❣️❣️❣️❣️❣️❣️
*RANTSUWAR JINI*
*(THE BLOOD VOW)*
❣️❣️❣️❣️❣️❣️
*EPISODE 15*
*STORY AND WRITTEN*
*BY*
*MAMAN NOOR**MY SAVIOR*
........................ K'ira'ar surutul maryam ne daga bakin alaramma sudais ne sautin yake tashi a hankali hankali cikin dad'i da sanyin murya mai tausasa zuciya, shiga rai, da sanyawa duk wani bawa mai kasala da sanyin zuciya.
Al-qur'ani mai girma kenan, littafi mai tsarki da tsarkakawa.
kallo d'aya zakayi masa ka fahimci tarin nutsuwa da jin dad'in sauraranta dayake yi.Kwance yayi da bayan shi jikin kujeran motar, kanshi na kallon sama, idanuwansa duk a lumshe, hannunsa na saman goshinsa, annurin dake fuskarsa kad'ai zai nuna maka tsantsar jin dad'i da k'aunar abinda yake saurara. shiyasa tun dasuka taso driver sa yake ta k'ok'arin yaja shi da hira, amma bai na san yanayi ba, ballantana yasamu albarkan amsawa.
Shima driver sai ya kama kansa da bakinsa yayi shiru, saboda yasan indai ogan sa ne, bai cika son ana tafiya a mota ana hira ba, dad'in dad'awa yana tsananin daraja ayar Allah, indai shine to baya yini bakaji ya kunna alqurani ba, walau a gida, ko a mota.
Ringing d'in wayarsa ce tasa shi bud'e ido ya d'an tashi zaune yana kallon view d'in waje ta gilashin motar.
Tabbas gari yayi haske sosai, mamaki ya kamashi na har yaushe ne haka gari ya waye waje yayi haske, dama bacci yayi kome?
Ya maida idonsa kan agogon gucci dayake hannun shi, ya kalli agogon na seconds, sai kuma yayi tsaki ya kauda kai. yana mamakin yanda sun jima suna tafiya amma sai yanzu k'arfe shida na safe zaiyi.
this is one of the reasons daya tsani tafiyar mota, indai ba tafiyar cikin unguwa ni ko wani wajen within the city ba, ya tsani zaman mota, gundurarsa take, yanzun ma k'auye zaije saboda wani medical outreach da zasuyi awajen shine kuma shugaban taro wanda aka wakilta, so zaije wajen ya gani da idonsa, ya monitoring activities na wajen kafin suzo, next week rana ita yau.
Ya yamutsa fuska yana jin tafiyar duk ta gundireshi tamkar ya fasa, k'aran wani kiran awayarsa ne yasanya shi tunawa da kiran da akayi ta masa d'azu.
Habibty! nagani a rubuce yayinda wayar ta cigaba da k'aran neman agaji. wannan karon baiyi nawan d'aukan wayar ba.
Saima gyara Zama dayayi yana murmushin da sai yana tareda ita ko ta kira ka ganshi a fuskarsa.
Sun jima suna waya, tana masa k'orafin ya tafi bai mata sallama ba, sorry kawai yace mata wai yaga tana bacci ne, but yayi mata alk'awarin dawowa da wuri.
Shikenan love! but please take your eyes off akan matan k'auyen nan, ka sansu da shegen wayo, sun san yanda sukeyi su seducing d'in mazan mutane, ta kuma yin k'asa da murya, please love kar ka basu dama, i don't want any girl taje kusa da kai ballantana ta k'wace mun kai.
Yayi murmushi, yana jinjina kishi irin nq FARIDA tuntuntuni yasan halin Farida da k'yamar kishiya, kishiya ko na mak'ota akayi to shikenan ta tsani kishiyar, ko gaisuwa bata yarda suyi.
Farida balarabiya ce y'ar k'asan Sudan, iyayenta masu kud'i ne na gaske, amma hakan baisa ta kasa sakin jiki ta kyautatawa mijinta ba, kullum idan akace mansur na gari, to fa bata gajiyawa da yi masa hidimar abinda yafi so.
Farida kyakkyawa ce sosai don ko ta ina Allah ya bata baiwan kyau, badai ka kalleta kasamu abin kushewa ba a jikanta, tanada kyau tanada diri daidai misali, saidai kushen mai kushe.
Love! ya naji kayi shiru lafiya koh? ya d'an waske yana murmushi kamar tana ganinsa, yace it's nothing dear just continue resting kafin na dawo.
Ta turo baki gaba irin na shagwab'ab'un nan tace ni gaskiya love bazan iya yin wani bacci ba, thinking that matan k'auyen nan sun iya k'wacen miji.
YOU ARE READING
RANSTUWAR JINI (The blood vow)
RandomThe story of a love triangle, twist and deception RANTSUWAR JINI labarine da a sanadiyyar RANTSUWAR JINIn mutum biyu, yayi sanadiyyar rushewar farin cikin mutane da dama