Sosai Baba ke shafe zufan da ke tsiyayo masa ta cikin naman kansa.
Zaune yake gaban wani shirgegen mutumin dake sanye da wata jar riga mai yankakkaken hannu. Cikin wani irin yanayi mutumin ya kira sunansa.
"Iro, Iro, Iro! Kira nawa na yi maka?"
"Uku" Baba ya faɗa yana mai dafe zuciyarsa dake neman fitowa saboda firgicin kalaman da za su fito a bakin Tanda.
Wata dariya mai ƙaraji Tandan ya yi da ta karkaɗe ilahirin dajin kafin ya ɗaure fuska ya ce.
" Abu uku ne zan gaya maka. Na farko. Wa'adin zamanka da matarka Salamatu ya ƙare. Dole ne tayi nesa da duniyarka idan ba haka ba zata ɓalloma aikin da zaifi ƙarfinka.
'Dama bisa sharaɗinka nake zaune da ita. Ta daɗe da isata. Allah ya raka taki gone' Baba ya faɗa cikin ransa yana ɗan jin sanyi a zuciyarsa.
Tanda ya sake duba tukunyar dake gabansa yace. "Abu na biyu kuma, akwai wani ƙulli da ya soma kwancewa a cikin ƙullukanka. Sai dai Iya-ada na nan na ƙoƙarin ganin ta maidashi yanda yake saboda sadaukarwarka gareta, dan haka wannan bakada damuwa da shi.
"Abu na uku kuma, shine mafi muni a cikin abubwan nan guda uku. Naga tauraruwarka tana nan tana disashewa sauran haskenta ba zai wuce shekara ɗaya ba, ma'ana duk wata nasara taka a cikin shekara ɗaya ce tak, idan har aka shekara baka cika wancan sharaɗin namu na farko ba toh fa komai zai iya faruwa, idan nace komai ina nufin komai da komai"
Wani irin tsalle hantar Baba ta yi ta doke tsokar zuciyarsa jin waɗan nan kalaman na Tanda.
"Na shiga uku dan Alla...."
"Kada ka kuskura ka kira sunansa a nan"
Tanda ya katsesa cikin ɓacin rai."Ka yi haƙuri ba halina ba ne ya mai sharen hawaye. Ka taimake ni, ka bani wata mafita idan waccan ta farin ɗin ta gagara, wallahi ban san minene ke jikin yarinyar tawa ba da nakasa aiwatar da buƙatarka gareta ba. Ka taimake ni Tanda kamar yanda ka saba taimako na, bani da wata dabara da ta wuce abunda ka ɗora ni akai ko da yafi wancan aikin muni. Ka taimake ni kar duka sadaukarwata da wahalata su ƙare a banza"
Wani daɗi Tanda ya ji ya mamaye masa zuciya, saboda irin matsayin da Baba ke ɗorasa akai na ɗaya daga cikin nasarorinsa.
"Ba wata mafita sai waccen ɗin. Amma kar ka samu damuwa na gano maganin matsalar dake damun ɗiyarka bancin nasha wahala sosai." Ya faɗa tare da janyo wani ruɓaɓen kasko ya ɗan yi dan surƙullensa sannan ya ce.
"Aure shi ne makarin abinda ke jikin Yarka, dan haka zamu karya wancan aiki saboda idan har yarka bata yi aure ba abunda ke jikinta ba zai taɓa barinta ba. Sannan idan zaka aurar da ita, mutane na farko da za su zo neman aurenta kada ka kuskura ka basu ita saboda zasu iya zama barazana a gare ka har taurarwarka ta dusashe ba tare da ka cimma burinka ba. Mutane na biyu da za su zo neman aurenta kada ka hana musu, saboda su kaɗai zasu iya zama mataimaka ga buƙatunka abinda suke nema wurinta na lokaci ƙalilan ne da sun samu kai kuma zaka samu abunda kake nema. Sannan kuma kada ka yi bincike ga dukkanin mutanen nan da zasu zo a gareka."
Abun ya daurewa Baba kai sosai, sai kuma ya samu bakinsa da kasa tambayar Tanda manufar yin haka, saboda yasan ko yaushe ne zai gaya masa dalilinsa na yin abunda ya yi muddun ya aikata yanda ya ce masa. Yasan Tanda ba zai taɓa bashi kunya ba har abada.
YOU ARE READING
Zuciya Da Hawaye
RomanceWani irin zufa mai yawa yake sharcewa a ko wace kusurwa ta jikinsa. Tun tana 'yar ƙanƙanuwar ta yake ɗauke da buri a kanta, yake so ya biya buƙatarsa gareta dan cimma wata manufa ta shi guda ɗaya da yake rayuwa domin ta a doron ƙasar nan. Amma ko da...