❣️❣️❣️❣️❣️❣️
*RANTSUWAR JINI*
*(THE BLOOD VOW)*
❣️❣️❣️❣️❣️❣️
*EPISODE 16*
*STORY AND WRITTEN*
*BY*
*MAMAN NOOR**DR MANSUR*
*not edited please, ayi hak'uri da typing errors😖*…................... Lokacinda daya shigo gida FARIDA na bacci don haka batasan ya shigo ba, shima bai damu ya tasheta saboda yana buk'atar hutawa. saidai hutun dayake son yin bai samu damar yi ba saboda yawan kiraye kirayen da ake mishi akan some patients da kuma rashin ganinshi da ba'ayi ba a wannan aikin da aka d'ora shi akai.
And tunda ya dawo ya kasa daina tunanin yanda ya barota da halinda take ciki, tabbas tana buk'atar k'yakkyawan kulawa if not akwai yiwuwar faruwar damages da baison tunada hakan.
Ya sanya hannu ya cire tie d'in wuyansa dayake jin tana neman damunsa, yafi mintuna yana kallon white d'in jikinsa datayi dabb'are dabb'aren dattin k'asa da jinin jikin HUMAIRA daya b'ata masa jiki, kwata kwata ya rasa tunanin daya kamata yayi akan HUMAIRA nan, a ido gata very innocent abin a tausaya mata, but idan ka dubi actions d'in ta sai kaji tamkar babu shed'aniya irinta.
Ya fisge rigan da k'arfin tsiya, yana tuno da ranar da aka bashi test results d'inta, da kuma yanda Ramsy ke fad'in "yanxu HUMAIRA ciki kika yarda kikayi, cikin ma na bariki" lallai tabbas wannan maganar tayi zaman daram a cikin k'wak'walwarsa taki goguwa duk kuwa da irin son ta gogen dayakeyi. he hates a loose woman komai kyanta fita take a kansa
Shiyasa duk y'an matan nan masu rawan kai, da yin matsastsun kaya suna rataya gyale a wuya basu tab'a birgeshi ba, baya kuma tunanin akwai yarinyar dazata birgeshi bayan FARIDA.
Work out room d'insa ya shiga bayan ya gama sauya kayan jikinsa zuwa k'aramar wando iya guiwa da kuma singilet.
Power lift ya d'auka yana d'agawa kamar yanda ya saba, saidai duk seconds sai ya tuno da maganar Dr Muhammad dayake cewa "Ta tilastawa mijin ya sake ta gudu ta shiga bariki"
Yayi wurgi da abin yana haki saboda sam ya kasa concentrate yayi training d'in yanda ya kamata, he don't know why he's always thinking about a loose girl like her, a hali irin nata ko hate d'in sa bai kamace ta ba, saboda she don't even deserve to be think of talk less of feeling pity for her.
Love ya haka zaka cire min k'afa ne? ya tapping goshinsa da hannu, irin shit d'in nan kafin ya d'ago da sauri yana kallon FARIDA dake tsaye a gefen power lift d'in daya jefar yanzu.
Am sorry! fatan bai ji miki same ki ba? ta b'ata rai ta juya k'eya gefe tana fad'in i don't know.
Ya mik'e tsaye ya nufota don yasan FARIDA sarai da y'an k'ananun shagwab'a, yanzu nan wai fushi take yi.
Ya rik'e kwankwasonta ya juyar da ita, ya d'aga mata giran ido ba tareda yayi magana ba, ta sak'ala hannayenta a saman wuyansa ta zagayesu. why did you came back ta tambayesa tana kallon k'wayan idonsa.
Ya sanya yatsa yana zagaye saman fuskar ta dashi, cikin salon iya sarrafa mace yace cos of you dear.
Tayi murmushin da tuntuni babu a fuskar ta tace da gaske love saboda ni ka dawo. yayi murmushi yana k'ok'arin b'oye damuwar dayake ciki, bayason k'arya kuma bayason ayi masa, but bazai iya fad'awa Farida gaskiyan abinda yasa ya dawo ba, yasanta da kishi yanzu zata fahimci zancen a baibai.
Tunanin shi ya katse lokacinda da wayar sa ta fara ringing ya cirota daga aljihun wandonsa, Anti momi daya gani shi yasa ya kuma jin wani iri, ya d'ago kai yana kallon Farida kamar yanda itama ta kafa masa ido tanayi masa kallon tuhuma.
Ka amsa mana love, ko ba Anty momi bane, ya maida wayar cikin aljihunsa ya kissing d'in goshinta, sannan yace kyale aunty momi nan, tun jiya ta dameni wai bana zuwa gidanta.
YOU ARE READING
RANSTUWAR JINI (The blood vow)
SonstigesThe story of a love triangle, twist and deception RANTSUWAR JINI labarine da a sanadiyyar RANTSUWAR JINIn mutum biyu, yayi sanadiyyar rushewar farin cikin mutane da dama