❣️❣️❣️❣️❣️❣️
*RANTSUWAR JINI*
*(THE BLOOD VOW)*
❣️❣️❣️❣️❣️❣️
*EPISODE 37*
*STORY AND WRITTEN*
*BY*
*MAMAN NOOR**THE BROKEN YORK*
______________ BIBA! dukkaninsu suka maimaita yayinda suke dad'a kallon BIBAn wacce ta mak'ale a jikin BIMBIn ta, shikuwa MANSUR na nan tsaye a gefe ya folding hannayensa a gefe, everything happening seems like a written script.
NAJEEB dake kwance a k'asa feeling alot more weaker, ya mik'e da k'yar idanunsa tsaf duka na kan BIBA wacce ganinta tamkar almara take awajensa.
Yana layi had'e da tangal tangal ya iso har gaban ta yana dad'a k'are mata kallo trying so hard to console his self cewa ba Zainab bace daya dad'e yana jin zafin mutuwar ta cikin zuciyarsa without a valid reason.
BIBA kam kallo d'aya tayi masa taja tsaki ta kuma rumgume BIMBInta, ya had'iyi yawu da k'yar saboda wani abu dayaji ta bigesa a zuciya daga yanayin kallon tsanar dayaga tanayi masa.
Maganar UMMA ne ya kuma jan attention d'insa zuwa ga HUMAIRA da tuntuni take tsalle ajikinta kamar y'ar goye.
Yanzu fisabillillahi HUMAIRA aure kika kuma yi, meye dalilin kashe auren ki kuma? a ina kika bar y'ar taki? kafin HUMAIRA tayi magana NAJEEB yace nima tambayar danake yi mata kenan kullum UMMA, meyasa ta matsa saina saketa bayan babu abinda ya had'amu. Umma wallahi inason ta sosai kamar raina.
Yaya MUDI daya saki baki kamar wawa, everything is confusing awajen, though by now ya d'an fahimci wani abu, wanda it's a real shocker to him. shiyasa ma NAJEEB bai k'arashe magana ba ya shiga tsakani cikin tsananin b'acin rai ya nuna sa da yatsa, ka juya ka fice daga gidan ko na karya ka, na kuma sa a kulle ka for intruding of privacy.
NAJEEB yayi shiru yana kallonsa, ko kad'an baida k'arfin sa'insa, cikin sanyi da taushin murya yace kayi hak'uri yanzu nima zan tafi, but please let me talk to my wife tukunna.
Yaya MUDI ya cafko wuyan rigansa yana fad'in yanzu kai har kanada guts na kiran k'anwata da matarka, wai yaushe ma ka auri SHATUN da har tazama matarka? ko itama kayi amfani da k'arfin yaudara da butulcin daka kware akai ne ka yaudareta ka barta.
Upon all the dogon bayanin da Yaya mudin yayi, abinda najeeb d'in yaji kawai shine "k'anwata a matsayin matarka" what does he mean by that? ya tambayi kansa a zuciya. ya ture hannun yaya MUDI daga jikinsa yana fad'in you must be joking, this is HUMAIRA mother ya fad'i yana nuna Umma, she has no relationship with you. yaya MUDI ya kuma harzuk'a da furucin NAJEEB yace dayake kai d'in kanin ubanane danake tsoro, shiyasa ma zan tsaya yi maka wasa. maybe bansan ya akayi ka AURI SHATU ba, duk da nasan bazaka aure ta batareda kaga dangin ta ba, amma kasani HUMAIRA k'anwata tace, kamar yanda take k'anwa ta Jini awajen yarinyar daka yaudara har kayi sanadiyyar barin ta duniya.
NAJEEB ya zare idanu cikin tsagwaron mamaki yake kallon su duka biyu, kafin ya maida kallonsa wajen HUMAIRA data had'e rai tamkar bata dariya. ya d'an bar wajen yaya MUDI ya matso kusa da HUMAIRA datace wa su UMMA su shiga ciki zasu shigo, Umma ta kalleta ta kalli MANSUR da har yanzu yana jingine jikin motarsa wayarsa ma yake dannawa, sai ka rantse hankalinshi baya wajen.
Ta kad'a kai ta juya wajen BIMBI suka shige ciki, NAJEEB ya kuma cewa da gaske ne abinda yaya mudi ya fad'i HUMAIRA? is it true shi d'in d'an uwankine da Zainab? Humaira please talk to me zuciya ta na bugawa fiyeda k'aida.
HUMAIRA ta gyara tsayuwarta tana mai facing d'insa da kyau, tace what did you want me to say? naga kamar yaya mudi da kansa ya gama yi maka bayani, what other thing do you need? ko k'arya kake son nayi maka? oh now you are confused! mu kuma ay mun dad'e da shiga confusion lokacinda ka nuna mana butulcin naka, ka watsa mana k'asa a idanu, ka wulakan tamu to the extent that your decision took the life of two greatest, beautiful and important people in my life.
YOU ARE READING
RANSTUWAR JINI (The blood vow)
RandomThe story of a love triangle, twist and deception RANTSUWAR JINI labarine da a sanadiyyar RANTSUWAR JINIn mutum biyu, yayi sanadiyyar rushewar farin cikin mutane da dama