❣️❣️❣️❣️❣️
*RANSTUWAR JINI (the Blood Vow)*
❣️❣️❣️❣️❣️
*EPISODE 6*
*STORY AND WRITTEN*
*BY*
*MAMAN NOOR**THE PREGNANCY*
.............................. kwance yake asaman kyakkyawan faran sofa daya sha shimfid'a da k'ananun kyawawan throw pillows daya yayi pillow da wasu, wasu kuma ya rumgume a k'irjinsa.
Ta fito daga bedroom d'inta tayi wani arniyan dressing mai d'aukan hankali. Idan ka kalleta a wannan lokacin sai ka rantse zataje gasar kyau ne na duniya.
Abinda zai baka mamaki shine yanda take iya yawo da wani irin takalmi mai shegen tsini ta k'asa a dandamalin tiles d'in d'akin, ko shakka babu tayi kyau sosai Masha Allah da ita.
Harta k'araso inda yake bata bar karairaya ba, shigar jikinta ma kawai abin kallone, wato wata y'ar ficilar riga ne mai hannun shimi ajikinta wanda ko guiwa bai kai, sumar kanta a bud'e yake babu ko d'ankwali a kanta, sai y'ar k'aramar head band data kama gaban kan dashi, sauran kuma ta bajesu a gadon baya tana tafe suna tashi dama suna nan curly ne wanda suka rarraba kansu agefe da gefe, in which bazaka gane whether it was naturally or hand made.
Anutse tacigaba da taku mai matuk'ar jan hankali, cikeda nutsuwa da yanga, babu abinda yake k'ara a d'akin face takun takalminta.
Adaidai gabansa ta tsaya, tana jifansa da k'ayataccen murmushi daya kasa barin fuskarta, saida ta gama yi masa kallon k'urilla, sannan ta durk'usa gabanshi tana mai shafa sumar kanshi ahankali hankali tamkar mai yi masa susa.
Ya d'an gyara kwanciya tareda rumgumeta ajikinsa batareda ya bud'e ido ba, tayi murmushi cikeda jin dad'i ta kissing d'in kumatunsa tareda janye jiki, tana mai hura masa iska a kunne.
Ya d'an yamutsa fuska kafin ya bud'e ido a hankali yana kallin kyakkyawan fuskar abin k'aunarsa, yayi murmushi kamar yanda tuntuni take aika masa.
Love! la'asar fa tayi, ta fad'i tana d'an jujjuya Idanu cikeda kissa, ya tashi zaune yana mai janyo ta saman cinyarsa,kafin yayi k'ok'arin bud'e idanun da har yanzu suke yi masa nauyi a hankali ya d'an k'are mata da kallo kafin ya kalli window waje da d'anyi duhu babu hasken rana ko kad'an
Ya kama k'asan hab'arta yana kallon kyakkyawan fuskarta yace what time is it? ta kalli ogogon dake d'aure a hannunta na dama tace 10 minutes pass 4, ya d'an dafe kai da hannu sannan ya kuma kallonta da d'an serious face yace FARIDAAA! ya kira sunan da d'an ja.
Tayi saurin mik'ewa tareda rik'e kunnuwa, am so sorry love kai d'in ne bana gajiya da kallonka, yanzu ma da k'yar na iya daurewa na tashe ka, you look so beautiful and cute while asleep. and kaga garin yayi duhu hadari ne ya had'u sosai a wajen, and the weather is so cold out there.
Ya mik'e shima batareda ya kuma cewa komai ba, ya d'auki shirt d'in sa dake saman sofa yasaka akan farin singilet d'in dake jikinsa, harya fara tafiya FARIDA tace love!! ya juyo a slow motion yana d'an yayyamutsa fuska, ta jujjuya jiki tana mai d'ad'aga rigar jikinta tace bakace nayi kyau ba, yayi mata kallon few seconds kafin ya jinjina mata hannu da babban yatsa, duk da ba haka taso reaction d'in sa ba, amma tayi masa uziri may be he's still tired that's why.
Batayi k'asa a guiwa ba, ta tashi ta nufi kitchen, tasanya cook d'in ta girka masa d'an abu mai ruwa ruwa da sauri kafin yayi wanka ya fito.
Tana dawo falo ta mik'e k'afafu tana cin Apple tana kallon K drama series cikin nishad'i da kwanciyar hankali.
Dr Mansour tagani cikin shiri ya fito da sauri yana receiving call, tayi saurin mik'ewa cikin kulawa ta tari gabanshi, love ina kuma zakaje da yammar nan.
Ya cutting call d'in ya k'arashe da am on my way. ta kuma cewa love ina kuma zaka bayan nasa ayi maka girki?
Yayi mata peck a kumatu ya sab'i coat d'insa a kafad'a yana fad'in till i come back babe.
YOU ARE READING
RANSTUWAR JINI (The blood vow)
RandomThe story of a love triangle, twist and deception RANTSUWAR JINI labarine da a sanadiyyar RANTSUWAR JINIn mutum biyu, yayi sanadiyyar rushewar farin cikin mutane da dama