Yanzu ba kasafai take ganin Jabeer a gidan ba sai dai takan jiyo motsinsa a wani lokacin kasancewar yanzu ba abunda ke haɗata da shi.Dan dai da ma can abinci ne kawai ke haɗata da sahi , yanzu kuma Alhamdulillah ba ta da matasala da takeaway ɗin shi, dan store ɗin gidan cike yake da kayan abinci duk abinda take buƙata akwai, har nau'in kayan miya da nama duk an sanya mata a deep freezer.
Kusan kuma ko da yaushe idan zata dafa abinci tare da shi take dafawa, sai dai, bai taɓa nuna alamar ya gani ba ballantana har ya yi sha'awar ci. Yanda ta ajiye haka take kwashe kayanta.
Zata iya cewa tun lokacin da mahaifinsa ya zo ya gaya mata kaɗan daga cikin matsalolinsa take yawan mafalki da shi. Sai dai yau mafalkin da ta yi ba ƙaramin tsaya mata a rai ya yi ba, shi yasa take son jajircewa ta cire tsoronsa ko ta ya ya ne, ko hakan zai sa ta samu ta fahimci da wane irin mutum ta ke zama kafin ta fara ɗaurasa kan hanyar da ta yi wa kanta alƙawarin ɗorasa a kai idan ta samu dama.
Babbar matsalarta shi ne, bai taɓa shiga lamurranta ba, hasali ma ko magana ba ta sake shiga tsakaninta da shi ba tun wancan lokacin.
Sau da yawa idan suka haɗu ko kallonta ba ya yi. Ita kuwa tsoronsa ke hana ta yi masa magana, da ta gansa take guduwa ɗakinta har sai ta daina jin motsinsa sannan za ta fito.
Yau kasancewar ranar assabar tun da ta tashi da safe ta ke jin motsinsa cikin gidan, amma da yake ta riga ta ƙudurtawa ranta cewa za ta fara gwada sa'arta kansa yasa ta cirewa ranta tsoro, ta fito ta wuce sa a falo yana kallon ball a tv, ta shiga kitchen ta soma aikin abincinta.
Ko da ta kammala ba ya falon amma ga dukkan alamu ba nesa ya je ba saboda wayoyinsa da agogon hannunsa duka suna kan center table. Hakan ne ya ba ta damar shigowa da abincin ta ajiye tare da fara shirya wormers ɗin a inda ya tashi, cikin ranta kuwa addu'a kawai take yi kan Allah ya ɗora ta kansa kar ya gwatsaleta.
Tana cikin jera abincin ne ya shigo. Sosai ta ji gabanta ya faɗi amma sai ta danne tare da furta. "Sannu da zuwa Hamma" cikin siririyar muryarta.
Ba tare da ya amsata ba ya zauna a inda ya tashi tare da ɗaukar remote yana chanja channel.
"Hamma ga abincinka nan, a yanzu za ka ci na yi saving ɗinka ko sai anjima idan an yi sallah." Ta faɗa ba tare da ta san me take haifarwa a zuciyarsa ba.
Wannan karon ma bai ce mata komai ba ya ci gaba da kallonsa.
"Hamma dan Allah ka da ka ce baza ka ci abincin nan ba yau, Hamma ba ka taɓa cin girkina ba, dan Allah ka ci ko sau ɗaya ne idan har ka ci ka ji bai yi maka ba zan daina girkawa da kai insha Allahu" Ta faɗa cikin rawar murya, ganin yanda fuskarsa ke ƙara haɗewa kamar hadari.
"Get the hell out of here before i slap you." Ya faɗa cikin tsawar da ta so ta ruguza ɗan ƙarfin guiwar da take tunanin ta fara samu.
Amma da yake an riga da an yi ma ta shaidar taurin kai shi yasa sam ba ta karaya ba sai ma girgiza kanta da ta soma yi idanuwanta tab da hawaye ta ce. "May be this is how you treated her shi yasa ta tafi ta barka."
Wani irin kallon mamaki ya jefeta da shi, idanuwansa na ƙara ƙanƙancewa.
Ba tare da damuwar komai ba ta cigab da cewa. "Idan dai har ba haka kake yi wa Nabeelar ba, me yasa ta kasa cigab......"
YOU ARE READING
Zuciya Da Hawaye
RomanceWani irin zufa mai yawa yake sharcewa a ko wace kusurwa ta jikinsa. Tun tana 'yar ƙanƙanuwar ta yake ɗauke da buri a kanta, yake so ya biya buƙatarsa gareta dan cimma wata manufa ta shi guda ɗaya da yake rayuwa domin ta a doron ƙasar nan. Amma ko da...