RANTSUWAR JINI(THE BLOOD VOW)27

7 1 0
                                    

❣️❣️❣️❣️❣️❣️
*RANTSUWAR JINI*
*(THE BLOOD VOW)*
❣️❣️❣️❣️❣️❣️
*EPISODE 27*
*STORY AND WRITTEN*
*BY*
*MAMAN NOOR*

*MY HUSBAND AND I*

_________________ Tun shigowarsu gidan, mai aikinsu MIRIAM ta rakata d'akin da aka ware a matsayin nata, aikuwa tana shiga ta cire hijabi ta bi lafiyar gado, tun lokacin kuwa take ta bacci tsawon awa biyu, dama Humaira akwai son hutu ga bacci, ballantana da aka kawo ta nan sunayi mata alluran dayakesa bacci, yake sa hutu da rage stress wato  "MIDAZOLAM INJECTION" is an injection that put someone to sleep and relieve anxiety.  

BIBA kam dataga tayi bacci sai ta kwantar da Isha datake ta jujjuya idanu tak'i yin bacci yau, inji BIBA wai tana murnan mamanta ta ganota ne yanzu. Ita kam bata zauna a d'akin ba, tana kwantar da ita ta fita y'ar k'aramar barandar dayake bayan d'akin saboda d'auraye wasu kayan data cire tun kwana biyu dasuka wuce. dama BIBA mutum ce mai tsananin tsafta, batason datti ko kad'an, shiyasa bata bari kayan sawarta yayi datti a jikinta, da wuri zata ciresa ta canza. duk kuwa da cewa akwai washing machine da kullum sai mai aikin gidan MIRIAM tace ta kawo ta wanke mata a cikin washing machine d'in, amma sai tak'i wai ita bata yarda da wani wankin inji da duk zai sa kaya yayi laushi yana darewa da kanshi.

MIRIAM tun nayi mata magana akan hakan har ta gaji ta bari, kayan ISHA kawai take wankewa, saboda umarmine daga wajen asalin mai gidan.

Shi kam yana shiga d'akin shi ya shiga bayangida ya sakarwa kansa shower, yana tsaye ruwan zafin na zuba a kowanne sak'o na jikinsa tana ratsawa tun daga saman lallausan sumar kansa yana bin saman fuskarsa tana shiga har cikin k'wayan idonsa.

Haka ya barta tana sauka a fuskarsa tsawon mintunan da zai iya kaiwa biyar, kafin yaja wani dogon numfashi ya girgiza kai, sannan ya bud'e idonsa yana mai sanya hannu ya kashe kan shower. ya kuma sanya hannu ya share fuskarsa zuwa kansa yana furzar da hayakin dayake cikin bakinsa.

HUMAIRA! naji ya fad'i yana mai kallon tafin hannunsa datayi jajir dashi, ya dunk'ule hannun tamkar zai kaiwa wani nashi da ita, yafi minti biyu yana kallon hannun ko me ya faru da hannun tayi jaaa sosai ta kwaye amma da alama ciwon bana yanzu bane, ya sanya hannun acikin ruwa kafin ya kuma cirewa yana yarfewa gefe, na sake jin yace HUMAIRA wannan karon da kana iya hango d'an guntun murmushi a fuskarsa.

Ya sanya bathrobe, yayi alwala ya fito yayi sallah, sannan ya shirya cikin shigar k'ananun kaya wanda yafi yi anan tunda sukazo.

Keys d'in motarsa ya d'auka yasa a aljihu tareda wayarsa daya rik'e a hannu ya fita daga d'akin, har zai wuce, ko me ya tuna sai ya nufi d'akin daya bata a matsayin nata, yayi sallama kafin ya shiga, saidai as usual shiru kakeji tamkar babu kowa aciki.

Bai tsaya jiran sai an amsa masa ba ya tura k'ofar d'akin a hankali yana k'arawa da wata sallamar da iyakarta lab'en bakinsa ne. still cikin d'akin shiru harya fara tunanin ko basa ciki ne, sai idonsa ya hango mishi su kwance akan gado.

Ya kad'a kai yana tuna da tabbas dole yasameta tana bacci, saboda effect na alluran da akeyi mata, bai gama barin jikinta ba. dama yaya HUMAIRA asalinta akwai son bacci, ya lura da hakanne lokacinda suke aiki tare, yasha isketa most of the times akwance tana bacci a nurses ward, idan yayi tambaya ko lafiya take bacci, sai ace masa lafiya lau, kawai wai bacci takeji shiyasa.

Awannan lokacin, bai tab'a cewa a tasheta ko kuma yayi mata fad'a akan hakan ba, saboda shima yasan she's hardworking, a duk cikin nurses d'in yafi jin dad'in aikinta fiyeda kowa, saboda zafin nama datake dashi da kuma jajircewa akan aikinta, amma kuma bai tab'a complementing d'inta ba, shiyasa ma basa shiri, saboda ita a tunaninta yafi kowa tsanarta, shikuma yana ganin kimar igiyoyin aurenta, shiyasa yake d'auke kai a duk wani ragama tata.

RANSTUWAR JINI (The blood vow) Where stories live. Discover now