Babi na ashirin da uku

81 6 0
                                    

Assalamu alaikum makaranta wannan labari ina mai baku hakuri na jina shiru da kuka yi na tsawon lokaci. Hakan ya faru ne sanadiyar uzurran rayuwa. Amma insha Allahu ina maku albishir na samun update akai akai kudai kawai kuci gaba da hankuri kuma kuci gaba da biyoni har lokacin da zan tsaida alƙalamina.

Nagode.






Jabeer ya fara falkawa, ya kai idanuwansa kan Rumana tana ta barcinta a hankali tamkar babu wani abu dake ruɗa duniyarta.

Jin kaifin idanuwansa a jikinta yasa ta buɗe idanuwanta ta watsa a saman fuskarsa. Wani irin ƙayataccen murmushi ne ya suɓuce a leɓenta da ya fito direct daga  zuciyarta.

Bai taɓa ganin murmushinta ba. Zai ma iya rantsuwa da Allah kan bai taɓa ganin fuskarta cikin yanayi irin na yanzu ba. Kallonta ya cigaba da yi yana ganin kammanunta na rikiɗewa suna komawa sak irin nata.

"Hamma!" Ta kira shi a hankali tamkar mai yin raɗa.

Janye idanuwansa ya yi daga kallon da yake yi ma ta, ya maida kansa gefe ɗaya yana jin wani yanayi na taso masa sanadiyar jin sautin da ta kira sunansa da shi.

"Hamma dan Allah kada ka kwanta ba tare da ka yi sallar asuba ba. Bai wuce mintuna biyar a tada sallah ba." Ta faɗa tana kai dubanta ga agagogon da ke manne a bangon falon.

Ba tare da ya ce mata komai ba ya miƙe ya nufi ɗakinsa. Ganin haka yasa ita ma ta miƙe ta wuce nata ɗakin tare da yin saurin ɗora alwala  dan gabatar da raka'atainil fajir kafin ta sauke farilla. Ta daɗe zaune tana azkar kafin ta sake hawa gado ta kwanta tana jin jikinta na yi ma ta ciwo saboda irin yanayin kwanciyar da ta yi a daren jiya.

Jabeer kuwa har zuwa yanzu bai daina mamakin kansa ba na bin umurnin Rumana da ya yi ba. Dan  duk yanda yaso ya kwanta kasawa ya yi har saida ya gabatar da sallar asuba kamar yanda ta buƙata.

Da ya gama sallar ma bai wani samu ya  kwanta ba  ya ɗauki system ɗinsa ya fara aiki.

Shi kansa yasan  ya ji daɗin barcin da ya yi a daren  jiya dan ya daɗe bai samu barci cikin nutsuwa ba irin na jiya.
Tabbas qur'ani rahama ne. Shi ba ma ba zai iya tuna when last ya buɗa qur'ani ya karanta shi ba.

Sosai yake jin zuciyarsa sakat tamkar an ɗauke wani ƙaton dutse a cikinta, shi yasa yake ta yin aikinsa cikin nutsuwa .

Ba shi ya tashi a gaban system ɗin ba har sai kusan ƙarfe bakwai, sannan ne ya je ya yi wanka ya shirya ya fita office ba tare da ya sake bi ta kan Rumana ba duk  kuwa da irin yanda take yawan zuwar masa a tunaninsa...**"*.

"Ni ban san ko sai yaushe ne zaki riƙa yin lamurranki cikin tako ba Falmata. Ko yaushe maganata ɗaya ce akan ki da ki riƙa rage zafafa al'amurranki kan wannan yaro.
Bana tunanin kin fini tsanarsa saboda kasancewarsa ɓata gurbi a cikin zuri'ata. Amma koyaushe ina ƙoƙarin ganin na kiyaye a gaban mahaifinsa  dan a zauna lafiya. Ke me yasa ba za ki riƙa kama kanki game da shi ba a gaban mahaifinsa ba? Sanin kanki ne cewa Abdu'fatah yana da rauni sosai game da Jabeeer. Me yasa ko yashe kike so ki yi abunda zai sa wankin hula ya kaimu ruwa ne? Me yasa Falmata?"

"Mama nima ban san me yasa nake yin hakan ba, ban san kuma ya zan yi in rage yi gaban Yaya ba.
Ba zan iya yi maki ƙarya ba Mama wallahi bana son ma na rage ɗin, saboda a cikin ko wace daƙiƙa ƙara tsanarsa nake yi a cikin raina. Bana son ina kallon Yaya ina ganin tarin kaunar yaron nan a cikin idanuwansa. Ina ji kamar in kashe kaina idan ina ganin soyayyar Jabeer fiye da ta ahalina a cikin idanuwansa." Ta faɗa tare da shafe guntayen hawayen da suka zubo a idanuwanta sannan ta ci gaba da cewa.

Zuciya Da Hawaye Where stories live. Discover now