Babi na ashirin da biyu

124 12 1
                                    

"Abdulfatah dai ya riga ya rantse sai ya gurɓata mana zuri'armu da bare." Kalaman dattijuwar matar da suka gama zagaye dukkanin kunnuwan Rumana.

Tun lokacin da suka shigo gidan ta ji  hankalinta bai kwanta ba. Musamman da taga irin yanayin kallon ƙasaƙancin da dattijuwar matar da aka kira Hajiya Babba take yi mata tare da ahalin gidan.

Yanzu kuma da kalamanta suka ƙare sauka a kunnayenta yasa ta ƙara tabbatarwa kanta cewa ba ta ƙarbu ga matar ba kamar yanda ita ma matar ba ta yi mata ba.

Kallon Jabeer Hajja Babba ta yi da tun da ya gaida ta da sannu bai sake cewa kowa komai ba. Sai wayarsa da ya maidawa dukkanin hankalinsa tamkar babu wasu halittu a cikin ɗakin.

Ganin haka yasa Hajja Babba ta kallesa ta ce.

"Sannu isasshe! Nasan ai kasan ina gidan nan amma dan rainin wayo ba ka ga damar zuwa ka gaida ni ba har sai da na roƙa.  Koda yake ma ai daɗin abin ni nake iko da duk wanda yake ɗaure maka gindi a gidan nan har ka ke aikata abinda kaga dama.

"Hajiya da ma kin daina ɓata bakinki kan wannan ɗan hau, dan ubansa ya riga ya ɗaure masa gindin aikata abinda yaga dama sai dai kawai a kawo na gani a zuba masa, dan ni kaina ba zan iya tuna when last ya tako kafarsa cikin gidan nan ba sai fa kwanan baya kafin ya yi auren nan na asara da na ji an ce ya zo ya gaida ubans..." Hajja Falmata ta katse maganarta jin shigowarsu Khamal da uncle Sulaiman.

"Yau ƙanena ne a gidan nan ko idanuwana ne ke min gizo" cewar Khamala yana zama kusa da Jabeer.

Sai lokacin idanuwansa suka sauka ga Rumana da ke gefe kanta na ƙasa.

"Ko amaryar ce aka kawo ma Hajjiya Babba?" Ya faɗa yana murmushi.

Uncle Sulaiman da ya zauna kusa da Mahaifiyarsa ya ce. " Kar dai ka ce kaima ba ka je ka ga amaryar ba?"  Ya faɗa cikin shakiyanci irin nasa.

Murmushi Khamal ya yi ya ce" Uncle naso mu je da Nazifah ai abubuwa ne suka muna yawa wallahi. Amarya sannunki da fatar ba ki yi fushi da Babban yayan ango ba" Ya faɗa yana kallon Rumana da take jin kamar ta yi tsuntsuwa ta ganta gida.

Cikin jin kunya Rumana ta ɗago kanta tana gaidasu. Sai dai ganin mutumin da ke zaune kusa da Hajiya Babba ba ƙaramin tashin hankali ya sake sanyata ciki ba.

"Sule kunama!" Ta faɗa can ƙasan makoshinta yayin da jikinta ya shiga kakkarwar da ba lokaci ɗaya zaka iya ganewa ba.

Hajiya Babba ta ce. "Kai tafi can banza ai shi ne ya kamata ya kaimaku ita. Amma duk laifin mahaifinku ne da ba ya iya yi masa magana yake aikata abinda yake so ni ban taɓa ganin mutum irin Abdulwahab ba"

Cikin yanayin jin haushi Hajja Falmata ta ce. "Ai sai dai hakuri kawai amma tunda har kika bari ya chakuɗa jininsa da aljihun baya ba yan....." Maganarta ta katse jin yanda aka kira sunanta da ƙarfi.

Juyawa suka yi dukansu banda Jabeer da yanayinsa ya daɗe da sauyawa.

"Ki iya bakinki Falamata, kar ki ƙure hakurina in aikata abunda zamu yi nadama baki ɗayanmu." Ya faɗa cikin tsananin ɓacin ran da yasa ya kasa controling fushinsa a gaban mahaifiyarsa kuma surukarsa.

"Innalillahi wa'inna illahirraji'un a gabana yau kuma Abdulwahab? Lallai na yarda jinina ya surka da na ɓata gurbi. Allah ya isa tsakanina Hellina da ta kawo sauyi a zuciyarka" Cewar Hajjiya Babba tana taɓa hannayenta kamar za ta yi kuka.

Zuciya Da Hawaye Where stories live. Discover now