Babi na ashirin

73 9 1
                                    

Duka board members na kamfanin Amfagsons drugs field industry yau sun halarta a wurin meeting ɗin gaggawa da aka tara.

"Ko haed of laboratories zai tashi ya yi mana bayanin ta yanda aka yi aka samu mutuwar mutane kusan shidda a garin jos sanadiyar maganin da aka fitar a kamfanin nan cikin satin da ya gabata" cewar Uncle Sulaiman yana kallon Jabeer wanda kusan duka mutanen wurin shi suke kallo.

Sai da Jabeer ɗin ya ɗan ɗauki lokaci kamar ba zai yi magana ba kafin ya fara koro bayaninsa cikin ƙwararren turancinsa irin na mutanen amurka.

"Duka magungunnan da suka fita a satin da ya gabata an haɗasu ne a ƙarƙashin kulawata hakan ne yasa ba na tunanin akwai wani mistake da aka yi da har zai iya salwantar da waɗancan rayukkan da aka lissafa duba da cewa maganin da ya fita a satin da ya gabata duka antibiotics ne da ke ɗauke da less side effects ɗin da ko overdose ɗinsa aka yi ba zai yi wa mutum muguwar illa ba ballantana har ta iya kai sa ga mutuwa." Ya faɗa tare da janyo wani kwalin magani ya ɓalla ya jefa baki.

"Wannan shi ne maganin da ake zargin ya yi kisa a jahar jos. Gashi yanzu ni nasha kuma insha Allahu ba zai kashe ni ba." Ya faɗa tare da janyo wasu kwalayen da ke gefensa na irin maganin da ya sha, ya ci gaba da bayani.

Wannan da na sha mai jan kwalin shine exert irin wanda muka kai jos, kuma tare aka yi distribution ɗinsa da wannan mai green and yellow kwalin da aka ajiye a nan lagos Ibadan da enugu. jan ne kawai da ba ya da yawa aka kai jos saboda kaɗan suka yi requesting. My question here is me yasa sauran duka ba su yi kisa ba sai wannan ɗin da ya banbanta kawai da kwali?"

Sosai ɗakin taron ya ɗauki sowa kowa da abunda ya ke cewa, daƙyar aka samu suka yi shiru sannan ya ci gaba da bayani.

"Ina kira da ƙungiyar WHO da ta sanya pharmacies ɗin da aka yi ma distribution ɗin  maganin da su dawo da shi a ƙara bincikawa. Idan har aka bincika ba a samu komai da ke iya salwantar da rayuwa ba a ciki mu kuma zamu yi ƙarar duka pharmacies ɗin da suka kira kungiyar WHO dan su ɓata mana suna da wannan zan rufe jawabina nagode.." Ya faɗa tare da ɗan dafe kansa da ya soma yi masa nauyi saboda maganar da ya yi mai yawa.

Da yawa ba haka suka so ba. Sun so ne ya yi abunda zai dulmuye shi ciki dan a karɓe lasisin aikinsa. Amma ganin yanda mutane da yawa ke jinjina ƙwazonsa yasa suka sha jinin jikinsu.

Haka dai taron ya watse inda ƙungiyar WHO ta roƙesu gafara tare da basu tabbacin za ta sake gudanar da bincike kan inda matsalar ta samo asali.


"Kai ba zaka taɓa daina bawa mutane mamaki ba JB. Bravo!" Cewar Al'ameen lokacin da aka fito meeting ɗin.

Murmushi kaɗan Jabeer ya yi, yana sipping coffee a hankli yan lumshe idanuwansa da suka fara yi masa nauyi.

"Amma a ganinka a ina matsalar nan take ne? Al'ameen ɗin ya sake tambaya.

"I dont know. And ko ma a ina ne they can go to hell"

"Hmmm. Ka dai kiyaye dan Allah. Masu son ganin bayanka a kamfanin nan yawa ke garesu."

Jabeer bai ce komai ba dan yasan gaskiya aminin nasa ke gaya masa.

"Yaushe zan zo in ci tuwon amarya" cewar Al'ameen ɗin cikin tsokana.

Harararsa Jabeer ya yi yana sake jinsa cikin wani yanayi shi har ga Allah an takurawa rayuwarsa kawo yarinyar can da ta mannewa tunaninsa cikin duniyarsa.

Zuciya Da Hawaye Where stories live. Discover now