❣️❣️❣️❣️❣️❣️
*RANSTUWAR JINI*
*(THE BLOOD VOW)*
❣️❣️❣️❣️❣️❣️
*EPISODE 9*
*STORY AND WRITTEN*
*BY*
*MAMAN NOOR**New me*
.......................... Sanata binta ta kashe cctv video tana kallon RUFAIDA data had'e giran sama da k'asa tamkar wacce akayiwa mutuwa.
To ke kuma mai akayi miki? ta kuma turo baki gaba, gaskiya mummy yarinyar nan ta tafi gida kawai, ay NJ ya riga da warke.
Sanata binta tayi murmushi ta zaunar da RUFAIDA, to wai ke yanzu bakiji kunya ba, y'ar k'aramar yarinya kike son d'aga hankalin ki akan ta.
Ta kuma had'e rai, mommy bakiga yanda take k'ok'arin cusa kanta awajen N. J bane, d'azu fa kina gani ya kissing d'inta.
Ni wallahi ban yarda da yarinyar nan ba, ta fice kawai ta tafi.
Sanata binta tace, i don't care ko kwanciya yayi da ita, ba damuwa ta bace, my only problem shine naga baby boy d'ina ya samu lafiya.
RUFAIDA ta fashe da kuka, ta wuce d'aki da gudu har tana tuntub'e.
Sanata binta ta kad'a kai, ta tab'e baki itama ta koma dak'inta, domin tanada taron zuwa, ita shirmen RUFAIDA sam bai dameta ba, in as much yanda ta tsani HUMAIRA bai kai d'igon son data keyiwa NAJEEB ba, don haka ne k'orafin RUFAIDA bai karb'u ba.
*************
Tsawon awa biyu tana durk'ushe a ajikin k'ofar banda kuka babu abinda take yi. kowanne seconds idan ta tuna da wai namijin da ba muharraminta ba, ba mijinta ba ya tab'a ta, sai ta kuma rushewa da kuka, she feels so disgusted.
Gashi tun lokacin yak'i bud'e k'ofar, ta tuna lokacinda ya razanata wai zai kwanta da ita, batayi k'asa a guiwa ba wajen tsala ihu ba, saidai yayi saurin toshe mata baki da nasa, and she was shocked.
Ta sanya hannu ta ture shi da k'arfi har saida ya fad'i asaman gadon, ta nufi k'ofa da gudu saidai har yanzu k'ofar a datse take, ta jijjiga shi da k'arfi tana ihun neman taimako, amma ko guda babu wanda taji ko gani yazo wajen da niyyar bata taimako, ta juyo tareda durk'usawa awajen tana mai cigaba da kukanta.
Beauty kin hak'ura zaki zauna tareda da d'an iskan kenan.
Na d'ago kai da jajayen idanuwa na ina kallon shi, ya kashe min ido d'aya sannan ya tashi ya kuma zuwa inda nake ya durk'usa, nayi saurin k'ank'ame jiki ina cewa, wallahi ka tab'ani sai na cijeka.
Yayi dariya sosai ya sanya hannun kuwa kamar zai tab'a ni, sai kuma ya janye yana dunk'ule hannun baya.
Kamar ba zaiyi magana ba, saboda irin kallon dayake yi mini, sai kuma naji yace what's your name beautiful?
Na kuma had'e rai na kau da kai gefe ina cizan leb'e, ya mik'e tsaye yana fad'in tunda bazaki fad'a min sunan ki ba ay shikenan na riga da nasani, muryan tsiwan nake son ji.
Ya koma bakin gado ya zauna, ina kallo ya ciro laptop ya bud'e yana danne danne.
Takaicin duniya ya kuma kamani, wato k'arfi da yaji an kawo ni nan ne ana son maidana ni tamkar wata prisioner, dubeni tun jiya babu waya , babu fita, babu freedom of speech.
Please inason nayi waya da Umma ta, ko zaka taimaka min da waya.
Ya d'ago kai ya d'an kalleni kamar zaice wani abu, sai kuma ya d'auko wayar a k'asan pillow sa ya mik'a min.
Na mik'e da k'yar saboda zafin da k'afana yayi min, a tunani na idan na isa kusa da shi zai tab'ani kamar yanda na lura shi d'in bai san d'a a ba.
Saidai ko kallon inda nake bai yi ba har na karb'i wayar, na dawo inda nake.
YOU ARE READING
RANSTUWAR JINI (The blood vow)
عشوائيThe story of a love triangle, twist and deception RANTSUWAR JINI labarine da a sanadiyyar RANTSUWAR JINIn mutum biyu, yayi sanadiyyar rushewar farin cikin mutane da dama