aka ciwota kamar yanda aka saba idan an cinye shi ita kuma sai a tafi da ita. Gani take kamar wata hanya ce ya ɓullo mata dan karta sake aikata aika-aikar da ta aikatawa Sule Kunama.
Wani abu ta ji ya soki ƙahon zuciyarta lokacin da ta tuna rabuwarta da mugun mutumen can Sule kunama wanda har yanzu bata san ko yana raye ko a mace ba.
Suɓulewar hannun rigarta ne yasa ta
fahimce abunda ya ke kallo a jikinta, saboda kayan jikinta kaɗai abun kallo ne a matsayinta na wadda aka kawo ɗaki yau.Idan dai har aurar da ita ɗin Baba yayi da gaske toh tabbas tasan sai dai ya aurar da ita ga irinsu Suzuki ko waɗanda sukafi su nakasar zuciya. Idan kuma har ba a irinsu Suzuki ba, to lallai duk wanda aka ɗaurawa aure da ita an cutar da shi mafi munin cutarwa.
Wata zuciya kuma ta raya mata cewa wata ƙil sadakarta ya bada a masallaci kamar yanda mama ke shawartarsa yayi a wasu lokutta. Tanada yaƙinin cewa muddun ba chacha aka ciyota ba, to tabbas sadakaarta aka bada matsayinta na macen da babu wani mahaluƙi da ya taɓa furtawa a kalmar so. Ko Suzuki tasan Saif ne ya kaimasa tallarta, shi kuma yake kwaɗayin jikinta kamar yanda sauran mutane ke yi. Amma tabbas tasan ba sonta yake yi ba. Wani irin rauni ta ji ya ziyarce ruhinta yayin da take jin kaifin kallon halittar nan da ta shigo ta kasa ƙarasowa a gareta. Ji tayi tana so ta gansa, so take taga ko waye shi, sosai take so ta yi arba da fuskarsa koda hasashenta na biyu zai zamo gaskiya a gareta. Sai dai bata san me yasa ta kasa ɗago idanuwanta ta kallesa ba. Tasan Idanuwanta baza su taɓa bata haɗin kai ta kallesa ba a halin yanzu saboda basa son kallonsa dan kar su hango abinda suke gani a fuskokin dake yi mata gizo a zuciyarta.
Bankar ƙofar da aka yi aka sake fita ne yasa tayi saurin ɗago da idanuwan nata a karo na farko tabi ƙofar ɗaakin da kallo ba tare da ta hange ko ƙurar wanda ya shigo ya fitan ba.
"Ya rabb!"
Ta faɗa da wata irin gajiyayyar murya mai rauni.A hankali kuma sai ta ji leɓunanta sun saki wani malalacin murmushin da sam bai da alaƙa da nishaɗi.
A hankali ta miƙe tsaye lokacin da ta ji kamar an fita da mota a cikin gidan.
Wurin Dressing mirror dake manne da bangon ɗakin ta isa ta tsaya tana karema kanta kallo tare da neman munin dake fuskarta.
Dubanta takai ga kayan dake jikinta. Ba laifi kayan nada ƴar damarsu tunda sababbi ne sai dai bata san a inda aka same su ba, amma kuma ga dukkan alamu na Anty Hindu ne da ta ɗunka ba ta sanya ba, saboda yanda wuyan rigar ya yi mata yawa sosai sai kame-kame take yi dan kar ta faɗi.A hankali ta sake kallon fuskarta tare da nuna kanta da yatsa tace.
"Ke mummuna ce, dan ba ki da farin jinin da mutane zasu so ki, sadaka zan yi dake Rumana dan nagaji da ganinki a gidan nan har yanzu"
Ta faɗa a fili kalaman Mamar na sake dawo mata akai kamar yanzu take furtasu gareta.
"Wan can mutumin da ya fita idan dai har ba suzuki ba ne to tabbas shi ne aka baiwa sadakar ki. Idan kuma ba haka ba, to tabbas babanki ya fanshe kansa dake ne a wurin caca." Ta sake faɗa ba tare da ta damu da cewa babu wata halitta a kusa da ita da zata ji ta ba.
YOU ARE READING
Zuciya Da Hawaye
RomanceWani irin zufa mai yawa yake sharcewa a ko wace kusurwa ta jikinsa. Tun tana 'yar ƙanƙanuwar ta yake ɗauke da buri a kanta, yake so ya biya buƙatarsa gareta dan cimma wata manufa ta shi guda ɗaya da yake rayuwa domin ta a doron ƙasar nan. Amma ko da...