❣️❣️❣️❣️❣️❣️
*RANTSUWAR JINI*
*(THE BLOOD VOW)*
❣️❣️❣️❣️❣️❣️
*EPISODE 30*
*STORY AND WRITTEN*
*BY*
*MAMAN NOOR**MY WORTH*
___________________ BIBA na kwance can k'uryan gado, yayinda BABY ISHA ke kusa da ita,d'akin yayi shiru tamkar babu wani mai numfashi aciki dukkanin su suna sharar baccinsu. kamar yanda kusan kowa a wannan lokacin yake bacci saboda hutu daga al'amuran bawa na yau da kullum.
Saidai abin ba haka bane awajen HUMAIRA, ita nata hutun daban yake dana sauran bayin Allah, ita nata hutun yakan zo ne jifa jifa acikin kowanne bugun dak'ik'a, minti, hour, rana ku, kowanne sati, wata, ko kuma shekara, baza ta iya cewa ga specific lokacinda ta mori tsantsar farin cikin a cikin wad'anda lokutan.
Rayuwarta cike take da k'alubale kala kala, rayuwarta na d'auke da mummunar destiny had'e da tarin darrusa masu tarin yawa, littafin rayuwarta nada tsayi da fad'in da ba kowa zai so k'arasawa ba, ba kuma kowa ne zai k'arasa batareda ya zubda kwalla ba.
K'alubalen rayuwarta ya fara ne daga lokacinda ta focussing all her life determination on that idiot, that good for nothing of a man, that person that ruins her family happiness, wannan mutumin da a sanadiyyar sa tayi vouching d'in daya koma kanta yana hunting d'in nata rayuwar, a duniyar nan kowanne bawa da nashi k'addaran da kuma yanda rayuwa zatazo masa, kowa da sanadin calamity sa, sanadin kuka da dariyansa, amma ita nata sanadin yazo mata a matsayin NAJEEB! NAJEEB is really a curse in her life.
Ta fashe da kuka tana fad'in i hate him, i really hate him, tayi saurin toshe bakinta, saboda gudun muryanta ya fita ganin datayi BIBA na juye juye, ta tashi da gudu ta bud'e k'ofar barandar d'akin tana cigaba da kuka tamkar ranta zai fita, ta zube guiwowinta asaman tiles d'in wajen, hannayenta bibbiyu asaman fuskarta wanda duk ya jik'e da hawaye ya b'ata mata fuska da gaban rigarta.
Oh really! you are regretting being alive kenan koh? tayi shiru na d'an dak'ik'a, kafin ta d'ago jajayen idanuwanta tana kallon shi.yana tsaye asaman kanta ya d'aure hannayensa asaman k'irjinsa, daga shi sai y'ar k'aramar half jeans da farar singlet a jikinsa.
Ta sanya hannu ta share hawayen fuskarta, tareda mik'ewa tsaye tana gyara dogon rigan baccin da tsantsin sa yake sa shi tattarewa ya kama jikinta.
Cikin sanyin murya daya dad'a mak'alewa ciki saboda kukan datayi, tace sorry ba haka bane na kasa bacci ne. Exactly ya fad'i yana dad'a kureta da lumsassun idanunsa, wanda ya kafeta akan wuyanta daya sha y'ar k'aramar plaster, ya gimtse idanunsa yana tuno yanda taji wannan ciwon, ya kuma bud'e idanunsa dake cike da bacci da tarin damuwan da ba sai an jira harshe ta furta ba.
Kin hanani bacci, k'aton muryanki har d'akina, why are you crying? yayi mata tambayar cikin sanyin muryan da bata tab'a ji ba, hakan kuwa ya dad'a karya mata zuciya, ta d'an k'ure shi da ido, sai ta kuma fashewa da kuka tana girgiza kai.
Ya lank'washe wuya yana kallonta cikeda mamakin what is making her cry, i didn't know that you can cry like a river, ay da tuntuni na nemo miki abun tara hawaye it might be handy, ta kuwa k'ara sautin kukan ta harda d'an buga k'afafu irin yanda yara keyi, itama cikin kuka tace why are you always grumpy, yanzu kukan nawa shine abin wasa a wajenka, ay atleast sai ka tambayeni HUMAIRA why are you crying this late? wani abun kikeso ne? ask me with so much care da zanji dad'i, but kazo kawai kana min dariya.
Ya k'ara fad'in idonsa, did she just say wai yanayi mata dariya, yaushe yayi hakan, lallai kam anyi gaskiya da akace fear women no matter how young they are, yanzu wani da baya wajen ay sai ya yarda da abinda ta fad'a, ya zuba mata idanu yana kallon yanda take yin abu tamkar y'ar 17, so it is true da aka ce mata ko sun shekara nawa ne kamar yara suke.
Ya kad'a kai yana kallon yanda take cigaba da kukan ta harda kwalb'e hanci, duk ta sukurkuce ta fita out of shape, she's not good at crying, ko don bai saba ganin tana kuka bane, she's always brave, yana wuya kaga ta nuna gazawarta a abu, koda kuwa gashi a fili wannan abin yafi k'arfin ta.
YOU ARE READING
RANSTUWAR JINI (The blood vow)
CasualeThe story of a love triangle, twist and deception RANTSUWAR JINI labarine da a sanadiyyar RANTSUWAR JINIn mutum biyu, yayi sanadiyyar rushewar farin cikin mutane da dama