Yau satin Rumana biyu a gidan miji kuma tun lokacin da su Hajja Falmata suka zo babu wata rayuwa ƙwaya ɗaya da ta sake zuwa gidan cikin yan uwanta ko nasa.
Zata iya cewa ita kaɗai take rayuwarta a cikin gidanta, saboda ko shi kansa mai gidan ba kodayaushe take jin motsinsa ba.
Idan bata manta lissafi ba yau kusan kwana huɗu bata ji ɗuriyarsa gidan ba, marabinta da shi tun ranar da ya tashi jibgar ta saboda kayan jikinta. A ce warsa kayan da aka kawo mata ranar da su Hajiyya Falmata suka zo na uban waye.
Sai da ta ɗauki kayan ta kai ɗakinta sannan ta gane cewa ashe kaya ne aka kawo mata na sawa daga gidansu.
Ba laifi kayan sun yi kyau duk da cewa waɗanda aka ɗinka sun dan so su yi mata yawa. Amma dogayen rigunan ciki su na yi mata lafiya lau shi yasa ta zaɓi ta riƙa saka su kawai.
Misalin karfe uku na yamma tana zaune falo kamar yanda ta saba jikinta sanya da wata black ɗin riga da aka ƙawata da pappule and ash stones. Ta ja jela ta ɗaure daga baya, ta ɗaura ɗankwalin rigar a kanta. Ba laifi kayan sun mata kyau dan sosai suka fitar da dirin jikinta.
Tun wayewar safiyar yau bata ci wani abincin kirki ba. Takeaway ɗin da yake sanyawa a fridge kwana biyu bai saka ba tunda baya nan, wanda ke nan kuma ta cinye duka.
Tana nan zaune tana ta zullumin ta inda abinci zai fito mata, ta ji ana buga ƙofar gidan da ɗan ƙarfi. Tabbas ta san ba maigidan ba ne. Dan bai taɓa buga ƙofa ba tunda gidansa ne.
Bata kawo komai a ranta ba ta tashi ta je ta buɗe.
Take ta ji nunfashinta na neman daukewa lokacin da idanuwanta suka yi tozali da nasa. Cikin kankanen lokaci ta ji duniyarta ta tsaya mata cak! Wani abu ta ji ya tsayamata a ƙirji mai taurin gaske.
Kasa cewa komai ta yi sai jikinta da ya dauki rawa tamkar mazari.
Shi kuwa ƙare mata kallo yake yi tun daga samanta har ƙasanta. Kafin ya yi wata irin dariya da ta soma zama baƙuwa a gare ta.
"Sannu da zuwa Baba." Ta fada tana jin kanta na sara mata ganin shigar jikinsa da sam bata dace da wanda ya zo da mutunci ba ballantana wanda ya zo gidan surukinsa.
"Ummu Rumana!" Ya fada cikin wata murya da zata iya rantsewa bata taɓa saninta a cikin muryoyinsa ba.
Dubansa ya sake ajiyewa a falon yana mai ƙare masa kallo kafin ya ce.
"Me yasa kika wuce sati ɗaya a gidan nan?"
Nan take ta ji gabanta ya yi wata irin mummunar faɗuwa. Saboda bata yi da kowa sati ɗaya zata yi a gidan ba.
"Baba aure fa aka ce na ɗaura min, ban yi tunanin akwai wani ƙayyadaden wa'adi da ake ginɗayawa a rayuwa ta halali ba."
Wani irin tsalle ƙirjinsa ya yi. Yana mai jin tsoron abunda yake tunani na ƙara kama ruhinsa.
Bakinta ya kaiwa wani irin bugu mai zafi da bayan hannusa.
"Har kin yi bakin da zaki gaya min magana har haka Rumana?" Ya faɗa yana mai sake buɗe mata rikitattun idanuwansa.
"Ka yi haƙuri Baba amma ni ba wanda ya gaya min sati ɗaya zan yi a gidan nan"
"Ni ai na gaya maki yanzu. Dan haka yanzu yanzun nan za mu je ba sai anjima ba."
YOU ARE READING
Zuciya Da Hawaye
RomanceWani irin zufa mai yawa yake sharcewa a ko wace kusurwa ta jikinsa. Tun tana 'yar ƙanƙanuwar ta yake ɗauke da buri a kanta, yake so ya biya buƙatarsa gareta dan cimma wata manufa ta shi guda ɗaya da yake rayuwa domin ta a doron ƙasar nan. Amma ko da...