Gudu take da dukkanin sauran kuzarin da ya rage a jikinta.
Tsoro take jin na tasowa yana lulluɓe dukkanin ruhinta. Tabbas yau shine na ƙarshen da zata sake amincewa Baba ya kai ta wani wuri. Ta riga ta kudurta a ranta cewa duk inda aka sake kaita ba zata sake zaunawa ba sai dai a fito da gawarta.
Wani wawan birkin da aka ja a gabanta ne ya sake tsoratar da duniyarta.
Ƙasa ta duƙa jikinta na matuƙar kakkarwa.
Da sauri ya fito daga motar ganin yanda hankalin yarinyar ya yi masifar tashi duk da yana da yaƙinin cewa ko zozar ta da motarsa bai yi ba, amma da yake shi mutum ne mai nagarta kuma mai tausayi yasa yakasa haƙuri har sai da ya fito dan ganin halin da yarinyar take a ciki. Dan ga dukkan alama a tsorace take.
"Subhanallahi. Allah yasa ba ki ji ciyo ba?."
Ya faɗa yana mai leƙen fuskarta ganin yanda taketa kakkarewa."Ki yi haƙuri dan Allah ban lura da ke b....."
Kalamansa suka yanke ganin yarinyar da ya yi tozali da ita.
Kasa gaskganta idanuwansa ya yi har sai da ya kullesu ya sake buɗewa.
Idan ba kwanyarsa ke nuna masa ƙarya ba ita ɗin dai ce da yake gani wasu lokutta a shagon saida abinci da ke gefen kamfaninsa. Haka kuma ita ɗin dai ce da ke wanzuwa a barcinsa mafi yawan lokutta.
Sai dai yau abun ya yi matuƙar tsorata shi ganin yanayin da ya ganta a mafalkinsa gata nan a irin yanayin a zahiri.
"Ka taimake ni dan Allah Baba wasu mutane ne suka biyo ni" Ta faɗa cikin tsananin ruɗewa. Tana waiwaya bayanta.
Saida ya ɗan yi jim kaɗan kafin yace ta shiga, Ba tare da tambayar inda zai kaita ba, saboda ganinta a irin wannan lokaci yasan ba zata wuce zuwa restaurant ɗinsu ba. Sai dai maganar cewa da ta yi an biyota ne yake tantama saboda yanayin wurin da ya ganta bai yi kama da wurin da yan iskan Lagos ke zama ba.
Ita kuwa Rumana kwata kwata hankalinta bai bata ta gaya masa inda zata je ba saboda lokaci ɗaya ta ji zuciyarta tayi ammanna da dattijon mutumin.
Sosai tayi mamakin ganinta gaban shagon mahaifiyarta tunda tasan ba ita ta sanar da shi ba . Sai dai ganin dattijon ya lankwasa motarsa ya shiga babban kamfanin da ke gurin yasa ta fahimce dalilin da yasa bai yi mata wasu tambayoyi ba. Ita sam bata san shi ba kasancewar bata ɗaya daga cikin mutanen da suke yawan rike fuskokin mutanen da basa cikin sabgarsu.
Da shigarta cikin restaurant ɗin ba ta tsaya wata wata ba kawai ta faɗa ban ɗaki ta ɗoro arwala ta gabatar da sallah tare da rokon gafarar mahaliccinta.
Mama ma sai da ta tambayeta dalilin da yasa take sallah wannan lokacin, sai kawai ta ce mata nafila ce take yi.
Ita kuma kasancewar ba wata masaniya addini ba yasa bata bi takan nafilar ba, ta ci gaba da sabgar gabanta ita da ma'aikatanta.
Rumana kuwa tsoro ne taf a ƙirjinta. Duk abunda ake yi mata bata taɓa yunkurin maida martani ba ko da kuwa za a kasheta ne. Amma yau ta rasa me ya hau kanta. Ta rasa me ya tunzura ta har ta aikata abunda ta aikata. Ita tsoronta ɗaya kar ta zamo sanadiyar rasa rayuwar Sule Kunama dan yanayin da ta barsa ciki tana da tabbacin sai wani hukuncin Allah idan zai tashi.
YOU ARE READING
Zuciya Da Hawaye
RomanceWani irin zufa mai yawa yake sharcewa a ko wace kusurwa ta jikinsa. Tun tana 'yar ƙanƙanuwar ta yake ɗauke da buri a kanta, yake so ya biya buƙatarsa gareta dan cimma wata manufa ta shi guda ɗaya da yake rayuwa domin ta a doron ƙasar nan. Amma ko da...