Chptar 18

2 0 0
                                    

🙆‍♂️ *UWATA CE SILA* 🙆‍♂️

          *By S REZA*

A

☀️ *FIRST CLAAlS WRITER'S ASSO* ....☀️

https://youtube.com/channel/UCbdwy4ipF9kQs-yzYtv3i2A 

 *My you tube channel🖕 please kumin subscribe* 


      *PAGE* 👉1️⃣8️⃣

...................... *BENUE STATE* Jibrin ne zaune a gaban Mom jikinsa har rawa yakeyi Mom ta ce "Kace kunyi magana da Ameera kuma kace itace ta ce kazo ka sameta a gida? Jibrin yace "A'a dama kawai naga ban ganta bane kwana biyu shine na ce bari nazo gida ko ba lafiya ba. Mom ta ce "To kai d'in waye a gurin ta?Jibrin fa ya rikice domin kuwa Mom ta masa kwarjini da zararr zaiyi maga sai ya din ga jin nauyin ta. Ya ce "Dama dama ni friend na tane. Cikin'bacin rai Mom ta ce friend ko? To dan ubanka tashi ka bar gidannan yaro 'karami da kai har zakazo har gida kana cemin wai kai friend d'in tane. Da sauri Jibrin ya fita daga palorn Mom kuwa ta biyoshi har waje tana zagin sa, shi kuwa Jibrin da wani irin gudu ya ture IRO Maigadi wanda ke tsaye ya ki bod'e 'kofar sai surutu ya keyi...

Mom ta ce "Kar ka sake barin kowa ya shigo gidannan "IRO Maigadi dake 'kasa ya ce "To hajiya in an fi 'karfina yazan yi. Mom ta ce "Me kace? Ya ce "Na ce bazan bar kowa ya shigo ba.

Alhaji lawan da Nana da Matarsa sun dawo gida lafiya in da yan uwa da abokan arzi'ki suke ta zuwa musu jaje, saide har yanzu basu san mai ya faruba da Nana ba su a tinanin su saceta a kayi kuma suka kar'bota, haka dai mutane suke ta zuwa suna fita. Washe gari Alhaji lawan ya samu matarsa wato Fatima ya ce "Tindade babu wanda yasan wannan maganar Dan Allah mu rufe wannan asirin mu biyu, Fatima ta ce "Kai a tinanin ka wannan abun zai rufene? Kasan fa zakuje kotu kuma duk abun da yaje kotu ai ya riga da ya baiyana, sannan kuma mutanan da zakuyi shara'a dasu manyan mutanene kaga kenann dole yan jarida su ji, kuma kaima ba 'karamin mutum bane. 

Alhaji lawan ya ce "Ni wallhi 'yan babban gidane bana son su sani in har suka sani to wallahi komai ya lalace, Fatima ta ce "To ai kuwa dole su sani domin kuwa suma ai zasuje gurin shari'ar. Alhaji lawan ya ce "No babu wanda zai je ni kad'ai ma na isa.

Fatima ta ce "To amma ai zaka sanar wa da yayanta ko? Nanma Alhaji lawan ya ce "na cemiki bana son kowa ya sani. Haka dai Fatima ta ha'kura ba dan tasoba, kuma duk da hakan bata ha'kura ba sai ta sanar wa da 'yan babban gidan.

'Ban garan gidan su Nusee kuwa Rakiya fa izuwa yanzu itama han kalin ta ya tashi, ita ba damuwar ta 'batan da Nusee tayi ba a'a ita damuwar ta yanzu bata da kud'i, shikuwa Daddy han kalin sa in yayi dubu to ya tashi, babu irin duban da bai yiba amma ko ina yaje sai ace batanan. Har gurin Mom wato gidan su Meera ya je amma ba ita suma har yanzu naiman Meera sukeyi. Ganin haka ne yasa ya ha'kura a kan koma ina taje da kanta zata dawo.

Mommy da kuma Kabir da sauran danginsu da sauran al'umma ne da suka halarci wannan shari'ar ne a gaban al'kali domin sauraron hukuncin da zai yankewa Najib. Gefe guda kuwa ga Uncle wanda shima an fito dashi Saboda shine ma haifin sa, yana staye tare da wani Police a bayansa. Ga kuma Nusee da Meera sun samu guri sun yi zaman sai mun ji 'kwa-kwaf.

 Al'kali ya ce "bayan 'kwararan hujjoji da kuma amsa laifi daga gurin wanda yayi laifi, kotu zata yanke hukunci dai-dai da abun da mai laifin ya aikata.

Al'kali ya ci gaba da cewa, dubada cewa mai laifin ba a cikin haiyacinsa ya ai kataba, sannan kuma bai kai she kara talatin (30)ba. Saboda haka wannan kotu mai adalci ta yankewa Najib Bashir hukunci zaman gidan kaso har na tsawon rayuwar sa tare da aiki ma tsananin. Wanda yaga hukuncin bai masaba zai iya d'akaka 'kara nann da watan hudu cikin wannan shekarar. Yana kaiwa nann ya buga wannan gudumar tasu ta al'kalai har sau biyo.

UWATA CE SILA. is true life story. CompleteWhere stories live. Discover now