🙆♂️ *UWATA CE SILA* 🙆♂️
( *By S REZA)*
☀️ *FIRST CLASS WRITER' SASSOCIATION...* ☀️
_Love all my fan's wad'anda na sani dama wad'anda ban saniba, love all🥰🙏._
*KASHI NA ASHIRIN DA D'AYA*
*PAGE* 👉2️⃣1️⃣
................. *UNCLE* Ya ce "Duk abun da yarinyar ta fad'a 'karyane shi bai ma santaba. Haka dai Alhaji mudi da Alhaji Bashir suka dage a kan su dai basusan komai ba kawai dai sharine a ka 'kullamusu. al'kali ya d'aga shari'ar zuwa ashin da d'aya ga wannan watan da muke ciki, kowa da ke cikin kotun sun jinjina wannan lamarin, yayinda al'kali ya bada umarnin a cigaba da tsaron su Alhaji mudi da Alhaji Bashir a police station. Kadija da megidan ta ABUJA suka huce, su Daddy kuwa da su baba'karami suma gida suka huce, yayin da S M yace zai zo gida amma sai ya kaiwa a bokin sa ziyara tukun.
Cikin tsananin 'bacin rai Meera ta ce "Ban gane abun da kike nufiba? Nusee ta ce "Dan Allah ki taimaka min wallhi da gaske nake ina son sa tin lokacin da na fara ganin sa naji ya kwanta min kuma zan... "Ya isa haka Nusee ya isa ya isa, Meera ta katseta cikin tsananin b'acin rai. Meera ta ce "Nusee kin san me kike cewa kuwa? 'dan gidan Uncle babban ma'kiyinmu shi kikeso, yaron da mukaje har gidansu muka ci masa mutunci shida mahaifiyar sa shi zakice kinaso?
Nusee ta ce "Ai bamu masu komaiba sabo da haka nidai wallhi ina son sa kuma so irin na aure. Wannan abun ne yasa su Nusee basu je kotu zam farkoba. Yayin da Meera tayi watsi da maganar Nusee, ita kuma Nusee tayi Al'kawarin sai ta mallaki Kabir koma mai zaifa.
Daddy ya kalli babban yaya MLM Sani ya ce masa "In har ta yarda ina son aje a nemamin izinin ta sai ta koma d'akina, MLM Sani ya ce "Kai amma gaskiya nayi farin cikin wannan abu, kuma in sha Allah zata amince kaga kawai sai a sha biki, haka dai suka cigaba da zan cen in har ta yarda to bikin bazai yi wani nisaba. Daddy tin lokacin da yayi ido biyu da Mom yaji ta kwanta masa, sannan kuma dama yana son yarama abun da Fatima ta masa na zuwa da tayi ta tona asirin Nana, dama yana son 'kara aure amma yarasa wacce yarin ya zai samu sai kawai yaga Mom.
Haka dai maganar ya je kunanan Hajjo ai kuwa Hajjo ta ce "Dama abun da ya kamata kenann hakanne ma zai 'kara 'karfin zumuncin naku. MLM Sani ya je har gidan Mom ya sameta da maganar Daddy a kan yana son auranta. Mom tayi shiru tana tinani sannan tace "Ita gaskiya bazata yi wani aureba mutu'karr ba'a ga Ameera ba, domin bata da kwanciyar hankalin da zatayi wani auran a halin yanzu.
MLM Sani ya ce "Dama ba wai yanzu-yanzu za'a yi auranba yana son dai ki amin ce masa ne? Mom cikin rashin jin dad'in wannan maganar ta ce "Tom zanyi tinani. MLM Sani ya ce "tom Allah ya sa muji allkairi domin kuwa muna son 'kara d'ongon zumuncin mu ya 'karu.
Mom taje ta samu Uncle Bala da maganar auran ta da Daddy ya ce zaiyi. Uncle Bala ya ce "Alhamdu lillh dama ai kece da taurin kai in namiki maganar aure sai kice ke bazaki iya zaman gidan wani kuma Ameera ta tashi a matsayin agolaba, to yanzu dai gaishi uban Ameera d'in ne kinga kuwa babu maganar agolanci tin dade a yanzu batada wani uban da ya huceshi, ko da aure zatayi to shine mai aurarr da ita.
Jin hakanne yasa hankalin Mom ya kwanta kuma taji ta amin ta da wannan auran, ammafa sai taga Ameera. Uncle Bala ya ce "Aisha kenann ni nace Miki Ameera ba 'bata tayiba ki kwantar da han kalin ki da kanta zata dawo kiyi auranki kawai, amma Mom ta ce "Itafa sai anga Ameera.
Haka Daddy yazo har gida gurin Mom ya sanar da ita bu'katar sa ita kuma ta amince amma akan cewa sai anga Ameera kafin a d'aura aure. Daddy ya ce "Ayi auran kafin a nemota amma Mom ta ce "No. Hakade badan Daddy badan yasoba ya bari a kan cewar ko yau a kaga Ameera to gobe za'a d'aura auran.
![](https://img.wattpad.com/cover/323867620-288-k291310.jpg)
ВЫ ЧИТАЕТЕ
UWATA CE SILA. is true life story. Complete
Любовные романыLabinrin mai cike da abun al'ajabi da tsan-tsar cin amana da soyayya mai zafi. labarin tausaya illar watsi da zuminci, sakacin iyaye ga yaransu. labarin Meeera And Nusee.