'Me ya sa zaki kashe kanki Rumana? Me yasa ba zaki ci gaba da jurewa ba? Shin ko kina ganin zaki sami sassauci a gurin Allah idan kika aikata wannan ɗanyen aikin? Shin baki san azabar Allah ta lunka wahalar da kike sha sau dubu miliyan ba? Shin ko kina tunanin Allah ba zai hukunta ki ba ne idan kika ɗauki rayuwar da ya baki aro ba?
Kalaman da nagartatar zuciyarta suka riƙa gaya mata kenan, wanɗanda nan take suka yi tasiri sosai a gangar jikinta. Abu ɗaya ya rage mata shine amincewar ƙwaƙwalwarta, wadda kuma ko ba'a faɗa ba ta tabbatar da ta aminta, duba da yanda take bin umurninta tana mai sauke ƙafarta ɗaya da ta ɗora kan ƙarfen tare da sadata kusa da 'yar uwar halittar ta.
A hankali ta riƙa janye jikinta a wurin har sai da ta sada kanta cikin madaidacin falon gidan.
Zubewa ta yi kan tiles tana mai sakin wani iri marayan kuka. Kukan da ya fito direct daga zuciyarta.
Kuka take yi da dukkanin iyawarta. Kuka take yi tana jin tamkar tafi kowa matsala a duniyarta.
Zafi take ji wanda bata taɓa jin irinsa ba a rayuwarta.
Nauyin da zuciyarta ke yi mata wannan karon nuyi ne wanda bata saba yi mata irinsa ba a tarihin wanzuwar matsalolinta. Ciwon da take ji a rayuwarta ciwo ne da take ji kamar ba zai taɓa gushewa ba har sai lokacin da ruhinta zai bar gangar jikinta.
A hankali ta riƙa jin wani iska na kaɗawa mai sanyin da ba irin wancan da sheɗan ya riƙa kaɗa mata ba, wannan iska ne mai sanyi tare da sanya natsuwa a zuciya da gangar jiki.
Nan take taji wani yaji yajin barci a idanuwanta, cikin ƙanƙanen lokaci idanuwanta suka rufe ruf, wani irin bacci mai daɗi ya kwashe ta ba tare da ta gayyacesa ba.
Bata san safiya ta waye ba sai da sanyin asuba da na AC suka fara illatar da awazzunta, duba da yanayin gurin da ta yi kwanciyar akai.
Miƙewa ta yi ta wanzar da kanta a cikin ɗakin da take tunanin nan ne muhallinta.
Banɗakin dake cikin ɗakin ta shiga ta yi alwalla. Bata san ina ne gabas ba, ta dai karkata gabanta a inda ya kwanta mata a rai kuma take tunanin nan ne alƙibla ta gabatar da ibadarta.
Lokacin da ta kammala sallar sai ta jingina bayanta da jikin gado. Kanta ta sanya cikin cinyoyinta tana tunanin rayuwarta da duhun dake lulluɓe a cikinta. Tabbas dun dake rayuwarta duhu ne da ke gigitar da tunaninta, haka kuma duhu ne da ke tsoratar da duniyarta. To ko sai yaushe duhun zai yaye haske ya bayyana a gare ta? Allah ne kaɗai masani, kamar yanda shi kaɗai ne ya san abinda take ji a halin yanzu da take zaune tana neman gafararsa da ƴan yatsun hannunta.
Ba zata iya cewa ga abinda take ji ba a halin yanzu. Amma tabbas ciwon da take ji da nauyin da zuciyarta ke yi mata sun ragu sosai a cikin ruhinta. Tabbas kuka rahama ne kamar yanda ta ayyana a zuciyarta. Dan tun ranar da Hajja ta rasu bata sake tarfa hawaye ba sai yanzu.
Haka Rumana ta yini zaune, tun tana tsammanin ta ji wani motsi na wata halitta mai rayuwa a gidan har ta gaji ta haƙura ta zubawa sarautar Allah ido.
Haka ta yini gidan ta kuma sake kwana ba tare da ta ji motsin kowa a cikin gidan ba. Lamarin da ya sake jefa rayuwatrta cikin tashin hankali, da wani irrin zullumi mai girma a ruɗaɗiyar duniyarta.
YOU ARE READING
Zuciya Da Hawaye
RomanceWani irin zufa mai yawa yake sharcewa a ko wace kusurwa ta jikinsa. Tun tana 'yar ƙanƙanuwar ta yake ɗauke da buri a kanta, yake so ya biya buƙatarsa gareta dan cimma wata manufa ta shi guda ɗaya da yake rayuwa domin ta a doron ƙasar nan. Amma ko da...