❣️❣️❣️❣️❣️
*RANSTUWAR JINI*
*(THE BLOOD VOW)*
❣️❣️❣️❣️❣️
*EPISODE 8*
*STORY AND WRITTEN*
*BY*
*MAMAN NOOR**Momma's Boy*
.......................... Washe gari da k'yar na iya tashi daga bacci.
HUMAIRA ta d'an yi wani irin dariya mai k'ayatarwa wanda zee bata tab'a ganin tayi irinsa ba.
Tacigaba da fad'in wato aunty zee abinda ya bani dariya na tuno da yanda na uzzirawa kowa sai an kawoni asibitin na duba shi a wannan daren ke kyace wani k'anin ubanane shi.
Ummah tayi fir ta fitittike ido wai babu inda zanje, ay bani kad'ai bace likita a asibitin. ni kuwa harda cewa Ummah idan banje ba zai iya mutuwa.
Ummah ta kuma hayayyak'o min, ta inda take shiga bata nan take fita ba.
Abba ne ya cooling maganar akan abarni naje, ay aikin ceton rai nake yi, ba don Ummah tasoba na tafi a wannan daren Abba yasa driver ya kaini har cikin asibitin.
Aunty zee bansan ya zan iya kwatanta miki irin tashin hankalin dana iske ba a cikin asibitin ba, so horrible.
A harabar asibitin naga mutane gam sun cika sai jiniyar ambulance dake tashi a tsakiyan wajen.
Ay kuwa da gudu na k'arasa ga jikin gadon da aka nad'osa tamkar gawa, ga mutanen danake tunanin y'an uwa da iyaye ne sun baibayesa sai kuka sukeyi tamkar an riga da ance ya mutu.
Security basu barni na isa ga inda yake ba sukayi saurin yi mini katanga.
Na shouting ku barni naganshi na 5 minutes don Allah. attention d'in mutane gabad'aya ya dawo kaina.
Security sukayi saurin pointing d'ina da bindigoginsa, dolena na tsaya cak, saboda a yanda sukayi mistake kad'an idan nayi a wannan lokacin zasu iya harbina.
Waje yayi tsit tamkar babu wani mai numfashi a wajen sai ni, saboda numfashin danake mayarwa saboda d'an gudun danayi tsakanin wajen da akayi parking d'in motar mu.
Who are you? Naji an jefo min tambayar batareda nasan wanda yayi min ba.
Yawwa wannan ay itace yarinyar da ake magana akanta d'azu.Kowa yayi shiru yana kallonta, sai kuma wannan matar da har wannan lokacin bansan wacece ita ba, ta tab'e baki tace su sauke bindigar su sa mata d'a a mota.
Bansan me doctor iliya ya fad'a mata ba, naga ta d'ago kai tana kallona, kallo irin na k'ask'anci, kafin naga ta juya tayiwa doctor iliya magana.
Sai naga an bani hanya na iso, anan fa dramar zai tashi ta kuma yin wani irin dariya tace Aunty zee baki tambayeni with all this running, stressing and drama na zuwa wajen only for me to be there and start thinking why am there at the first place.
Wallahi aunty zee na durk'usa a gabanshi a wannan lokacin ne kawai amma Allah yasan ko kad'an bansan me zanyi masa ba.
Banda hawayen dana farayi tamkar an aikosu, d'aya na bin d'aya.ganin ya kuma yin fiyau dashi tamkar wanda babu jijiyan Jini a jikinsa, duk da cewa yini guda ba,a bar saka masa Jini ba, har wannan lokacin akwai ledan jini a d'aure a hannunsa.
Rigan jikinsa irin na asibiti ne da ake sawa patient da hula, ga wanda yasanta yasan light blue ce, amma a yanzu da Jini ya b'ata rigan ta koma jazur saboda jinin dake zuwa ajikinsa minti minti.
Audugan da aka toshe masa kunne da hanci sun jik'e jak'ab, na sanya hannu na cire su, na karb'i wasu a wajen medical team d'in wajen na saka masa.
Saina koma nayi tagumi kawai ina k'are masa kallo tamkar abinda aka kirani yi kenan.
YOU ARE READING
RANSTUWAR JINI (The blood vow)
RandomThe story of a love triangle, twist and deception RANTSUWAR JINI labarine da a sanadiyyar RANTSUWAR JINIn mutum biyu, yayi sanadiyyar rushewar farin cikin mutane da dama