❣️❣️❣️❣️❣️❣️
*RANSTUWAR JINI*
*(THE BLOOD VOW)*
❣️❣️❣️❣️❣️❣️
*EPISODE 7*
*STORY AND WRITTEN*
*BY*
*MAMAN NOOR**THE PATIENT*
............................ Umma! Umma! fito fito kiji abinda na jiyo, umma dake zauna akan y'ar dardumarta tana d'an gyangyad'awa rik'e da y'ar dogon carbinta.
Haba Ummi! wannan irin kira ay sai kisa jinin mutum ya hau fiyeda kima, ke kenan kullum ba kya abin masu hankali. Ummi da ko kad'an maganar UMMA bai dama ba, ta k'araso wajen umma dake k'arasa sauka daga stairs.
Umma wallahi ba kiji labarin danaji bane, mai firgitarwa, ay kuwa nace banci na zama ba, ko jira a fara event d'in send off d'in banyi ba, na wanke k'afa na dawo, don nace labarin nan sai a kunnen ummata.
Umma ta d'an ja kunnenta suka k'arasa ga kujera tana fad'in amma Ummi keba k'aramar ja'irar yarinya bace, yanzu akan wata banzar labari kikazo kina tsunduma min kira tamkar na ciyo miki bashi.
Ummi ta d'an janye kunnenta tace gaskiya Ummi hannunki badai zafi ba, wataran ay sai ki ciren kunnen gabad'aya.
Umma da bata d'auki maganar Ummi da wata muhimmanci ba, tace ay dayafi, kinga mun huta da kwarototo koda yaushe.
Ummi ta d'an bata rai, jin haushi, Allah Umma ba don ke bace da na hak'ura da baki labarin.
To ni Ummi yaushe na ce miki ina sha'awar jin batun mutane, kul fa! na haneki da d'auko rahoto da kuma cin naman mutane.
Ummi ta turo baki gaba ta kauda kai gefe, wai nan ita an b'ata mata rai.
Umma ta girgiza kai, ta mik'e tana fad'in idan kin gama kumbure kumburen kije d'akin yayanku ki gyara masa kafin ya dawo.
Ta tashi tana bubbuga k'afa, Allah Umma yaya fa ya sani a gaba a gidan nan wai nice nan na dawo mai aikinsa, to gaskiya Umma kisaka shi yayi aure mu huta.
Umma taci gaba da tafiya tana fad'in ke me yasa ba zakiyi auren ba, naga har waya kikeyi da samari a b'oye, ko kin zata bansani ba.
Cab! ni nayi aure hauka nakeyi, haka kawai wani k'ato ya yauderani da sunan aure, bayan an kwana biyu yayi min koran kare da takardar saki, shikenan na zama bazaura, kamar YANDA d'an iskan NAJEEB d'in nan yayiwa aunty HUMAIRA, gashi yanzu ta shiga duniya babu wanda yasan inda take.
Cak Umma ta tsaya tamkar wacce aka tsayar da remote control, ta juyo tana kallon ummi da ta cigaba da b'ab'atun ta. Ummi me kikace? kamar naji kin ambaci HUMAIRA da wasu shirmen zance.
Ummi ta d'an had'e rai tana wani shan k'amshi, yo UMMA ba daman ke kika k'i tsayawa saurarona ba, ay labarin danake son baki kenan akan HUMAIRA
UMMA ta sauko da sauri daga stairs, Ummi kinga banson shashanci, waya fad'a miki wannan magana.
Umma wallahi ba k'arya nake ba, wannan cousin d'in NAJEEB, watake da suna ma.. uhmm yawwa Rufaida ita ke bada labarin a wajen send off d'in mimi da naje d'azu.
Harda cewa saki uku yayiwa HUMAIRA, sannan ya kwace AMAL yayi mata korin kare, shine bak'in cikin hakan yasata shiga duniya.
Innalillahi wa inna ilaihirraji'un kawai Umma ke maimaitawa, wannan wace irin masifa ce ke kunno kai.
Ummi anya kin tabbata kinji da kyau kuwa? ko dai wata HUMAIRA take nufi, Ummi ta ciro wayarta daga y'ar k'aramar pos d'in dake hannunta
Tayi y'ar danne dannenta saita ciro wani hoto ta nunawa UMMA kin ga hotonta tareda NAJEEB da Amal, wannan hoton sun d'auke shi sallar azumin daya wuce a gidansu HUMAIRA.
Ta mayar da wayan jaka tana fad'in UMMA ina fad'a miki RUFAIDA y'ar uwarsu NAJEEB ne, tana gaban mahaifiyarsa ne da zama, kinga kuwa dole tasan komai nasan kuma bazatayi irin wannan k'arya ba, don jin dad'in bakinta ba, ta riga da tasan HUMAIRA y'ar uwatace.
YOU ARE READING
RANSTUWAR JINI (The blood vow)
RandomThe story of a love triangle, twist and deception RANTSUWAR JINI labarine da a sanadiyyar RANTSUWAR JINIn mutum biyu, yayi sanadiyyar rushewar farin cikin mutane da dama