❣️❣️❣️❣️❣️❣️
*RANTSUWAR JINI*
*(THE BLOOD VOW)*
❣️❣️❣️❣️❣️❣️
*EPISODE 24*
*STORY AND WRITTEN*
*BY*
*MAMAN NOOR**ZAINAB CHAPTER 3*
*BEFALL THE TRAGEDY*____________________ Yaya malam ya tafi amma zai dawo muyi aurenmu, zai dawo ya d'aukeni muje birni inda ya koma, yaya malam d'ina zai dawo na fad'a muku.
Zainab kenan! abinda kullum ta zauna take fad'i kenan, koyaushe a yanzu batada maganar daya wuci na yaya malam kaza, yaya malam kaza.
Mutane da dama dariyanta sukeyi, saboda sun san asalin abinda ya faru, itace dai batasani ba, tausayinta yasa yadikko zaunar da ita ranar daya cika kwana arbain da tafiya. kina jina! Zainab ta gyad'a kai tana jin wani irin fad'uwar gaba, saboda ba kasafai yadikko take zama waje d'aya da ita ba, har suyi wani dogon magana.
Saida yadikko tayi mata dogon nasiha, kafin, ta fara yi mata bayanin abinda ya faru dalla dalla. Zainab tayi shiru tana jin yadikko na fad'a mata wai yaya malam d'in tane bazai dawo ba, yaya malam d'in ta da sukayi RANTSUWAR rik'ewa juna amana har tsawon rayuwar su, yaya malam d'in da ko jikinta duk kunne ne, bata yarda zai guje mata ba a tsawon rayuwarta.
Shiyasa duk abinda yadikko ta fad'a babu wanda ya zauna mata, ita dai damuwarta d'aya yaushe yaya malam zai dawo, shiyasa kullum ta tashi z
sai ta shiga gidan malam mustafa ta gaishe idan zata fita saita tambaye shi yaushe ne yaya malam zai dawo, ya kan yi murmushi sannan yace taje tayi ta addu'a.Yawancin lokuta amsar batayi mata dad'i, don ita tafison ace ga ranar dazai dawo, amma kullum babu tak'amammen amsa. wannan dalilin ne yasa yau dayake cika wata shida da kwana goma da tafiya, ta fito idanuwanta jajir alamun bak'aramin kuka taci ba.
A hanyar ta ta fitowa ta had'u da SIYAMA wacce ke k'ok'arin shigowa hannunta rike da kwanukan data kai abinci gona dashi.
A'a zainaba ina kika nufa da uwar ranar nan? Zainab ta share guntun k'wallar daya zubo mata a idanu ta kalli SIYAMA sai kuma ta fashe da kuka tace zanje wajen malam ne ya fad'a min inda aka kai yaya malam, nima zan bishi , SIYAMA tayi saurin rik'e mata hannu, ta d'an waiga gefe da gefe kafin taja hannun Zainab d'in suka shiga can cikin gidansu ta baya wajen inda ake d'aure tumaki, suka zauna a wasu dutsen k'asa dayake wajen.
Kina jina zainaba, kiyi shiru ki daina kuka, bansani ba ko yadikko ta fad'a miki asalin abinda yasa akazo aka d'auki yaya malam, amma gaskiya abinda nasani shine, babu wanda yasan inda aka kai yaya malam.
Zainab ta zaro idanu waje cikeda tsoro, tace don Allah da gaske, nifa yadikko tace min baabarsa ce ta d'aukesa saboda yaje yaga inda take zama, saboda basu wani san juna ba shida ita, kasancewar tun yana yaro wasu suka saceta aka nemeta aka rasa.
SIYAMA tace tab! to yadikko ba gaskiya ta fad'a miki ba, yaya malam dai da k'yar ya dawo, saboda yanda naji su uwale na fad'a wai wannan baabarsa tanada kud'i sosai, wai shiyasa ta turo k'atti suzo su kawo mata shi ta k'arfin tsiya saboda, ta tsani talauci, shiyasa ma ta gudu ta barshi da malam lokacin yanada shekara uku, wai don ita ta gaji da zaman talauci ta ajiyewa malam shi wai ta sadakar dasu wa duniya, ita kam zata fita nema ne, duk ranar data samu zata dawo ta d'auki yaronta.
To wallahi a yanda naji uwale na fad'a, barikinta kawai taje tanaci, tsawon shekaru masu yawa babu wanda yaji d'oriyarta, sai lokacinda data turo wad'annan samudawan su tafi da yaya malam, bakiga dukan da sukayi wa malam mustafa ba, saboda yana ta hanasu tafiya da yaya malam, muguwace akace sosai, wallahi zainaba kiyi hak'uri kawai ki manta da yaya malam tunda gashi iliya mai nama ya nace yana sonki.
Zainab data gama jin bayanin SIYAMA tamkar labarin k'anzon kurege babu abinda ta d'auka sai anzo an tafi da masoyinta yaya malam ta k'arfin tsiya.
Ta share hawayen idonta, ta mik'e harta fara tafiya ta juyo tana kallon SIYAMA data sake baki tana kallonta sakaka cikeda mamaki. Yaya malam d'ina zai dawo, idan bai dawo ba, ni zan bishi, kisan da wannan.
YOU ARE READING
RANSTUWAR JINI (The blood vow)
AléatoireThe story of a love triangle, twist and deception RANTSUWAR JINI labarine da a sanadiyyar RANTSUWAR JINIn mutum biyu, yayi sanadiyyar rushewar farin cikin mutane da dama