RANTSUWAR JINI(THE BLOOD VOW)26

9 0 0
                                    

❣️❣️❣️❣️❣️❣️
*RANTSUWAR JINI*
*(THE BLOOD VOW)*
❣️❣️❣️❣️❣️❣️
*EPISODE 26*
*STORY AND WRITTEN*
*BY*
*MAMAN NOOR*

*THE NEW SAGA*

_________________ Ya ma za'ayi na girka abinci don cikina kazo ka bud'e k'afa da k'aton bakinka ka cinye, bai d'ago ba ballantana ya nuna cewa dashi yakeyi. ya k'araso inda yake zaune hannunshi rik'e da wani kopi ya d'auke plate d'in wacce ke cike da soyayyen chips da kwai asaman shi.

Wannan karon he has no option than ya d'ago, ya kalli BASH daya d'auki plate d'in ya koma kujeran dayake facing d'insa ya zauna yana kai lomar chips bakinsa batareda ya damu da NAJEEB dayake kallonsa ba.

Kaifa bak'aramin mugu bane Bash, yanzu me kake nufi daka kwace abincin, ko kunya bakaji ba. Bash yayi dariya yana kurb'an ruwan shayinsa.

Kunya gaba muka bata ba baya ba, kai ina kunyar taka take lokacinda na gama shan wahala nayi girkina kazo da waftareren hannu ka d'aga  without my consent, sannu d'an masu kunya.

Naji, basai ka zageni ba, kaine wahalalle saika tsaya girkawa, kasan abinci saidai banyi niyyar ci ba, order kawai zanyi akawo min, ko kuma na kira salima tazo ta girka min.

Oh! Samira, Bash ya maimaita yana tauna abinda yasa a baki, dama har yanzu baka bar yaudaran yarinyar nan ba. Najeeb da yayi niyyar tafiya, amma sai yaja ya tsaya yana yiwa Bash wani irin kallo

What do you mean by the kalmar yaudara da ka fad'i? oho kafini sani ay

Najeeb yace oh nagane you're now her spokesperson, to k'orafi bai karb'u ba, bari ma na fad'a maka da kyau, you can even go and tell her for all i care, banasonta, bana k'aunarta, she's not the type of woman i want, the only person danakeso kuma zan iya komai akanta itace HUMAIRA

BASH ya kuma fashewa da dariya, amma NJ kamar ka tab'u a kwakwalwarka, or maybe kasamu memory loss. for all i can remember shine kasaki lovely HUMAIRA ka, saki d'ayi d'ayi har uku, don haka HUMAIRA ta haramta da kai yaro think twice.

NAJEEB ya tako har gaban Bash da idanuwansa da sukayi kalan b'acin rai, yasanya hannu ya buge plate d'in chips d'in gaban Bash, ya juya yana fad'in you should learn to mind your business, idiot!

Bash ya bi chips d'in dake zube a k'asa da kallo, sannan ya d'aga murya, shege d'an bak'in ciki, wato bakaci ba nima bazan ci ba, to Humaira dai tayi maka nisa, ta haramta da kai, naga yanda zakayi ka dawo da ita.

Ya tsuguna ya kwashe chips d'in tas ya mayar plate d'in yana fad'in duk bakin cikinka sai naci, atoh yunwa dai ba danginmu bace.

Shi kuwa NAJEEB yana shiga d'ari ya fad'a kan gado yana jin wani irin k'una da zogi a cikin zuciyarsa, kwata kwata har yau ya kasa yarda shine ya saki Humairansa, yarinyar dayakeso tamkar bugun numfashinsa, yarinyar dayake jin gwara da ya bari sun kashesu gabad'aya a wannan lokacin daya fiye masa wannan k'unci dayake ciki.

Ya shafa saman k'irjinsa yana jin yanda bugun zuciyarsa yake k'aruwa tamkar ana buga ganga, tabbas wannan bugun zuciyar tasa tana kamada bugun k'arfin son dayake yiwa Humaira ne, yana jin son ta na bin jinin jikinsa a kowanne bugun second, to ahaka ne za'ace masa ya loosing Humaira, waye zaiyi tunanin jini da hanta suna rabuwa? never! never would he stop loving Humaira, and never would he accept loosing her.
Ya tashi cikeda azama tunowa da yayi kwana biyu bai kira sanata Binta ba, kamar jira take ya kira, bugu d'aya ta d'auka cikeda jin dad'i take tambayar sa, son badai kyakkyawan albishir bane zaka bani?

Ya b'ata rai yana wani shashan k'amshi tamkar tana ganinsa, ni momy ba dogon zance na kira muyi ba, just want to know if Humaira is back?

Ta b'ata rai itama tamkar a gabanshi, yanxu son har yanzu maganar yarinyar nan bai bar bakinka ba, duk k'ok'arina akan ka manceta amma all in vain

RANSTUWAR JINI (The blood vow) Where stories live. Discover now