Babi na sha bakwai

78 7 0
                                    

Waiwaye.

Lokacin da Dr Abdulfatah Goni ya kai Rumana shagon abincinsu daren ranar ma sai da ya yi mafalki game da ita. Haka yasa bai tsaya wata wata ba ya fara bincike kanta. Cikin ikon Allah ya gane mahaifinta.

Amma lokacin da ya gane asalin waye mahaifinta da kuma halayensa ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba. Sai dai tuna cewa shima nasa ɗan yana da nasa aibun da ba kowa zai so ya haɗa zuri'a da shi ba yasa ya kauda tunanin komai ya barwa Allah, dan bai san ɓoyayyen lamari da ubangiji ya barwa kansa sani  game da ƙaddarar ɗansa da Rumana ba.

Hakan ne yasa Dr Abdulfatah bai ɓata lokaci ba ya tunkare Baba da zancen yana so ya baiwa ɗansa auren yarsa. Baba bai ma sauraresa ba lokacin, ya nuna sam shi ba yanzu zai yi wa Rumana aure ba. Ba yanda Dr bai yi ba, amma Baba ya ƙi saurarensa. Daga ƙarshe ma tafiyarsa ya yi ya barsa tsaye cikin tashin hankali.

Gida ya koma cikin tsananin damuwa, ya kira ƙanensa Alhaji Mahmud Goni ya shaida masa duk yanda ake ciki. Saboda Alhaji Mahmud ɗin yasan komai game da mafalkayyan da yake yi da Rumana. Ganin haka yasa Alhaji Mahmud ya ce  ya bar komia hannunsa zai zo Lagos da kansa. a cewar sa zai zo ne ya samu mahaifin Rumana ya yi masa bayani ko zai taimaka masu. Idan kuma ya cije ya ce a'a sai su barsa da yarsa, su ga yanda Allah zai yi nasa iko.

Lokacin da Alh Mahmud ɗin ya je ya samu Baba, bai nuna masa ya san wani ya zo nemanta ba kawai ce masa ya yi yana neman iri ne a gidansa. Ga mamakinsa kuma sai ya ga Baba bai yi wata wata ba ya ce ya amince kuma so yake a ranar a ɗaura aure kuma su tafi da amaryar idan sun amince, idan kuma ba su amince a ranar ba, toh su ƙara gaba wani zai baiwa. Ganin haka yasa Alh Mahmud ɗin bai ɓata lokaci ba ya bada sadaki aka daura aure dama tare ya je da wani abokinsa da driver su suka zama shaidu aka ɗaura auren a nan Masallacin kusa da gidansu Rumana. Sai dai Rasuwar Hajja a ranar ne ya hana su Alh Mahmud su tafi da ita, suka ce a barta kawai har zuwa wani sati idan an yi sadakar bakwai zasu turo a ɗauke amaryar.

Duk da ba haka Baba ya so ba dole ya amince ba tare da kawo komai a ransa ba, tunda Tanda ya riga ya gargaɗesa kan kar ya yi binciki game da duk mutanen da za su zo neman auren Rumanar.

Bayan an yi sadakar ukun Hajja ne sai kuma Saif ya zo masa da maganar Suzuki na son auren Rumana. Ba tare da damuwar komai ba Baba ya gaya masa ya aurar da ita dan haka ya tashi ya basa wuri kar kuma ya sake yi masa maganar wani Suzuki. Haka Saif ya tashi ya tafi yana ta zage zage kan an hana Amininsa auren ƙanwarsa an baiwa wani da bai san ko waye ba.

Bayan an yi sadakar bakwai na Hajja Baba ya neme Alh Mahmud kan tarewar Rumana kuma ya nuna masu shi ba zai yi mata komai ba dan ba shi da zarafin yi mata. Dan haka duk abunda za su yi mata  idan ta je can sai su yi mata idan suna iyawa idan kuma basa iyawa su barta hakanan.

Ba tare da damuwar komai ba suka amince, aka turo mota ɗaya kamar yanda Baba ya buƙata. Shi da kansa ya bisu su ka je ya kaita gidanta da shi da matarsa. Cikin ransa yasan sati ɗaya ya yi yawa zata sake dawowa garesa dan biyan buƙatarsa.

Wannan kenan.


A gefen Baba kuma, lokacin da ya bar gidan Rumana ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba. Dan daga gidan bai zarce ko ina ba sai wurin Tanda. Abunda Tanda ya sanar da shi saura ƙiris ya yi ajalinsa haka ya koma gida cikin tsananin tashin hankalin da ya so ya haddasa masa ciwon zuciya.

Bai taɓa tunanin cewa mutane ɗaya ne suka zo neman aure Rumana a wurinsa ba sai yanzu da abubuwa suka kwance masa. Yasan Dr Abdulfatah Goni farin sani. Amma bai san Alhaji Mahmud ba, dan bai taɓa ganinsa ba sai ranar. Gashi ba shi da halin yin bincike tunda Tanda ya bashi sharaɗin kar ya yi bincike ga dukkan mutanen da za su zo nemanta . Da yasan su yan uwa ne kuma duka akan mutum ɗaya suka zo da ya aurawa Suzuki ita dan sai yanzu ne ya gane shine mutum na biyun da Tanda ke nufin ya baiwa.

  Tabbas sun mamayesa kuma ya rantse da ransa sai ya cika burinsa ko ta halin ƙaƙa. Yasan ta inda zai ɓullo musu kafin Tanda ya neme sa. Dan ya ce ya je zai nemesa idan ya yi wani aiki game da auren. Shi kuma a yanda yake ji yafi son auren ya mutu kafin Tanda ya nemesa saboda baƙin cikin da yake ji game da auren ba zai taɓa barinsa ya huta ba idan har ba kashesa ya yi ba, shi yasa yake tunanin fara gwada tashi basira ko zai dace kafin aikin na Tanda da ba nan kusa ba, dan har ga Allah ya fara sarewa da aikin bokan nasa duk da yana da yaƙinin cewa  ba zai taɓa bashi kunya ba, tunda shima yana yi masa yanda yake so......*****"

Kano

Tun lokacin da Abba ya kamata a motar Jamal ya ƙara ɗauke mata wuta gaisuwarta ma baya amsawa. Amma ita duk wannan ba shi ne damuwarta ba dan ita ba kasafai halin mahaifin nata na ko in kula ke damunta ba.

Babbar matsalar da take fuskanta fushin Ummi, Saboda a  yanda mahaifiyarta ke matuƙar ƙaunarta ba komai ke ɓata mata rai game da ita ba. Amma yanzu ta yi mamaki sosai da wannan karon ita ma ta ɗauke mata wuta baki ɗaya. Tana son Ummi sosai, fiye da kowa duniyar nan dan haka fushinta ne kaɗai ke damunta cikin gidan shi yasa kallo ɗaya zaka yi mata kaga tsantsar damuwa a tare da ita.

Yau tun safe gidan ya kacame da shiryen shiryen tarbon Abbakar. Anty dai aikin gabanta take dan duk habaicin da Ummi ke yi mata da irin gorin da take mata akan ta fita sabgar yaronta toshe kunnayenta take y, ta yi kamar bata san tana yi ba. Shi yasa idan zai dawo ko wannensu zai yi shirinsa dan tarbonsa hakan da take kuma ba ƙaramin sayo mata soyayyar Abba ya yi ba.

Zulaiha na zaune ta tasa tv gaba tana kallo a zahiri amma duka hankalinta yana kan mahaifiyarta dake jeka ka dawo tsakanin kitchen da falo. Tun gaisawar safe da ta gaisheta ta karɓa ba yabo ba fallasa bata sake ce mata komai ba dan duk yanda taso ta yi mata magana kasawa take dan bataga fuska ba.

Yau dai ta ƙudurcta a ranta sai ta sasanta da Ummie ko ta halin yaya, dan ba zata lamunce  Ya Abbakar ya dawo ba tare da ta sasanta da ita ba.

Ƙaurin da ta ɗan soma jiyowa ne ya katse mata tunanin da take, ta yi saurin shiga kitchen ɗin da sauri ta rage gas ɗin dake kunne tare da motsa miyar da ta fara kama tukunyar saboda yawan da wutar ta yi mata.

Da sauri Ummi ta shigo kitchen ɗin ta karɓi ludayin miyarta tana biyarta da harara, kafin ta soma magana cikin faɗa. " Kada ki sake taɓa min kayana tunda ba sakaki na yi ba."

Sosai hawaye suka fito idanuwan Zulaiha ta kamo hannyen Ummi cikin gunjin kuka.
"Dan Allah Ki yafe min Ummi. Ni kam ya kike so na yi da rayuwata ne? Ummie Abba baya kaunata kema kina so ki bi bayansa ko?  Ni ina ganin zan mutu ne kawai duk ku huta da ganina a cikin gidan nan tunda kowa baya ƙaunata." Ta faɗa tare da fashewa da kuka mai tsanani.

Nan take sai jikin Ummi ya yi sanyi. Duniya idan akwai abunda ke ɓata ranta bai wuce a taɓa Zulaiha ba. Ita kanta bata san ne ya hau kanta har tayi fushi da ita irin haka ba. Idan Zulaiha na kuka har wani

"Ban san me yasa kike so ki haifar min da hawan jini ba Zulaihat, ban san me yasa ba kya jin magana ba" cewar Ummie kamar zata yi kuka.

"Ummie ba gaskiya Abba ya gaya miki ba. Kema kin san ba zan aikata abunda yace miki na aikata ba dan ba tarbiyar da kika bani ba kenan. Kawai dai dan ya tsaneni ne yake so kema ki tsaneni"

"Ƙul! Kar na kara jin kin yi wadan nan kalaman ga mahaifinki, kina jina ko! Mahaifinki ba tsanarki ya yi ba na sha gaya miki haka. Dan haka ki je ki wanke idanuwanki ki zo mu ƙarasa girkin tunda kin yi blackmailing ɗina"

"That is my mother. Ummie you know i love you so much ko? And u are the best mommy ever." Ta faɗa tana mai fita kitchen ɗin cikin murna.

Girgiza kai kawai Ummie ta yi, tana ci gaba da aikinta amma cikin ranta tana tunanin irin soyayyar da take yi wa ɗiyar tata kamar ta saɓawa ƙa'ida.

Vote
Comment and
Share

Follow me @ayshartone.

Zuciya Da Hawaye Where stories live. Discover now