"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un" Baba ya rika faɗ a lokacin da ya ji magangannu Rumana da Hajja.Dawowarsa masallaci kenan ya shigo gidan da niyar cin mutuncin Rumana na shanyasa da ta yi a waje yana jiranta. Sai dai yana doso daƙin ya yi tsaye cak sakamakon magangannun da ya ji Rumana na faɗi da suka kusa sumar da shi.
Sosai notukkan kansa ke kwancewa. Ya rasa gane ta inda ta samu ƙarfin guiwar faɗin magangannun da take faɗa.
Ya tabbatar da yau da ba dan aikin da ke kanta ba da tuni ta tona asirinsa, ga mahaifiyarsa.
Wani irin baƙin ciki ne ya tokare kirjinsa, yana jin magangannunta na dawowa cikin kwanyar kansa tamkar almara. Har shi Rumana zata iya buɗe baki ta ce ta yi nadamar kasancewarsa mahaifi a gare ta. Me yasa ta kasa fahimtar cewa, tana rayuwa ne kawai a doron kasar nan dan ya biya bukatarsa gareta.
Wani irin iska ya furzar, tare da ciza leɓensa na ƙasa.
Tabbas zai ƙara gyara shirinsa kar kallon kifi ya kaisa ruwa. Ba zai taba iya hakura da cikar burinsa ba, dan da zai iya da ya yi tun kafin wanzuwarta duniya.
Baki daya ma sai ya ji cacar ta yau ta fice masa a rai, shi yasa ya juya ya fita ba tare da ya kira ta ba.!!!!!!!!!!
Yan kwanakin nan yawan mafalkan da yake game da Jabeer su suka sanya shi cikin damuwa sosai har jininsa na yi masa barazanar hawa.
Yanzu ma da yake zaune waya ce a hannunsa yana trying dinsa amma sam ya kasa samunsa.
Hajja Falmata dake gefensa haushi kamar ya kasheta. Cikin kufula ta dubesa ta ce.
"Wai ni kam Alhaji Jabeer kaɗai ne ka haifa da zaka sanyawa kanka damuwa akan shi?
Wani kallo Alhaji Abdulfatah ya watsa mata mai tattare da kashedi.
Juyar da kanta ta yi, gefe tana taunar cingam
"Ka yi haƙuri amma gaskiya ce nake gaya maka"
Daga mata hannu ya yi.
"Nagode da gaskiyar da kike gaya min. Za ki kuma iya tafiya idan kin
Qare abunda ya kawo ki bana son damuwa Please." Ya faɗa fuskarsa ɗauke da damuwar da yake cewa ba ya so."To amma...." Sallamar Khamal ce ta katse mata sauran maganarta.
"Yauwa Khamalu zo ka kira min Jabeer da wayarka nasan kai kila zai ɗauki kiranka idan ka samesa." Dattijon ya faɗa ba tare da damuwar fuskarsa ta gushe ba.
Murmushi Khamal ya yi. "Daddy da ban dawo yau ba fa wa zaka sanya ya kira maka shi?"
"Da Mahmud zan kira in saya ya kirashi, dan nasan shi kaɗai zai sanya shi ya dauki kirana ba tare da an samu wata matsala ba"
Murmushi Khamal ya yi tare da fitar da wayarsa a aljihunsa yana cewa "Allah yasa in samesa dan nima ba kasafai nake samu ba. wani sa'inma idan na samu sai yaga dama yake daga wayar kasan halinsa, kowa bai bari ba." Ya fada yana daddana lambobin Qanen nasa.
Wata harara Hajiya Ruƙayya ke jifan Khamal da ita, tana jin tamkar ta shaƙesa ta karɓe wayar hanunsa. Duniya ita kam ta tsani wancan Jabeer ɗin. Ta tsanesa da dukkanin iskar nunfashin da take shaka a duniyarta.
YOU ARE READING
Zuciya Da Hawaye
RomanceWani irin zufa mai yawa yake sharcewa a ko wace kusurwa ta jikinsa. Tun tana 'yar ƙanƙanuwar ta yake ɗauke da buri a kanta, yake so ya biya buƙatarsa gareta dan cimma wata manufa ta shi guda ɗaya da yake rayuwa domin ta a doron ƙasar nan. Amma ko da...