Ranstuwar Jini(the Blood Vow) 10

7 1 0
                                    

❣️❣️❣️❣️❣️
*RANSTUWAR JINI*
*(THE BLOOD VOW)*
❣️❣️❣️❣️❣️
*EPISODE 10*
*STORY AND WRITTEN*
*BY*
*MAMAN NOOR*

*My sweet wedding days*

.......................... I won't say anything about what happened tsakanina da NAJEEB a wannan ranar, but all i know shine munyi alk'awarin rik'ewa juna alk'awari har tsawon shekarun da dukkannin mu zamu kammala karatunmu.

Awannan lokacinne kuma soyayya mai k'arfi ta k'ullu a tsakaninmu, bama kwana mu tashi ba tareda mun ji muryan junanmu ba.

Mutane da dama na mini kallon shashasha mara wayo, wacce NAJEEB zaiyi amfanine kawai da ita ya barta, banga ya aureni ba, tunda y'an gidanmu basu kai y'an gidansu kud'i ba, kuma babu wanda baisan NAJEEB da neman mata ba har sai zuwa lokacinda wannan lalurar tasame shi kafin ya saduda ba don Allah ba.

Mutane da yawa kan yi mamakin me nayi masa ma tun farko ne ya warke, wasu na ganin iyawata ce a matsayin nurse mai basira yasa shi warkewa.

Yayinda wasu ke ganin baiwace kawai daga Allah, da kuma sanin sirrin addu'oi ya taimaka min wajen warkar dashi da yardan Allah.

But for some people dama asali tun farko nina shirya hakan, ni nayi masa wani asirin da tsiddabarun so i could get chance to come near him, tunda gashi daga zuwa kusa dashi babu wanda yasan abinda ya faru gashi ya warke.

Nidai ban damu ba, ban kuma d'auki ko d'aya daga cikin suspicion d'insu a matsayin abinda zai sani na bar abinda nayi niyya (wato soyayya da NAJEEB d'ina)

A kwana a tashi ba wuya a wajen Allah yayinda nake kammala degree d'ina na farko a fannin nursing, NAJEEB d'ina saura saura sati uku ya dawo.

Murnar dawowarsa kad'ai ya hanani natsuwa, nasamu damar yin tawa murnar gama makarantar.

Kullum saina tambayi FATI ta bani shawarar abinda zanyi idan ya dawo, har FATI ta gaji dani, ta fara shareni.

A ranar dana graduate daddy ya ban kyautar key mota Honda accord, wayyo dad'i kamar nayi yaya.

Dama tun ina aji hud'u na koyi tuk'in mota, so ban sha wahalar morar abina ba, a cikin gari sai yawo dama gani y'ar son k'arya, kullum sai naje na d'auki FATI mun tafi yawo tunda tare muka graduate babu mai abinyi acikinmu.

A watarana ana saura two days NAJEEB ya dawo nida FATI  mun tafi Dinner  classmate d'ina zaliha wacce aka d'aura aurenta a yau da rana, so i was among the bride maids, naci kwalliyata cikin shigar doguwar rigana cot lace marun da head bak'a, nayi kyau sosai ni kaina na shaida hakan.

Duk da cewa FATI bata cikin k'awayen amarya, amma haka na sata dole tasa ankon, nima na d'inka mata da kaina, mutane da yawa sun san k'awancen mu, so idan ma baki samu dukanmu biyun a k'awayen ba, dole ne kiyi hak'urin ganinmu tare a wajen bikin ki.

Lokacinda muka shiga cikin event hall d'in, mun same shi acike dam da mutane, don har anyi nisa da farawa muka shigo.

Nan fa idanuwa suka dawo kanmu, har saida MC ya cire k'ida ya fara min kirarin Aishatul HUMAIRA kyakkyawa mai kyan suna, y'ar fara mai dogon gashi, a kyawun sura bakida tamka.

Oh my goodness! dake ba kunya gareni ba, haka na fara taka rawa ina juyi tun kan na k'araso, dama most of my mate sun san ni da son casu habawa sai fili ya kaure.

Maza da mata sukayo kaina, daga masu yi mini manni da masu snapping pictures sai masu tayani takawa.

I was the talk of the day, har naje na zauna wasu basu bar d'auka na a hoto ba.

Fati da tuntuni ta nemarwa kanta gurin zama ta harereni tace sai yanzu kika gama iyayin naki? nayi murmushi cikeda jin dad'i nace ya son ranki, ke ma kinsan na wuci masu iyayi, tsantsar class kikeji.

RANSTUWAR JINI (The blood vow) Where stories live. Discover now