❣️❣️❣️❣️❣️❣️
*RANTSUWAR JINI*
*THE BLOOD VOW*
❣️❣️❣️❣️❣️❣️
*EPISODE 35*
*STORY AND WRITTEN*
*BY*
*MAMAN NOOR**ENTANGLED*
*NOT EDITED*
__________________ Yau sati guda kenan tun bayan incidence d'in daya faru tsakaninta da Dr MANSUR, wanda ta d'auke a matsayin mistake, ko kuma ace just a sacrifice. duk da cewa deep down inside her is something she really can't forget.Komai takeyi idan taji sunan MANSUR ko muryansa sai ta tuna. ga wani uwar kunyar sa datake ji tamkar ta nitse k'asa ta b'uya. shiyasa ma tun ranar ta tsiro da wani wasan b'uya dashi.
Tun ranar bata k'ara yarda ta fito waje ba, tana can cikin d'akinta da BIBA da itama ta saka mata takunkumin dole, akan lallai saidai ta daina fita, tayi ta zama suna hira, idan kuma ta fita, to saidai idan taje nemo musu abinci don wai bataso yasamu damar shigowa.
Shiyasa tun ranar basu sake had'uwa dashi ba, ko d'aki bata bari a bud'e saboda wai kar ya shigo, unknown to her kullum da daddare sai yasa key ya shiga ya duba su tukunna ya fita.
Yau ma as usual, ta shiga wanka ta bar BIBA da baby Isha tana canza mata diaper, dama kullum lokacin wankarta kenan bayan la'asar, duk kuwa da cewa tayi da safe to da yamma ma sai tasa keyi saboda yanda take claiming jikinta nayi mata k'arnin goyo, sometimes ma idan taso sai tasa keyi ma da daddare.
Tana gama wanka ta d'aura y'ar k'aramar towel d'inta wanda bai gama isa guiwa ba, ta d'aura d'ayan karamin akanta, saboda sumarta data wanke
Ta fito tana cewa gaskiya BIBA baki sirka min ruwan nan yanda nakeso ba, nida nace miki jikina duk tsami yake yi mini, inason ruwa mai shegen zafi da zai sauke mini gajiya, shine zaki had'a ni da ruwa kamar na wankan jarirai.
Cak taja ta tsaya baki bud'e tana kallonsa cike da tarin mamaki daya kasa b'oyuwa a fuskarta. yana zaune a bakin gadon ta, rumgume da baby Isha data kafa masa idanu irin kallon yaran nan, ya d'ago kai yana kallon yanda tayi tsamo tsamo da ita tamkar kifin da aka cire daga ruwan zafi.
Suna had'a idanu tayi k'asa da kai, tana wasa da gefen towel d'inta ta k'asa. duk ta rikice ta rasa abinda ya kamata tayi.
Good afternoon! taji ya fad'i kamar daga sama, ta kuma d'ago kai da sauri tana kallonsa, saidai abinda ya bata mamaki, tamkar bashi yayi maganar ba, ganin yanda ya ta'allaka dukkanin attention d'insa akan baby Isha dake b'angale masa baki.
Sai kuma taji babu dad'i, ay koma dai menene MANSUR mijinta ne, he has some rights akanta wanda sam ta kasa saukewa, yanzu duba wai tanada miji amma kusan sati guda amma basu had'u ba, and when they finally meet she can't even greet him, sai shine zai gaisheta, really!
Ta tako a hankali tamkar kwai ya fashe mata a ciki, saida ta iso daf dashi sannan ta tsaya tace ina wuni Dr ya aiki.
Ya kuma d'ago kai yana kallonta, tayi k'asa da kai saboda yanda k'wayan idonsa keyi mata kiranye (injita).
Saidai a madadin ya amsa mata sai taji yayi shiru, wanda hakan yasata cikin tsarguwa, ta kuma d'agowa, still ita yake kallo da seductive eyes d'insa, kallon dayaja attention d'inta ga kallon inda yake binta da mayen kallo.
Tayi saurin had'e cinya tareda sanya hannu ta kare jikinta, ganin still bai bar kallonta ba, wanda ta lura da kallon shak'iyanci yake yi mata, sai tayi saurin juyawa zata koma, saidai from nowhere taji an saka mata k'afa, tayi k'ara cikeda mugun tsoron da taji harta sadakar zataji ta a k'asa , saidai abinda bata tsammani bane ya faru.
Ta kuma zaro zara zaran idanuwanta,
tana kallon k'wayan idonsa daya kafeta dasu, ta gimtse idanu saboda yanda take jin bambarak'wai na zamanta asaman cinyarsa gashi yasa hannu yayi mata shield babu ta yanda zatayi ta kubce masa.
YOU ARE READING
RANSTUWAR JINI (The blood vow)
RandomThe story of a love triangle, twist and deception RANTSUWAR JINI labarine da a sanadiyyar RANTSUWAR JINIn mutum biyu, yayi sanadiyyar rushewar farin cikin mutane da dama