RANTSUWAR JINI(THE BLOOD VOW)19

9 1 0
                                    

❣️❣️❣️❣️❣️❣️
*RANTSUWAR JINI*
*(THE BLOOD VOW)*
❣️❣️❣️❣️❣️❣️
*EPISODE 19*
*STORY AND WRITTEN*
*BY*
*MAMAN NOOR*

*DOUBLE BLESSINGS*

....................... Tunda ya fita daga wajen Hajiya da tayi tayi ya tsaya yaci abinci yaki, yana mota yana recalling d'in maganar da sukayi d'azun shi da aunty momi, maganar da yana jinta a cikin kwakwalwarsa tamkar ana tsikara masa allura, he don't even know what to think or decide, from all aspects yana ganin yarda da wannan auren da AUNTY Momi ta deciding zai zama babban matsala, ba matsalar bace ma babban abinda ta dameni shi, damuwar Hajiyar sa, how can he look into her eyes yace ya k'ara aure,upon all the signals, signs and warnings datake yi mai, though yasan idan yayi niyyan abu bai damu da opinion d'in kowa ba.

But hajiyarsa daban ne, bayason b'ata mata, bayason ganin b'acin ranta, bayason ya kasance cikin y'ay'an da zasu zamarwa iyayensu silar bak'in ciki, hajiyarsa is a jovial person, he don't want to hurt her.

In order side ga Farida, his one and only love, matarshi dayake so, yake kuma ganin tafiye masa kowacce mace a duniya bayaga mahaifiyarsa. Farida macece iya mace, babu abinda ta rage shi dashi. does she really deserve this? ya tambayi kansa.

Wani gefen na zuciyarsa kuma na fad'a masa, to ay ba haram zai aikata ba, sunna ce, don ya k'ara aure bashi ke nufin Matar shi ta gaza ba.

But again wani b'arin kuma na fad'a masa matsalan shine yanda zai zauna da wacce yake zargi a matsayin matarsa na aure, no it's impossible bai kamata ya yarda a d'aura auren nan ba, hell no! ya daki siterin motar da hannu, yana jin wani irin k'una a cikin zuciyarsa. har baisan ya sake siterin ba, saida yaji wata mota tana tayi masa horn a kusa dashi, kafin ya farga, ikon Allah ne ya tsare shi motar ta tsaya a gefen titi tana wata irin k'ara har saida ya buga goshinsa har tana bleeding.

Ya d'an shiga shock na few minutes, kafin yaji muryan mutane asaman kanshi suna magana, since then bai kuma sanin inda yake ba.

Sai washe gari daya fara kamar yanda ya saba shafa kai as in habit d'insan nan dai, yaji kaurin bandage a wajen, ya kuma tattab'awa yana mai son tabbatarwa, ya tashi zaune da k'yar saboda tsamin da jikinsa keyi masa.

Love! how are you feeling? ya juyo yana kallon FARIDA dake k'ok'arin yi masa shield da pillow a bayansa.

Taci ado cikin shigar data sabayi wayo, shigar k'ananan kaya, dogon pencil jeans da body hug, ko dankwali babu a kanta, saidai ta nad'e suman tayi donut dashi ta baya, tayi mugun kyau tamkar sarauniyar kyawawan duniya.

Yayi murmushi yana mik'a mata hannu d'aya, Farida is always unique. ta iso ta zauna a gefensa tana maida masa murmushin.

Thank you!  ya fad'i yana mai rik'e hannayenta acikin nasa, ta d'ago kai tana dad'a kallonsa idanuwanta sun soma ruwa, tamkar zatayi kuka tace please love don't do that again.

Ya kalleta cikeda mamaki yace do what love? ta rumgume shi wannan karon tana mai fashewa da kuka.

Bai hana ta kukan ta ba, saida ta d'an tsagaita, kafin ya share mata hawayen yana kallon cikin idonta.

Ta d'an turo baki irin shagwab'an nan, nidai love please ka daina fita babu driver stress nayi maka yawa, yanzu ba don Allah ya tsare ba da bamu san iya abinda zai faru da kai ba, ta kuma rumgumarsa tana mai fashewa da kuka.

Bai hanata kukan ba, sai ma dad'a rumgumarta da yayi shima yana tapping d'in bayanta, yana jin pain d'inta har cikin jinin jikinsa fiyeda ita, fiye kuma da pain d'in dayake ji asaman goshinsa.
Ya janye ta daga jikinsa, tareda share mata hawayen fuskarta. stop crying i promise you daga yau sai abinda kikace nayi, zanyi a gidannan.

RANSTUWAR JINI (The blood vow) Where stories live. Discover now