RANTSUWAR JINI(THE BLOOD VOW) 25

13 1 0
                                    

❣️❣️❣️❣️❣️❣️
*(THE BLOOD VOW)*
❣️❣️❣️❣️❣️❣️
*EPISODE 25*
*STORY AND WRITTEN*
*BY*
*MAMAN NOOR*

*ZAINAB LAST CHAPTER*
*BLOOD VOW VERSION 2*

_____________Doctor Antonia ta cire translator dayake kunnen ta, wanda tasa shi saboda ya dinga fassara mata abinda HUMAIRA take fad'i.

Ta matso kusa da Humaira tareda rumgumeta trying to calm her down da dad'ad'an kalamai, ganin yanda duk ta rikice sai kuka take tamkar yanzu abin yake faruwa.

Saida ta tabbatar ta d'an samu relief, kafin ta bata ruwa tasha kad'an, tace Humaira ta kwanta amma tak'i, ta share hawayen fuskarta da bayan hannunta, ta d'ago kai tana kallon Dr MANSUR dake tsaya bakin k'ofa ya  had'e hannayensa a kirji idanuwansa duk akanta ko k'iftawa bayayi.

Suna had'a ido ta b'ata rai sannan ta kauda kai, haka kawai yanzu take jin haushinsa, shi kuwa bai damu da duk wani facial expressions d'in ta ba, his thought are deep at that moment.

Tayi shiru na d'an wasu seconni kafin ta cigaba da magana kamar haka :

***********
Mutuwar SHATU da kuma YADIKKO ya girgiza mutane da dama, tun daga masoyanta har izuwa wad'anda ake ganin basa k'aunarta, kowa mutuwar ta tab'e shi, dad'in dad'awa da mutuwar ya had'u da tafiyar yaya mudi wanda babu wanda yake, ko wajen daya nufa, mutane da dama sun alak'anta mutuwar su YADIKKO akan mutuwar mutum uku, saboda tsoro da tunanin yiwuwar dawowar yaya mudi nan gaba.

Bayan anyi kwana bakwai kowa ya fara watsewa dangi da abokanan arziki duk an fara had'a y'an tsummokaran su, saboda komawa gidajensu.

Hajiya Zeenat wacce aka fi sani da Ummah, babbar ya ce ga yadikko wacce tayi aure a garin yola, auren dangi da yaron kawunsu dake cikin birnin yola, itace kad'ai a d'akin su yadikko tayi aure a cikin birni, kuma take jin dad'i saboda yalwar da mijinta yake dashi.

Dama datazo ta'aziyyar niyyarta ta rok'i mahaifin SHATU ta d'auke ta su tafi yola tare, saidai abinda ta iske yasa taji ko ta k'arfin tsiya saita tafi da SHATU, saboda abinda ya faru.

SHATU y'ar shekara goma zuwa sha d'aya a wannan lokacin ta fara wayo tana fahimtar duk wani abinda yake faruwa, tundaga ranar da aka nemi Zainab aka rasa, har izuwa dawowa da gawarta da akayi, da dukkanin abinda yaya mudi ya fad'i duka a gabanta, dama tun ba'azo wannan ranar ba, taji ta tsani wannan yaya malam d'in da ake ta fad'i. ballantana yanzu datake ganin shine sanadiyyar mutuwar masoya kuma shak'ik'anta biyu, sai taji ta  tsane shi fiye da komai a duniya, shiyasa ma SHATU na cikin mutanen da basuyi wani kuka ba a wannan mutuwar, saidai ku ganta a zaune a gefe guda tana kumburi tareda jan numfashi akai akai wanda yake dad'a bayyana tsananin b'acin ran datake ciki

Sau da dama idan siyama ta tuhume ta akan dalilin dayasa bazatayi kuka ba, sai ta kuma had'e rai, tace ba zanyi kuka ba har saina saka wannan yaya malam d'in kuka, sai yayi kuka harda Jini, saina sashi yayi wahalar dayafi wanda yasa yaya Zainaba na aciki, nima wallahi saina rama mata.

Siyama kanyi shiru tana kallonta cikeda mamakin yanda take cikeda burin fansa azuciyarta, duk kuwa da k'arancin shekarunta, sau da yawa idan ta tambayeta abinda zatayi masa datake cewa zata rama, saita ce itama batasani ba, amma idan suka had'u zata sani.

Sai Siyama tace to a ina zaku had'u tunda bakisan inda yake ba? sai tace ko a ina ma tasan zasu had'u, tunda ta rok'i Allah daya had'a su tasan Allah ya karb'i addu'anta, ko bakisan ance addu'ar wanda aka zalunta ana saurin karb'a ba.

Most of the time idan tayi magana haka Siyama sai tayi ta mamakin kaifin basirarta, dama can SHATU akwai wayo, gashi ya had'u da tayi karatun addini sosai itada y'ar uwarta Zainab fiyeda kowa na gidan.

RANSTUWAR JINI (The blood vow) Where stories live. Discover now