❣️❣️❣️❣️❣️❣️
*RANSTUWAR JINI*
*(THE BLOOD VOW)*
❣️❣️❣️❣️❣️❣️
*EPISODE 18*
*STORY AND WRITTEN*
*BY*
*MAMAN NOOR**THE PROPOSAL*
...................... Kedai sadiya akwai d'an banzan surutu, wai anya ba kya zuba mana yawu a cikin abincin mu kuwa
Sadiya dake tuk'a tuwo asaman gas cooker, tacigaba da tuk'a tuwonta tana fad'in, ay wallahi Hajiya bakiji yanda matar ke zagin shi tana d'ebe masa albarka a cikin jama'a ba, wai duk don zai k'ara aure bai fad'a mata ba.
Hajiya RAFI'A dake cire wasu vegetables tana jerawa a wani tiren dake gefe, dama ta shigo kitchen d'in ne saboda had'awa mijinta miya, yau zai dawo, yawancin lokuta haka take, bata bari wani yayiwa mijinta girki, indai bawai bata gida ba, duk da cewa Sadiya na k'ok'ari sosai wajen girki, shiyasa yanzu ma ta barta ta tuk'a tuwon, duk da haka akai akai rana dubawa.
Ta rufe freezer da k'arfi ta juyo tana fuskantar Sadiya, idonta fal masifa, to ke Sadiya da kika kawo labarin kina jin dad'in bayani, ce miki akayi zan goyi bayanki ko me?
Sadiya tayi saurin toshe baki tunowa da wa take magana, ta cire muciyar tuwon tana dariya k'asa k'asa.
Oh dariya ma kikeyi, ay kuwa gara kiyi ta a b'oye don naga hak'orinki a gabana kina dariya saida zubar dasu.
Sadiya tace haba hajiyar mu tana cigaba da dariya, me yayi zafi kuma? hajiya Rafia ta b'ata rai ta hau ta fad'a, tambaya ta ma kikeyi sadiya, amma anya sadiya ba mijin wata kike shirin k'wace ba kuwa? kinsan zawara wan nan munfi tsoron ku, sadiya da ba kasafai take saurin fushi ko wata bak'ar magana yake b'ata mata rai ba, ta kuma yin dariya tace Hajiya kenan, yo ni wahalar da nasha a gidan miji har naji sha'awar k'ara aure nan kusa, shima don na rusa farin cikin wata, ay ni bazan iya ba.
Hajiya rafia ta d'an sake fuska tace da kuwa yafi miki, don ni bana d'aukan duk wani injustice daya shafi k'arin auren da maza, na sha fad'a miki ba d'aya ba biyu ba, ni ko hanyar da kishiya tabi mai sunan nawa, to har abada na yafe wajen, to ma yaushe zan sake har hakan ta faru dani ban d'au mataki ba. shegiya tuni zan tisa k'eyarta gaba.
Sadiya ta bud'e baki tana kallon Hajiya rafia da mamaki, duk da cewa ba yau ta fara jin hakan ba, amma kullum tayi irin wad'annan kalamai sai sadiya ta sandare da mamaki.
Ta cigaba da kad'a kai tana jinjinawa kishin irinsu Hajiya rafi'a da shekaru sun riga da sun ja, amma kullum kamar a nayi mata fanfon kishi.
Amma hajiya yanzu yanda kike wannan kishin kuma sai ki bari mansur d'inki ya k'ara aure koh? sadiya ta k'arashe tana kallon Hajiya rafi'a saboda ganin reaction d'inta.
Hajiya rafi'a ta d'auko tiren vegetables d'in data ajiye, ta tako a hankali tana hararan sadiya, saida ta iso daf da ita, kafin ta ajiye tiren a gefe, ta d'an k'arewa sadiya kallo, kafin tace mata a hankali.
Sadiya na fara lura da take taken ki fa a gidan nan , naga kamar lumbu lumbu kikeson mun ki rufe ni ruf da bak'in mayafi, to bari kiji na fad'a miki, idan ma plan d'in auren mansur d'ina kikeyi, to ki watsar, don ina nan nida kaina na isheki.
Wa ma ya fad'a miki ni irin uwayen mijin da kika saba gani ne, to bud'e kunnen ki kijini da kyau kyau yanda na tsani kishiya, haka na tsani sunanta a wajen kowa nawa, koda kuwa ace sirikata ce, ballantana sirikar kirki irin FARIDA, ay sai na zab'eta na watsar da MANSUR d'in muddin ya zab'i ci mini amanarta.
Kin ma tuna min wai ina mansur d'in ya shiga ne kwana biyu bana ganin shi?
Sadiya da bata daddara da magana tayi caraf tace, Hajiya nima fa na lura mansur ya rage zuwa gidan nan, kuma jiya inajin aunty Farida datazo tana waya dashi kamar ranta a bace yake, wai ina yake zuwa kwana biyu ko zaman gida bayayi kuma ta bincika wai asibitin ma ba ko yaushe bane yake zuwa, sadiya ta kuma yin k'asa da murya, anya Hajiya ba auren nan mansur yaje yayi kuwa a b'oye tunda kinga mazan nan sun maida yin haka kamar Ado.
YOU ARE READING
RANSTUWAR JINI (The blood vow)
RandomThe story of a love triangle, twist and deception RANTSUWAR JINI labarine da a sanadiyyar RANTSUWAR JINIn mutum biyu, yayi sanadiyyar rushewar farin cikin mutane da dama