Kallo ɗaya za ka yiwa Baba ka tabbatar da yau Allah kaɗai ne zai hana sa ya kurɓa ruwan barasa, saboda tsananin ɓacin ran da yake ciki. Shi ba wai tafiya da Rumanar ne ya ɓata masa rai ba, irin maƙudan kudaden da ya gagara ci ne a cacar ke baƙanta zuciyarsa.Kallon Rumana ya yi da ke ta share hawaye tun lokacin da ta tabbatar da a cinyesa cacar. Wani abu ya ji ya tsirgar masa a zuciya da ya rasa gane ko meye, dan ya sani ba tausayin ta ba ne ya ji, saboda ya daɗe da raba hanya da tausayi tun lokacin da aka shiga tsakaninsa da burinsa.
"Ki daina yi min wannan kukan naki na banza, kwana biyu ne kawai zaki yi a wurinsa, kuma da kwana biyun ya cika ni da kaina zan je in ɗauko ki. Ke nama san ba ma dole ne ki yi ko da kwana ɗaya ba, ki dai je ne kawai, ai ni na san abinda na taka, wallahi dan uban mutum kuma dole ya barki ko waye shi wallahi." Ya faɗa wani alfahari mai girma na wanzuwa saman fuskarsa.
"Amma dai Iro kasan kana ɓata mani lokaci ko?" Sule Kunama ya yi magana cikin ɓacin rai.
Harara Baba ya watsa masa sanna ya sake kallonta. "Ki wuce ki bishi kar in saɓa miki."
Ya faɗa ganin kamar tana so ta gwada masa taurarin kanta. Ganin tana ja da baya yasa ya yi saurin kama hannunta ya jata har bakin motar mutumen yana mai sakin wani murmushi da shi ka dai ya san ma'anarsa
******************************!!!!Abuja
129 Street square."This is bullshit, wannan ai shirme ne" Ya fada cikin ƙaraji tare da rufe allon computer da ke gabansa da ƙarfin gaske.
This is what i have been telling you JB. Wallahi mutanen nan karensu kawai suke ci ba babbaka a kamfanin nan."
"I dont care Al'ameen. Ban damu ba duk abunda za ayi cikin kamfanin ba damuwata ba ce. Amma me yasa za ayi connecting issue din nan da kamfanin mahaifina?"
"Look Jb bana son ka yi wasa da damarka. Mutanen nan sun fi ka sanin aikinsu. Tunda har kaga sun nace kan wurin to tabbas suna da dalilinsu, kai dai just do as they want, ƙila ma wahalarka ce ta kuza zuwa ƙarshe."
Kallonsa Jabeer ya yi. Yana jin tamkar kansa zai tsage saboda yanayin da yake jin zuciyarsa a ciki. Tabbas duk ta inda yake tunanin abun nan ya wuce nan.
"Gobe jirgin ƙarfe nawa zaka bi zuwa lagos ɗin?" Al'ameen ya fada yana mai katse shirun da suka yi"
"Morning flight ne, amma zan maida shi next week akwai abunda ban kammala ba."
"Ya kamata dai ka sa himma dan ka fara process din da wuri, duk da nasan zaka samu duk abunda kake so a gurin Daddy, sai dai nasan akwai kalubale mai yawa a wurinsa musamman ma gurin Hajja Falmata, ka san ta yi ta yiwa Khamal fighting din kujerar ya hana." Ya fada yana kallon Jabeer da yanayin fuskarsa ya sake chanjawa zuwa tsananin ɓacin rai.
"I will not tolerate her this time a round. Wallahi Al'ameen ba zan taɓa raga mata ba idan har ta kuskura ta shiga rayuwata." Ya faɗa yayin da manyan idanuwansa ke canja kala zuwa wani launi mai ban tsoro.
Karan taba ya janyo ya kunna ya sanya baki yana mai yi mata zuƙar ala tsine. Kafin ya jinginar da kansa a kujera Ya lumshe manyan idanuwansa dake nuna alamar jin barci.
Ganin haka yasa Al'ameen ya yi ma sa Sallama ya wuce yana mai nema ma sa sauƙin damuwarsa a cikin ransa.
******************************!!!!!
YOU ARE READING
Zuciya Da Hawaye
RomanceWani irin zufa mai yawa yake sharcewa a ko wace kusurwa ta jikinsa. Tun tana 'yar ƙanƙanuwar ta yake ɗauke da buri a kanta, yake so ya biya buƙatarsa gareta dan cimma wata manufa ta shi guda ɗaya da yake rayuwa domin ta a doron ƙasar nan. Amma ko da...