❣️❣️❣️❣️❣️
RANTSUWAR JINI (the Blood Vow)
❣️❣️❣️❣️❣️
*EPISODE 4*
STORY & WRITTEN *
BY*
*MAMAN NOOR **The video*
........................ Awannan daren Aunty B ta dawo, wanda a dalilin dawowarta aka had'a liyafa ta musamman acikin gidan, wanda HUMAIRA tayi ta mamakin irin mutanen da suka halarci taron. tabbas sai awannan lokacin ta yarda da cewa lallai wannan gida ba alkhairi bane agareta, to amma abinda ya kuma d'aure mata kai shine yanda ta kasa aiwatar da komai tun zuwanta gidan, tabbas tunda ta bud'i ido ta ganta a gidan take jin zaman wannan gida bai kamace ta ba, amma sam ta kasa yunk'urin barin gidan, duk da cewa ko mai gadi babu agidan amma tamkar wacce ake d'igawa k'aunar zaman gidan acikin zuciyarta ko yaushe takeji, ta rasa dalilin hakan.Haka tayi ta rarraba ido tana son hango wacece Aunty B da kowa yake ta korawa da kuma son ganin ta, meyasa take da mutane haka? kowa Aunty B! Aunty B! tayi ajiyar zuciya tana kallon ruwan abarban dayake kofin tangaran dake hannunta tace ko dayake da gani babban macece mai fad'a aji to amma...
Aunty B! Aunty B! kawai taji ana fad'i cikin hargowa da kirarin ban girma, ta d'an gyara tsayuwa tareda d'an jan d'amammen siket d'in da Billy tasata sawa k'asa, ganin yana d'angale mata bayan matsan ta dayayi, gashi Billy ta kafa mata sharad'in bata isa ta cire ba, saboda ba'a sanya manyan kaya idan Aunty B na gida, idan kuma zata karya doka ne, to fa she's on her own, haka Billy tayi ta juye juye tamkar macijiyar data mak'ale acikin bako. Sai tsaki takeyi akai akai saboda, gundura datayi da tsayuwar wajen, ballantana data kuma bud'e ido taga karafkataf idanun gantalallalun mazan na kanta, kowa sai rarraba idanu yake a inda yake ganin tafi dacewar kallon ajikinta. Wannan ya kuma assasawa HUMAIRA jin tsanar wannan baiwar Allah mai suna Aunty B da tuntuni sun kasa ganin walk'iyarta.
Alast! Yanzu kam ta bayyana, wato the long awaited Queen of the show! wato Aunty B.
HUMAIRA ta bud'e baki cikeda mamakin ganin Aunty B da tuntuni ake kurantawa, aketa mitsiltsilar nunata, wata y'ar ficilar mata da bata wuci ayi lomar tuwon k'arshe da ita ba.
Wai! sunan wani abu wai shamulok'i inji HUMAIRA dake k'ok'arin danne dariyan dayake kunno mata saboda yanda taga Aunty B ke k'ok'arin juya d'uwaiwan da batadasu da sunan tana rawa.
Duk yanda HUMAIRA taso danne dariyarta ta kasa, wai wannan itacen matan da tuntuni suke zaman jira tamkar wata matar governor, wallahi wannan batada maraba da sandar rake,tsigau fiyau take babu wani waje da zaka kalla ajikinta mai alamun tsoka sai dan tudun fuskanta dake d'an cike.
Amma duk da irin yanayin jikinta, haka ta zage take juyin rawa ga wani siririn takalmi data saka tamkar mai shirin lek'a future.
Saida ta gama y'ar sharholiyarta kafin aka samu waje ya d'an daidai, nutsuwa ya shigo wajen, itama mai karb'an bak'in ta nemi waje ta zauna awani had'add'an royal chair da aka jejjera wasu manyan throw pillows akai, ta kishingid'a tana rarraba idanu, gasu dama idanuwan manya manya dasu akayi rashin sa'a tayi musu ciko da k'arin eye lashes daya making nata look like wata growling monkey.
The only beautiful thing in her body is her long pointed nose, her small pink lips sai suman kanta da ko daga nesa ne, kana iya hango yawan shi da ka natural look d'insa, and that made her a little beautiful in the face, ba shakka tanada d'an kyau ta fuska ko don farin fatarta za'a iya kiranta da kyakkyawa.
Unexpected HUMAIRA taji wani sanarwan daya girgizata, ta d'ago kai da sauri tana rarraba ido inda Aunty B take, ata inda take jiyo tashin muryanta.
HUMAIRA ta had'iyi sauran juice dayake hannunta da k'yar, wanda yayi wani irin wucewa mara dad'i ta mak'ogoronta. tana dibi dibin ajiye glass d'in saboda d'imuwan data shiga har k'afanta na rawa, na jin abinda Aunty B ta fad'i.
YOU ARE READING
RANSTUWAR JINI (The blood vow)
OverigThe story of a love triangle, twist and deception RANTSUWAR JINI labarine da a sanadiyyar RANTSUWAR JINIn mutum biyu, yayi sanadiyyar rushewar farin cikin mutane da dama