Washe gari da misalin ƙarfe goma sha ɗaya na safe, Jabeer zaune kan kujera. Ya ɗora ƙafafuwansa duka biyu kan center table ɗin da ke tsakiyar falon sai zuƙar taba yake yi tamkar danta kawai aka haliccesa duniya.Yana ji ana bugun gida amma ko gizau bai yi ba ballantana ya tashi ya je ya buɗe kofar sai ma ƙara gudun hayaƙin da yake fitarwa ta baki da hanci da ya yi.
Saida ya tabbatar da ko su waye a jikin ƙofarsa rayukkansu sun riga da sun gama ɓaci sannan ne ya tashi ya tafi ya buɗe ƙofar.
Yana buɗewa kuma bai ko tsaya ya bi takansu ba dan ya riga yasan ko su waye, dan tun kafin zuwansu mahaifinsa ya turo masa saƙo ya sanar da shi zuwan nasu. Ba damuwa ya yi da zuwansu ko rashin zuwan nasu ba, shi yasa ma yana buɗe masu ƙofar ya koma mazauninsa ya ci gaba da zuƙar hayaƙinsa.
Kasa shiga gidan Hajja Falmata da Aina'u suka yi saboda yanda zuciyarsu ke tsananin tafarfasa ganin wulaƙancin da Jabeer ke son ya shuka masu.
"Mommy kinga wani sabon iskancin da ya ƙaro?" Cewar Aina tana riƙe baki.
Taɓe baki Hajja Falmata ta yi tare da cewa. "Ki barni da shi nice nan zan sauke masa duk wani abu da yake taƙama da shi. Nice nan zan ida kassara rayuwarsa idan bai daina shiga gonata ba." Ta faɗa tana sakin huci mai zafi
"Ni ban ma san ko waɗanne gantalallun mutane ne suka basa yarsu ba"
Kwafa Hajja Falmata ta yi tare da cewa "Wlh idan ɗiyar manyan mutane ce aka aura masa bada sanina ba sai na san yanda nayi da auren, da ni Abdulfatah Goni ke magana." ta faɗa tare da jan akwatin dake gefenta ta shiga cikin gidan.
Sai da suka zazzauna suna biyar fallon da kallo kafin Hajja Falmata ta yi magana.
"Ina Amaryar ko kuma bamu da arziƙin ganinta ne mu koma inda muka fito?" Ta faɗa tana kallonsa.
Bai ko kalle inda take ba ballantana ta sa ran zai amsa mata maganarta saboda ji yake kamar ya shaƙo wuyanta ya kaita lafira. Baya ƙaunar matar ko kaɗan duk ya randa ya ganta sai ya tuna da babbar gudummuwarta a rayuwarsa.
"Jabeer da kai nake magana ka yi kunnen uwar shegu da ni." Ta faɗa a hasale.
Still bai yi magana ba sai sake kishingiɗa da ya yi, ya lumshe idanuwansa yana tuna wani abu da sam baya so yana gitta tunaninsa.
Cikin kunne Aina'u ta raɗa mata. "A buge yake Mommy ko ba ki ga idanuwansa ba ne?"
Ya ji ta sarai sai dai bai da lokacin kula su a halin da yake ciki. Dan idan ya ce zai bi takansu yasan ba ƙaramar ɓarna zai tabka ba.
Motsin da suka ji bayansu ne yasa suka waiga.
Tsaye take tana rarraba idanuwa fitowar ta kenan saboda motsin mutanen da ta ji.
Kallo ɗaya zaka yiwa su Hajja Falmata ka ga tsantsar mamakin da ke shinfiɗe saman fuskokinsu.
Wata irin dariya ce ta ƙwacewa Mommy kafin ta nuna Rumana da yatsa. "Kar dai ke ce Amaryar Jabeer?" Ta faɗa fuskarta na nuna tsantsar ƙyama a gareta.
Kallon da ta yi wa Rumanan, ko alama
bai dame ta ba, saboda idan da sabo yaci a ce ta saba da kallon da mutane ke yi mata.
YOU ARE READING
Zuciya Da Hawaye
RomanceWani irin zufa mai yawa yake sharcewa a ko wace kusurwa ta jikinsa. Tun tana 'yar ƙanƙanuwar ta yake ɗauke da buri a kanta, yake so ya biya buƙatarsa gareta dan cimma wata manufa ta shi guda ɗaya da yake rayuwa domin ta a doron ƙasar nan. Amma ko da...